← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 38

Sashe 5

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A farkon auren su yayi haƙuri da lokutan da zai shiga banɗaki yaga Bilkisu ta jefa pant mai haɗe da pad cike da jini a loundary basket ɗin su. Ko kuma a lokutan da ta ke fama da mura ka ga tissue papers da ta face majina da shi a kan gadon su. Ba zai taɓa mantawa da ranan da ya shiga banɗaki tsantsin majina da aka fyace a ƙasan tile ya ɗebeshi ya faɗi ƙasa ba. Yayi haƙuri da kasancewarta ba ta girki saboda a gidan su bata yi, duk da kuwa girki na cikin abubuwan da ke taɓa ma sa zuciya. Girkin Misturah na ɗaya daga cikin abubuwan da suka saka shi faɗawa soyayyarta tun bai shirya hakan ba.

"Saif wannan pepper soup ɗin yana narka zuciyar namiji yana saka mishi nitsuwa. Inada yaƙinin koma mi yake damunka idan ka ci wannan peppersoup ɗin za ka samu sanyi" abinda ta faɗa kenan lokacin da ta miƙa ma sa ɗan ƙaramin food basket da ta riƙo ma sa.

Misturah ta yi gaskiya domin ranan da ya sha wannan peppersoup É—in ya samu nitsuwa.

SSk ya kai hannunsa ya shafa gashin wig da ya ɗan bulloƙo ta gefen hular baccin Bilkisu.

Yayi haƙuri da kasancewarta mai saka gashin wig duk da kuwa warin gashin na tada ma sa hankali.

Namiji na son mace da za ta fahimceshi, ta saurari maganar sa. Sai dai Bilkisu ba ta É—aya daga cikin irin matan nan.

Sau dubu Bilkisu za ta yi iƙirarin tana tsananin son shi tana kuma kishin sa, hakanan kuma sau dubu ba za tayi abubuwan da zai cire shamakin da ke tsakanin su ba, har ta samu damar mallake zuciyarsa.

A lokutan kaɗaici he find solitude in poetry, shiyasa ya ke ɓoye kansa da sunan KaSaSa wanda acronym ne na sunansa.

SSK yai murmushi ganin Bilkisu ta maki kanta tareda sosa tsakiyar kan.

Duk wani mulki daya ke da shi ya tsaya a bakin ƙofar gidan sa ne, a cikin gida shi mijin Bilkisu ne, Abban Nana, Mahira da kuma Junior.

SSK ya muskuta ya jawo Bilkisu jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, rabon daya samu nitsuwar miji da mata daga gareta kusan sati biyu kenan.

"Darling na gaji" ta faÉ—a cikin magagin bacci

"Kar ki damu ba abinda zan yi" ya furta a hankali wani abu na sukan ƙirjinsa...

***

"Kina jina? zan turo miki kuɗin idan na dawo daga office. Ya jikin Muttaƙa?

Tana saƙale da waya a kunnenta yayinda ta ke ƙokarin ɗaura agogo a hannunta.

"Sumayya ki tabbatar Ale bai san da kuɗin nan ba. Kuɗin maganin Muttaƙa kuma ki tabbatar an siyi duka magungunan shi"

Ajiye wayar ta yi ta fice daga ɗakin. Kai tsaye kitchen ta wuce inda Umma ke ƙoƙarin raba abun kari. Kunun gyaɗa ta yi da ƙosai da kuma soyayyen dankalin Hausa.

"Umma zan wuce" ta faÉ—a da yaren kurame

Umman ta amsa ma ta da cewa ta tsaya ta ci abinci.

"Zan makara Umma, amma ki haÉ—a min kunun da dankalin in tafi da shi office"

Murmushi Umman ta yi sannan ta fara neman inda za ta zubawa Asiya kunun.

Minti shida kacal ta ƙara aciki ta fito ɗauke da jakarta da kuma ledan da Umma ta ba ta. Motar Ubayd na jiranta a ƙofar gida dan haka tana shiga ya ja motar da gudu. Gaisawa su ka yi a tsanake ta cigaba da duba wayarta tana bitar report ɗin da ta haɗa jiya.

