← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 40

Sashe 24

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗambo:
Bayan wasu shekaru masu yawa:
Abubbuwa da dama sun faffaru, wasu masu daɗi wasu akasin hakan. Baba Huwaila Allah yayi mata rasuwa, Baba Shatu tsufa ya far mata. Itace ciwon idanu, itace ciwon sawu, itace tarin tsufa. Mahaifin Audu shima Allah yayi mishi rasuwa. Gidan a halin yanzu mune iyaye. Yaranmu sun girma harma an aurar da wasu. Shagari ɗan gidan Hindu, ƙanin Shatu yayi aure, Audu ya yanka mishi waje a cikin gida, ya gina ɗaki ciki da falo, suna zaune a gidan. Hannatu kuma tana gaban Hindun tana mata tallah. Ita kuma Zainab tayi aure a nan ɗan ƙauyen dake kusa damu. Sauran mazan kuma na Hindu, biyu daga ciki, sun gaji sana'ar mahaifinsu ta dambe.Auwal kuma bashi da aikin yi sai zaman majalisa, in damina tazo, yana taɓa aikin gona na kuɗi. Yarana kuma yanzu, Shatu dai tana aiki a wani kamfani a cikin Zamfara, Zaliha kuma, Lauya ce, Basira kuma tana aji biyu a jami'a tana karanta kasuwanci. Duk suna zaune a cikin gari, sun kama ɗaki, Shatu na kulawa dasu, kuma sun riƙe mutuncinsu sosai, sun taso da nutsuwa gami da kamun kai. Duk juma'a suke shigowa Ɗanbo, ranar lahadi da yamma kuma sai su koma. Usman kuma kiwo yake yi na awakai, harma ya haɗa garke guda, da a gida yake yi, amma Hindu sai tasa mugunta, kullum saimu wayi gari dabba ta mutu. Saiya tattare awakanshi, ya mayar gidan abokinshi. Daga bisani kuma, wani Alh daya gina gidan gona a bayan gari. Saiya samu labarin irin yanda Usman ya iya kiwo saiya neme shi akan yazo ya dinga kula mishi da kifinshi da yake kiwo, da awakai. To Usman saiya roƙi Alhn nan ya kai awakanshi can gidan gonar, duk yake kulawa dasu, duk wata yana biyanshi. Duk da sana'ar man ƙuli da ƙuli na, na ɗauki ragamar karatun yarana kab. Usman da yaƙi karatun ya nuna mun ga abinda yake so, saina ɗauki kuɗi na bashi, ya siyo akuya, da bunsuru. Kamar wasa, akuyarnan taita haihuwar mishi, ƴan hurhuɗu, tashi ɗaya garke ya haɗu, saiya siyo rago da tunkiya, suma sukaita hayayyafa. Yaran gidan duk sun girma, matan da yawa suna gidan mazajensu."
Ina zaune a tsakar gida, ina baza gyaɗa, Shatu tayi sallama ta shigo, cikin shiga ta kamala, ko ina a jikinta rufe rub. Hannunta riƙe da ƙatuwar leda.
"Mama Aikin gyaɗa kike yi? Bayan kinsan duk ran juma'a da asabar muke yi miki in mun zo. Ki dinga hutawa. Baba Mariya ina wuni, Baba Hindu ina wuni?" Mariya ce kawai ta amsa, Hindu kuwa kunnen uwar shegu tayi da Shatu. Hannatu taja tsaki tace.
"Aikin banza, aikin wofi, bayan munsan komai, ana zaune a binni ana tazubas" wani abune ya caki ƙirjina dajin kalmar da Hannatu ta jefi yarta dashi. Duk da inajin ana jifansu da kalmomi iri_iri, cewar na barsu sun tafi karuwanci a birni, sunƙi aure, sai yawon ɓel_ɓel. Shatu tayi murmushi, ta girgiza kai, dan rayuwar da Hannatu take gudanarwa rayuwace ta abun tausayi. Shatu tace.
"Mama dama tafe nake da baƙo yana waje, yace lallai_lallai shi yana son ku gaisa. Oganane a wajan aiki, kuma muna mutunci sosai, yana yawan rage mun hanya" murmushi nayi, ina kallon Shatu wacce ta zama ƴar gaye, tamkar ba'a tsakar gidannan tayi rarrafeba. Wato shi ilimi har ƙarama mutum kyau yake yi, gashi da sa kwarjini.
