Sashe 9
Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na ɗan jima a zaune a wajan. "Baba! Baba!!" Na jiyo muryarshi yana kirana cike da yarinta. Ko dana hangoshi gudu yake yi sosai, yana isowa ya faɗa jikina. Tsam na tiƙeshi fata nake dama mu dauwama a haka. "Inna kinyi ma Baba magana bazan sake tafiya in barki ba ko?" Kanshi na shafa, nace. Haba ɗannan ai wannan karatun da kake yi shine gatanka, kuma kayi haƙuri da duk abinda malaminku yake yi maka, gyaran tarbiyya yake yi muku. Kul na kuma jin kace bazaka koma ba, ka zamto mai bin umarnin mahaifinka a koda yaushe." Badan inaso ba na bashi haƙuri, nayi hakanne dan in kore mishi damuwa, gami da ƙarfafashi, ga ƙafafunshi duk raunin ƙarfen mari, ga datti da tsagewar fata har wani ɗoyi_ɗoyi yake yi. Ga ɗakin duhu da malaminsu ke rufesu a ciki, ni tsorona ma kar yarona ya rasa idanunshi, dan Mahaifinmu ya taɓa bamu labarin wani abokinsu ada lokacin suna wajan almajirci ya kasance mai yawan yin laifin da yasa kusan kullum sai an sashi a ɗakin duhu, daga ƙarshe wannan ɗakin shi yai sanadiyyar makancewarshi, sai gida aka mayar ma da iyayenshi shi. Babu wani mataki da aka ɗauka na shari'a shikenan an cuci iyayenshi. Na jima ina yi ma Idi nasiha, ina kuma kwatanta mishi rayuwa, mun jima sosai a wajan, daga baya mu kai sallama ni na nufi tashar Bodi, shi kuma ya nufi dandali. Kafin in isa Azare na jiƙe sharab da fitsari. Hakanne ya tilasta mun zuwa gida dan in gyara kaina. Kayana dana bari rannan shi mahaifiyata ta ɗakko mun na saka nayi ƙunzugu, sannan tace. "Naji cewar wai Yawale zai ƙara aure ko? Karma ki sake kice zaki ta da hankalinki a karon banza. Tunda kika taso kika tarad damu mu biyu da Lami a gidannan, kuma mun cakuɗe yaranmu ta yanda mu kaɗai muke iya banbancewa. Ki sanya salama a zuchiyarki, kici gaba da bin Yawale sawu da ƙafa. Zaki ci ribar yin haƙuri, Allah ya raya miki yaranku SU KULA DAKE." Inna Lami ce tayo sallama ta shirya tsab. "Tarana na fito, Musina tawo mu tafi maza, harma fa nasa tun safe Yayanku yaje ya kama mana layi." Jiki ba ƙarfi na fito muka wuce." In baka zuwa asibiti bazaka gane cewar ana ciwo ba. Nayi zaton masu yoyyon fitsari basu da yawa, amma abun mamaki sai naga a ɓangarenmu munfi mata hamsin. Harda ƙananun yara da basu wuce shekaru goma ba. Ashe nawa nafila ne, dan naga mata da dama da suke zaune amma fitsari na gudu a ƙasa daga jikinsu. Gun duk zarni. Ƴar nutsuwa na samu. Muna zaune ba'a soma ganin likita ba, kamar ma likitan baya nan. Sai muka ga wasu mata manya sun shigo. Sai nuna musu mu akeyi, sunata mana sannu da jiki. Basu jima da tafiya ba Likita ta iso. Nan kuma aka shiga bin layin shiga ganin likita. Duk wacce ta shiga sai in ganta ta fito da takadda. Har layi yazo kaina na tashi jiki ba kwari, Ƙasimu yana hannun Inna Lami. Tare muka shiga ɗakin ganawa da likita. "Bismilla zauna" waje ta nuna mana. "Musina ko zaki iya bani labarin sauyin yanayin da kika samu a jikinki kamun wannan lalurar ta ɓullo miki?" Hawaye na soma zubarwa, nama kasa bata amsa. Likitannan ta dubi Inna Lami tace. "Baba tare kuke da mai gidan nata ne?" "O'o ƴannan