Tafiyar minti shabiyu ya kaisu ma'aikatar su ta yiwa Ubayd sallama ta shige ciki yayinda shima Ubayd ya wuce Asibiti.

Tana shiga office É—in su ta printing report ta wuce da shi office É—in Editor I.

"Weldone Shahida" ya faÉ—a lokacin da su ka gama duba report É—in tare wanda kusan gyaran da ke ciki kaÉ—an ne.

Tana komawa office ta samu sauran colleages É—inta suna hiran taron da za ayi yau a jihar ta su. Da SSK da matar sa Bilkisu duk babu wanda ke burge Asiya a cikinsu.

"Shahida kin san wa za'a tura yau?"

Shahida ta girgiza kai tana cigaba da latsa laptop É—inta.

Mike ya sake cewa " ina tunanin Abigail za a tura, gashi har yanzu ba ta iso ba"

"Mike kar ka dameni dan Allah. Idan ba ta zo ba MD zai iya bawa wani ai, ko kai ko Usman"

Ta sani magana ya ke son gaya mata akan kada ma tasa ran MD zai bari ta je ta covering report ɗin wajen taron da za ayi na matan Gwamnoni. Ba ta san mi ta tsarewa Mike ba a wannan office ɗin. Tun tana bautar ƙasa kafin a ɗauketa aiki yake sa mata ido cikin lamurranta.

Ta cigaba da aiki tana yi tana shan kununta.

CY ya shigo office É—insu da sauri. "Aseey ki je office É—in MD yanzu-yanzu"

"Miya faru?" Ya É—aga mata kafaÉ—a ya fita da sauri.

Ta yi saurin kurɓan sauran kunun daya rage sannan ta goge bakinta da tissue ta fice daga office ɗin da sauri tana lura da yadda Mike ke binta da mugun kallo.

Ba ta da ikon yiwa MD musu lokacin daya sanar da ita cewa itace za ta kawo rahoton wajen taron da za ayi yau.

Lokacin da za ta tafi ya ce "Asiya bana son shirme"

"Ok Sir"

Ta sani Abigail yai niyyar tura wa saboda Abigail ta fita gogewa a wajen aiki. Tunda aka buɗe gidan talabijin ɗin ta ke aiki da su kusan shekaru shahuɗu da suka wuce kenan. Rashin Abigail Manji ne ya sa MD ya waiwayeta. A wajen CY ta ke jin labarin wai Abigail tayi tafiya, jiya da daddare mahaifinta ya mutu a chan ƙauyen su.

Ba su kaÉ—ai ba ne 'yan jarida da su ka zo É—aukan rahoto kusan kowanne gidan jarida sun aiko da wakilan su. CY ya fito da kayan aiki ya shiga saita camera É—in.

***

Chief of staff (COS) ne ya shigo ofishin mataimakin Gwamna da sauri hannunsa riƙe da ipad.

"Your Excellency za ka so ganin wannan"

SSK ya karɓi pad ɗin daga hannun COS ya danna kan video dake screen ɗin.

Yar jarida ce a gaban hall É—in da ake taron matan gwamnoni tana bada rahoto.

"Kaman yadda al'umma su ka shaida irin almabazzarancin da akayi a wajen wannan taro wanda ake iƙirarin anyi shine saboda talakawa. Ko ta ina talaka zai anfana da mawaƙan nan Wizkid da Patoranking da aka ɗauko daga Lagos domin matan Gwamnoni su shaƙata da waƙoƙin su?. Yayinda matar mataimakin Gwamna wato Hajiya Bilkisu S Kachallah take magana akan yadda za a gina gidan marayu, talakawa na nan suna alhinin rashin albashi, rashin ruwa ga uwa uba malaman makarantar firamare da ke yajin aiki tun sati uku da suka wuce har yanzu Gwamnati ba ta waiwayesu ba.

