← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 40

Sashe 22

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Malam. Gani gaku ku dangin Ɗahiru. Ga Zainabu ta wajena. Ga Binta, ga mahaifinta malam Ayuba. Ita waccan bazawara ta fita a cikin zancan tunda tayi aurenta. Amma ga malam Rabo mahaifinta yace yana son abi mishi hakkin ƴarshi. To duba da mutuncinku da nake gani, Malam da Baban Yara. Wallahi da tuni wani labarin akeyi ba wannan ba. Matasanmu ma zasu iya yin komai. Amma anyi zama na amana tare daku, kuma baku goyi bayan Ɗahiru kan taɓargazar daya aikata ba. Zainabu ta wajena, tunda wannan iftila'in ya dira a kanta. Du maneman ta suka tarwatse. Shekara sama da goma yarinya tana gabanmu, ƙannenta sai hayayyafa suke a gidan mazajensu. Binta tayi Auren harta haihu a gidan Aure, amma surukai suka sata a gaba har sai da a ka sakota, taci gaba da ɗanɗanar baƙin ciki a ƙauyannan. Yarinyar malam Rabo, ta samu tayi wani auren ita Allah ya rufa mata asiri. To sai ga labarin dawowar Ɗahiru cikin wannan gari nawa. Ina fatan zaku bi umarnina, shima zai ɗauki duk hukuncin da zan zartar akanshi? Domin a samu sulhu. Tunda yarannan suma da nasu laifin, ai ba fyaɗe yayi musu ba. Duk da muna jin jita_jita a gari cewar. Yana amfani da kwallin ƙiful danya cinma mummunar manufarshi akan duk yarinyar da tayi mishi. Fada tana son ganin Ɗahiru." Malam yayi gyaran murya yace.
"Allah ya gafarta mai gari. Ina ganin ko babu Ɗahiru ni tamkar uba nake a wajanshi. Kuma Allah yana gani dai_dai da sakan ban taɓa mance ɓata sunan gidanmu da Ɗahiru yayi ba. Yanzu haka Shehu yana can yana nemoshi." Shehu ne ya ƙaraso cikin shagon, Ɗahiru na biye dashi. Suna zama yaron Iyami ya iso. Tsugunnawa yayi ya kwashi gaisuwa sannan yace.
"Kawu Ɗahiru ana nemanka a gida. Umma Tani tana naƙuda." Zumbur Ɗahiru ya miƙe. Sai yayi kwarjini sosai a idanun jama'ar wajan. Aikin Tsubbu ya soma tasiri a jikinshi.
"Aimun afuwa mai gari. Amma ga Malam zaiyi komai. Kuma ina mai ba kowa haƙuri nayi kuskure nai laifi. Na kuma yi nadama. Kaina bisa ƙasa ina neman aimun sassauci. Yana kaiwa nan ya fita a shagon. Da mugun gudu ya falfala." Malam yace.
"Ni a shawarce mai gari. Mai zai hana a haɗu a rufa ma juna asiri. Yarannan tunda ga iyayensu. Muna nemama Ɗahiru aurensu. Ko ba komai wannan sirrin zai iya birne kanshi, duk da masu iya zance na cewa kunne ya girmi kaka. Amma yarannan da aka samesu bata hanyar aure ba. Kasancewar iyayensu a ƙarƙashin auren zaiyi musu rumfa, tunda Ɗahiru mahaifinsu ne. Malam Rabo muna roƙonka kayi haƙuri ka yafe hakkin ɗiyarka tunda tayi aure abunta." Fada ta ɗauki shiru na wasu lokuta. Dukkansu sun gamsu da shawarar Malam, duk da yaran babu wanda suka tsana duk duniya sama da Ɗahiru. Amma da yake su mata ne, sai suke ganin zama ƙarƙashin inuwar auren wanda ya salwantar musu da budurcinsu, kamar ya fiye musu. Badan komai ba ko dan su fita daga halin tsangwama da kyarar da akeyi ma ƴaƴan da suka haifa a gaban iyayensu. ( Ita mace a kullum tunaninta ta yaya zata samama yaranta kyakykyawar rayuwa mai inganci? Ita mace duk sanda ta zama uwa. Duk wani hange, da hasashenta akan, yaranta yake ƙarewa. Koda ita bazata samu ingantacciyar rayuwa ba. In dai yaranta zasu yi farin ciki da hakan, ta gammaci ranta ya zame ma yaranta fansa) ( Allah ka shiga lamarin iyaye mata ka taɓa, ya Allah ka kawo sassauci da rangwame a rayuwar iyaye mata. Ka dasa ƙauna, da soyayya mara yankewa a tsakanin yara da iyayensu Ameen.") Mai gari yace
"Na gamsu da bayaninka malam. Kuma na amince da shawararka. Amma a yanzu ku fidda sadaki, a ɗaura auren a yanzu anan, kowa ya huta. Ku mata matan na sallameku." Tashi suka yi, suka fice. ( Iyaye mazan kuma suka yadda yaransu su auri wanda ya lalata musu rayuwarsu. Badan komai ba, dan gudun bakin duniya. Basu yi duba da wacce irin rayuwa yaran zasu fuskanta a wajan miji, da dangin mijin ba. Basu yi tunani akan tsawon shekarun da Ɗahiru ya ɗauka bayanan ba, wanne hali yaje ya kwafo, ya ɗaura akan halin akuyancin da suka sanshi dashi? Oho ba wannan bane abun dubaba a wajansu. Abun duban a wajansu. Sun ya da kwallon mangoro sun huta da ƙuda) A wajan malam ya ciro abunda ke ajjihunshi, Baban Yara ma ya ciro nashi, Lauwali ma ya saka nashi. Shehu ya zura hannu a ajjihu sai yaji wayam. Shi dai yasan da kuɗi a jikinshi. Murmushi yayi daya tuna ashe a ɗaki ɗaya suka kwana da Ɗahiru, yasan tabbas shi ya yasheshi. Mai hali baya fasa halinshi. A wajan lauwali ya ari kuɗin ya saka. Take aka ɗaura Auren Ɗahiru da zainab, da Binta. A bisa sadaki jaka huɗu. Kuma aka ƙare zaman akan da daddare za'a kawo mishi matanshi, da yaranshi biyu. Mace da namiji. A haka taron ya watse.