mu kaɗaine, ni uwarta ce, sai yaronta na goye. A Saleri take ba anan ba. "Amma ina mai gidanta? Ai ya kamata ace shi zai rakota. Wai me yasa maza suke gudunmu da zaran laruri ya samemu, kuma duk yawancin lalurin sune suke zama sanadiyyar ɗaura mana, sai su dinga gudunmu in matsala ta samu. Nayi imani da shine wannan lalurar ta sameshi, ƙarshenta ita zata rakoshi asibiti, kuma taita ƙarfafa mishi guiwa. Baba Lokacin da tazo haihuwa a gida ta haihu ko asibiti? "Ƴannan a gida ta haihu, bata taɓa zuwa asibiti ba dai_dai da sunan awo, sanadiyyar wannan lalurinne yasa muka zo." Ɗan rubuce_rubuce tayi sannan tace. "Musina kinyi doguwar naƙudane a lokacin da kika haifi jaririnki, sannan watanshi nawa ne? Ki saki jiki kiyi mun bayani asibiti ana zuwane dan a samu mafita, ba'a ɓoye komai. Baki ga tarin mata masu yoyyon fitsari a waje ba? Wasu ma aiki za'ayi musu, ga wasu tari da yawa suna kwance a cikin asibitinnan an basu gado." Daurewa nayi nace. Nayi naƙuda ta kusan kwana biyu, kuma iyayen mijina sun hana a kawoni asibiti, dan alokacin mai gidan yaso a kawoni. Ko dana haihu har akayi suna ban dawo dai_dai ba. Yanzu wata huɗu da haihuwar tawa. Kwana takwas yau da faruwar abun." "Okey jikin naki ma da sauƙi kuma kinyi kyan kai sosai da kika zo asibiti, ba wajan maganin gargajiya ba. Zan ɗauraki kan wata shawara Musina mu gwada na tsawon sati biyu mu gani. In kika koma gida kita shan ruwa kawai, ko da ƙishi ko babu, fitsarin da kike yi zai ƙaru amma karki damu da hakan. In anyi sati biyu saiki dawo asibiti. Sannan in ba dai dare bane ya rufa ba, ki dena saka ƙunzugu, ki dinga barin wurin yana samun iska dan gudun wari da kuma gujema ƙwayoyin cuta masu cinye al'aurar mata wato Infection sanyi kenan a hausance. Sannan akwai wata gidauniya data ajjiye mana forms guda hamsin, kuma ga mata masu lalurar fitsari kawai suka bada umarnin a raba. Wannan gidauniyar zata ɗebi mata masu lalurar fitsarine ta horar dasu kan sana'a irinsu ɗinki, haɗa mandula, da sabulun soda, da omo na gari, da man shafawa. Kuma a kyauta zata horar daku, sannan ta raba jari gareku in zata yaye ku. Ga Form nera nera biyar zaki bayar a baki form. Za'a gudanar da aikinnan a filin firamare tamu, ina fatan zaki zama ɗaya daga cikin waɗanda za'a horar ko Musina? Bana fatan mijinki ya hanaki wannan abun kiyi ƙoƙarin kasancewa ɗaya daga ciki, dan zai taimaka miki ki tsaya da ƙafafunki." Ajjiyar zuchiya na sauke, jakata na buɗa na ciro nera biyar kamar yadda tace. A gabanta ta ajjiye Form ɗin tace. "Bari in cike miki, sannan ɓangaren wacce sana'a kika zaɓa?. Likita aina iya karatu da rubutu, na ajimi da hausar boko nayi firamare a makarantar gwamnati ta Azare." Murna naga wannan likitan nayi tace. "Amma iyayenki sunyi ƙoƙari sosai Musina. To ga form ɗinki sai ki cike, nan da sati biyu za'a soma horas daku, shima horarswar zata kai sati biyu ana yinta. Sai kuma a yayeku,a ɗan baku jari da zaku dinga jujjuyawa." Godiya Inna Lami tayi ma likitannan sosai. Mu kai mata sallama muka fito. Har saida Inna Lami taga bodin mu ta tashi, sannan ta nufi gida. Zuchiyata cike dake fal da fargaba. Dan