Yi maza ki shigo dashi, kaji ƴar nema shine kika barshi a waje?" Dariya tayi mun, ta fita zuwa shigo da baƙon nata. Ni kuma na shiga ɗaki na shinfiɗa mishi ƙatuwar daddumar da Zaliha ta sai mun." Ina zaune sai na jiyo sallamarsu, baƙon Shatu na gaida mutan gidan. Da sallama suka shigo. Cikin girma da karamci muka gaisa, kansa a ƙasa cike da tsantsar jin kunyata. Nace.
Ya sunan malamin? A kunyace yace.
"Sunana Isma'il dama kullum ina cewa ta gaisheki, sai yau Allah ya nufa nace bari dai, inyi tattaki inzo mu gaisa, dan zuwa da kai yafi saƙo." Murmusawa nayi. Nace.
Zahiri Isma'il. Kuma naji daɗi Allah yayi albarka. Shatu bashi ruwa yasha mana" Fita nayi na dawo tsakar gida na basu waje. Ina zama Zaliha da Basira suka shigo, a jere tamkar tagwaye, komai iri ɗaya suka saka na sutura. Suna ajjiye ledojin hannunsu, suka shiga baza mun ɗanyar gyaɗar da nake aikinta." Buguzum_buguzum Audu ya shigo gidan, bakinshi duk dabzar goro, yana kumfar baki yace.
"Ina karuwar ƴarki naji ance ta tawo da daduronta sun shigo nan gidan ko? Duk lalatar da suke aikatawa a birni bai ishesu ba har sai sun kawo mun daduro cikin gida? Ke wato magajiya harda basu waje." Kallo nabi Audu dashi, raina bai taɓa ɓaci makamancin irin na yau ba. Amma bana son tanka mishi dan gudun kar hakan ya taɓa darajar Shatu. Hindu ta nuna ma Audu ɗakina da bakinta, karab a idanuna. Harya nufi ɗakina, ya dawo ya fisge ledojin da su Zaliha suka shigo dashi ya zazzage. Kaji gasassu, da lemon roba ƙatuwa, da taliya, bushashahen kifi, da maggi, da farin mai, da tumaturin gongoni, da kayan abinci iri iri cimar ƴan birni ya gani sun zubo daga ledar nan. Baki ya rike, ya ɗauko kajin a ƙasa yace."
"Gaskiya naga kin sake, sai walƙiya kike yi. Ashe ribar bariki ake kawo miki. Ke Hindu zo ki tattare kayannan ki ajjiye mun a turakata. Yana kaiwa nan ya wuce fu zuwa ɗakina. Da mugun gudu Hindu ta iso gaban kayan, ko nauyin jikinta bata ji, ta hau kwashe kayan. Ni kuwa adda'a duk wacce tazo bakina furtata nake yi. Hawaye sai suntiri yake yi a kumatuna. Su Zaliha ma sunyi tsumu_tsumu tamkar an watsa musu ruwan zafi." Fisgo Ismail Audu yayi waje. Sai zabga mishi mari yake yi, tamkar ya samu maƙiyi a filin dambe. Jama'a aka taru, dan Audu sai kwakwaso yake ta faman yi, tamkar kaza mai ƴaƴa. Ismail da yaga Audu na shirin illatashi, aiba shiri ya zame, ya fice a gidan da fashashshen baki. Shatu ya shaƙo yana shirin illatamun ita. Kukan kura nayi na fisge Shatu a hannun Audu. Audu daya zuchiya, saiya rufeni da wani irin mahaukacin dukan da ko sanda nake da jini a jika bai taɓa yi mun irinshi ba. Faɗuwa ƙasa nayi hangurarriya ( sumammiya) Ban kuma sanin kaina ba, sai farkawa nayi na ganni a gadon asibiti, tsintsiyar hannuna ɗaure da ruwan bature. Fuskata tayi wani irin mugun nauyi, idanuna ma basa gani sosai, ko buɗuwa basa yi"

[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: *_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_

*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_

*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_

_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_

1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._

_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*

_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_

Mrs Bukhari[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: GAWURTATTU UKU

LAMBA TA GOMA SHA TARA
Saleri:
Chapter 24 · 0% Book details