Tani:
Mahaifiyarta da ƙannenta ne a kanta. Dan tun safe suka zo gidan, dansu gane ma idanunsu gaskiyane su Tani sun dawo? Dan tuni aka cire rai dasu. Sai kuma suka zo suka sameta a halin naƙuda. Jini sai zuba yake yi a jikinta." Ɗahiru daya shigo gidan a guje, sai yayi ɓarayin su matar Malam. A ƙofar ɗakin matar Malam ya ga dafifin mata, ko wacce hannunta riƙe da kumatu. Turesu ya dinga yi yana kutsa kai. Ganin iyayen Tani ne a kanta, hakan ya matuƙar kashe mishi jiki. Amma a hakan ya daure yace.
"Baba ku ɗan bani minti biyu, akwai wani taimako da zanyi mata ne. Yanzu zata sauka. Ba tare da sunyi tunanin komai a zuchiyarsu ba. Suka bashi waje. Kallon idanun Tani yayi, a runtse idanunta suke, bata ma cikin hayyacinta. Ƙoƙonnan ya ciro a aljihun ƴar shararshi, yasa hannu ya dinga kwarfatar jinin daya zuba a ƙasa, yana katse hannun nashi a bakin ƙoƙon. Ta cikin riga ya saka hannunshi riƙe da ƙoƙon. Wuf ya fice a ɗakin yana waige.
"Inna ku shiga, yanzu zata sauka" Ya wuce har yana shirin faɗuwa. Matar malam sai rangaɗa mishi kira take yi. Amma banza yayi da'ita, har saida yaje ya nemi waje ya adana ƙoƙonnan, sannan ya dawo. Ya samu Tani ta suntulo ɗiyarta mace, gyarasu ma akeyi. Matar malam ta yafatoshi suka koma gefe.
"Ɗahiru zabin da naga kaba Iyami ta gyare ta soye, na meye wai? Baki ya washe yace.
"Sadaka ce za'ayi mun Matar Malam. Kinsan dana je binni na koyo ilimin malumta irinna Malam, zan ɗan dinga taimakon jama'a masu ɗauke da ciwo ayi musu rubutun ayoyin Alkur'ani, da yardarshi da amincewarshi su samu lafiya. Masu ɗauke damuwa kuma a tayasu roƙon Allah. Wannan sadakar ta neman yardar Allah ce." Dariya Matar Malam tayi tace.
"Ai hakan yafi, da ƴan tsalle_tsallen da kayi. Ƴan satar kajin maƙota duk an daina" Ɗariya yayi yace
"Matar malam baki da mantuwa gaskiya. Miƙon mahaifar in burne, sai in koma fada na baro su malam anata fafata sharia." Mahaifar Matar Malam tasa Baba mai riga ta miƙo, aka ba Ɗahiru. Itama yaje ya adanata a inda Aljani kayanasu zai gani ya ɗauka. Ya nufi hanyar fada yana tafe yana surukai. "Ai nayi kuɗi na gama, zan kai Tani ta sauke farali, nima inje inyi adda'a, inga masallacin ma'aikin Allah" Kaciɓus yayi dasu malam a hanya.
"Kai dai baka da hankali kana tafe kana shashanci. Ya jikin Tani ince ta sauka?" Cewar Malam. Ɗahiru yace
"Ta sauka Malam an samu mai sunan Goggo. Kun gama da fadar ne?" Baban Yara yace
"Mun gama, kuma an samu fahimtar juna. Malam zaiyi ma bayanin komai. Allah ya raya Goggo" Shehu daya lula duniya tunanin ɗan da Laila ta haifa mishi. Yanzu da Ɗahiru yake faɗar haihuwar matarshi, sai yake jin inama shine aka haifama lafiyayyar jaririya. Ko mai ya tuno kuma oho, sai yayi murmushi harda girgiza kai."
Suna isa ƙofar gida, Malam ya zaunar da Ɗahiru yayi mishi bayanin komai. Take Ɗahiru ya shiga lashe baki, yana tunano irin romon daya sharɓa a wajan su Zainabu. Yayi farin ciki sosai da wannan aure, dan murna ma, har tashi tsaye yayi ya dinga yi ma kanshi kirari. Baban yara yace
"Sai kasa matan ƴaƴanka su share ɗakunan da suke can cikin gida, ta bayan sakaki can nesa, ɗakuna huɗu ne a jere falle_falle. Kaga kowa saita ɗauki ɗaya, kaima saika ɗauki ɗaya. Kayi haƙurin zama dasu, yara da suka haifa maka kuma. Ka tausaya musu Ɗahiru." Ɗahiru kamar na Allah haka yaita godiya. Kuma yayi musu bayanin irin wanda yayi ma Matar Malam kan malunta da zai soma. Sunyi murna dajin hakan sosai. Da yamma lis aka kawo amare.
Chapter 22 · 0% Book details