nasan ko ina shure shuren mutuwa dafara na fitowa a bakina Yawale bazai amince da wannan ƙungiya dana karɓi form ba. Ko ya amince nayi imani Baba Hauwa bazata taɓa amincewa ba. A zahirin gaskiya inason koyan sana'ar haɗa mandula, dan mandula in zamu saye, sai dai muyi sallahu a tawo mana dashi daga Azare, amma mu bamu dashi a ƙauyenmu. Zanso im koya ko dan in dogara da kaina, in kula da yarana. Dan nasan Yawale bazai kula dasu ba. Gashi ina da buri akan yarana mata in Allah ya bani, ina da burin ganin sunyi ilimin boko mai zurfi. Dan inason karatun boko sosai. Inna tsaya akan sana'a sai in kula da karatunsu ai. Da waɗannan saƙe saƙen muka iso madakata. Koda na shiga gidan babu wanda ma ya amsa sallamata, sai tottoshe hanci suke faman yi. Kai kawai na gyaɗa nayi shigewata ɗaki. A jiƙe na dawo sharab, kayan jikina na cire, na ɗaura zani a ƙirjina na fita tsakar gidan. Kayan Fitsarin na wanke, sannan na shika sakaki na ɗauraye jikina, na fito tsakar gida na ɗaura alwala na koma cikin ɗakina. Rayuwa haka tai ta garawa, har gida ya cika daf da jama'ar biki. Ranar likinin aka soma bikin bisa ga al'adar ƙauyen Saleri. Ranar litinin: In dare yayi Babannin Amarya zasu tafi gidan uwar dakinta, a kamo ta dakyar qawaye sun ɓoyeta, a fisgota, a sa mata lalle wanda aka kwaɓa da turare, sai a shafa mata suyi ta kuka ita da qawayenta." Ranar talata: za a yini a nata qunshi amarya da qawayanta, Haka laraba da yamma, babbar qawar Amarya, da mabi da babbar ƙawar Amarya, za su sai lalle a taru a dekashi adama da ruwa , su fito qofar gida kowacce ta daura tsohon zani, ba riga, mamunansu a bayyane, ayita zubawa juna duk su jiqe, a hakan za'a tafi gun angwaye ayi ciniki su biya, a dawo gidan da amarya take wato gidan uwar dakina . Da yawan samarin ƙauyan Saleri, a rana irinta yau, suke zaɓen matan aure, sabida mamansu a buɗe suke zuwa, mai so saiya zaɓi wacce mamanta yayi dai_dai da ra'ayinshi. Bayan sun koma gidan uwar ɗakin Amarya, sai su yi wanka. To in dare yayi kuma, gidansu ango zasu zo su kawo kayan sakun lalle, zasu kawo dakakken lalle, turmin zani biyu, sabulu, man shafa, turare, takalmi, gazal, jambaki, duk kowanne guda bibbiyu, da bokiti, baho, moda, kofi, se goro da minti za'a bara goro a faranti kowa ya dauki minti goro ɗaya, minti biyu " Ranar laraba: Asuba nayi baza ayi salla ba za'a zagaye garin baki ɗaya a nata waqoqin amarya iri _iri sai a wuce gidan wali nanma a yita waqa shima seya biya kudi tukunna ayi sallah a karya kumallo. Yamma nayi se kokuwar tsifa ɗaya bayan ɗaya za'a riqa yi amarya tana dokawa, ƙawayen amarya sai su taru a kadata ɗaya ta zauna tana tsefe mata kai, saura kuma suna waqa har agama. kowacce za ta duqa amarya ta zage tayi mata dundu abaya sau biyu, sai su tafi gun angwaye a biya su. Daga nan sai su wuce gidan amarya. Rufar qofa kafin akawo amarya, za su rufe ɗaki nanma sai angwaye sun biya sannan su bude a saka amarya. Ingari yawaye za'a sami budurwar da tsawanta yayi dede dana amarya se tasa kayan amarya a zagaye gidan dangin miji, ana waqa wannan su bada taro wancan su bada sisi da haka har su gama a dawo.