Na zanta da wasu matasa inda su ka bayyana mini cewa taron da Hajiya Bilkisu ta yi wani farfaganda ce kawai da ke son É—auke hankalin talakawa daga matsalolin da su ka sha mu su kai..."

Tsaida video ɗin yai ya miƙawa COS ipad ɗin

"Your excellency kana buƙatar mu tuntuɓi gidan talabijin na Hill TV ne?"

"A'a"

COS na fita daga office É—in SSK ya É—au waya ya kira commisioner of finance...

*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....

*©Azizat Hamza*

wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim

Book one

03

"Aseey we are dead" CY ya faÉ—a lokacin da suka shiga mota za su koma office.

"Ni fa ka ganni nan ba na tsoron ta ɓaci wallahi. Gaskiya ce zan faɗa ko da ba za ta yiwa wasu daɗi ba. Idan ban faɗi gaskiya ba miye amfanin aikin jaridan da na ke yi"

"Dama kin fi kusa da MD ai"

"Kai ka san wannan"

Lokacin da su ka isa office Asiya ta É—auka MD zai ma ta faÉ—a amma bai ce komai ba. Ta yi mamaki kam dan indai MD da ta sani ne to da tuni ya fara diri akan ta sako maganar albashi a rahoton da ta kawo.

Awa É—aya bayan SSK ya kalli rahoton Asiya, ya saka hannu aka sakewa ma'aikata albashin su, zuwa yammaci kusan fiye da rabin ma'aikata kowa ya ji alert É—in albashinsa.

Mintuna kaÉ—an bayan SSK ya sake albashi kiran Gwamna Saminu Bacchi ya shigo wayarsa.

Duk da Gwamna Saminu ya girme shi da shekarun da ba za su wuce biyar zuwa shida ba, SSK bai chanchanci irin tsawan da Gwamnan ya masa ba akan ya sake albashi kafin ya dawo.

Bayan ya ajiye wayar ne ya fara tunanin anya kuwa zai iya cigaba da irin wannan tozarcin..

***

Daf an kusa tashi aka kawowa Asiya Shahida letter daga office É—in MD. Tana gama karantawa ta wuce office É—in sa da sauri.

"Sir yanzu aka kawo min wannan letter, ban gane ba. Two weeks suspension sannan ka maida ni copy editor"

"Kafin ki tafi ki je ki reporting a wajen News Director"

"Sir???"

"Ba za ki sake airing komai ba har sai kin iya banbanta professional da personal affairs"

Sai yanzu ta gane ashe shirunsa ɗazu ba yana nufin cewa ransa bai ɓaci da abinda ta yi ba ne.

"Idan kuma ba ki gyara ba, Hill TV za ta iya É—aukan mataki mai tsauri akan ki"

Haƙuri ya ke so ta bashi ta sani kuma ba zata bayarba.

"Shikenan Sir, nagode" daga haka ta fice daga office ɗin tana dunƙunƙune takardar da ke hannunta.

Ko jira lokacin tashi ba ta yi ba ta É—au jakarta ta bar station É—in...

Asiya na zaune akan stool a ƙofar ɗakinsu tana yiwa Ummanta kitso Ubayd ya shigo gidan da sallama. Da sauri Umma ta jawo hijabinta da ke gefe ta saka ta bar Shahidah da buɗe baki. Umma ba dai kunya ba. Ta faɗa a zuciyarta. Wai dan ma ba ayi aurenta da Ubayd ba kenan.

Ubayd ya tsugunna ya gaishe da Umma. Ya iya gaisuwa kam amma har yanzu bai fahimtar yaren kurame sosai kodan bai taso a gidan ba ne?

Ya ajiyewa Umma wata ƙatuwar leda tareda kuɗi acikin envelop.

Umma ta shiga yi ma sa godiya, ta zunguri ƙafar Asiya alamar ta tayata yiwa Ubayd godiya.

"Ya Ubayd yaushe aka yi albashi?"
Chapter 5 · 0% Book details