← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 40

Sashe 11

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_

*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_

*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_

_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_

1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._

_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*

_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_

MRS BUKHARI
MATA IYAYEN GIJI

BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)

( GAWURTATTU UKU)

INA MIƘA SAƘON GODIYATA GA HAƊAKAR MARUBUTAN NAJERIYA BISA SHAIDAR KARRAMAWA DA SUKA BANI, AKAN LITTAFINA MAI SUNA ( UNGULU DA KAN ZABO) NAGODE MATUƘA ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI. INA MIƘA GODIYATA GA SHUWAGABANNIN HAƊAKAR MARUBUTA, DA ALƘALAN DA SU KAI ALƘALANCI.

*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*

SAMFOTI

LAMBA TA TAKWAS

BAKORI:
Da isar Shehu Bakori bai zarce ko inaba, sai ƴar kasuwa wajan mahaifin Laila malam Zangina. Inda anan yake kasuwancin sai da musullar ƙarfe, da musullar da ake cirewa a jikin bushiya da matajin kai na katako, da wuƙaƙe masu ƙota. Wannan itace sana'ar mahaifin Laila, taburin dake kusa da nashi kuma teburin wan Laila ne Jibirila. Shi kuma yana siyar da, kayan aikin gona. Garma, ƙota, cebur, da sauransu. Haka Shehu ya ratso kasuwar nan yazo wajan mahaifin Laila afujajan.
"Shehu kaine tafe afujajan haka? kar dai almurar yarinyar nan ta kuma tawowa ne? Ka haifi yarone baka haifi halinsa ba, amma zanje gidan in bata kashi yanzu." Shehu da yake duk a burkice, dan ana tafe a hanya yana tunano mata mazan da Laila ta haifa mishi, wannan wacce iriyar ƙaddarace haka? Yace.
"Ba kuma fitowa tayi ba. Ta samu kaine"
"A masha Allah, tana dai lafiya ita da abunda aka samu ko?"
"A'a gaskiya, ita da jaririn duk ba lafiya, Laila bata san wanda yake ma kanta ba, jini ne ya ɓalle mata wallahi, saida aka jiƙa mata manda tasha. Jaririn kuma mata maza ta haifa " wani zumm mahaifin Laila yaji a jikinshi, yayi shiru yana nazari irin nasu na manya, ya tausaya ma ɗiyar tashi gaya, kafin daga bisani yace
" Hmmmm Allah ya bata lafiya, shi kuma yaro Allah ya raya shi da imani. Muje gidan in sanar ma da mata, in yaso sai a samu mata su bika ko?"
"Toh" kawai Shehu yace, dan hatta mahaifin Laila Shehu haushinshi yake ji.
"Malam tsalha ga kayana kayi mun jira, yanzu zan dawo" malam Tsalha abokin malam Zangina ne sosai. Zungui_zungui suke tafiya kowanne cikinsu da abinda yake magana akai a cikin zuchiyarshi, Malam Zangina sai tunani yake yi, gami da taraddadin halin da iyayen Laila mata zasu shiga, in sunji halin da take ciki, da kuma abunda ta haifa, dan a wannan zamani mata maza tamkar mayu, ko aljanu aka ɗaukesu, gidan da akwai mata maza ma, ba'a aiken yara gidan, kuma an camfa cewar iyaye suna shiga halin fatara da shiga iftila'i kala_kala da zaran sun haifi mata maza. Har suka iso gida, malam Zangina tunani yake yi, hankali, da nutsuwa, basu da gurbi a jikinshi tsabar kaɗuwa. Tare suka shiga gidan da Shehu. Malam Zangina shi ya Faɗama su Ta asibi da Daddo halin da Laila take ciki da abinda ta haifa kuma. Take Ta Asibi ta soma zubarma da ɗiyarta hawaye. Dan tasan mutanenmu na ƙauye zasu camfa Laila da yaronta, ƙila ma a ɗaura musu karan tsana. Gabaki ɗaya suka tashi hankulansu, Shehu sai kallonsu yake yi, yana jin wani mugun haushinsu na ɗarsuwa a ranshi Daddo cikin murya mai cike da karaya tace.
"Malam to yanzu yaya za'ayi maganar tafiyar?"
"Ke da Laraba saiku je, amma ke dubota zaki yi ki dawo, ita Laraba saita zauna da'ita zuwa kafin su tawo wanka. Shehu ka shiga ka sha ruwa, zanje Fada in tambayi mai gari mijin ƙanwar tawa izini, sai mu tawo ku wuce." Fitarshi da mintuna talatin, sai gashi shi da Laraba ƙanwarshi, itama a kiɗimen take sosai.
"Daddo fito ku tafi, zan aiki wannan yaron yaje ya sanar da ƙannenshi batun haihuwar, ranar suna sai su ɗunguma suje." Daddo ta fito da ƙunshin kayanta a ƙunshe a ɗankwali, Ta Asibiti ta fito da ƙunshin yajin daddawa, da soyayyen man shanu, da yajin gauta, ta miƙama Laraba.
"Kuje Laraba Allah ya bata lafiya. Laraba tace.
"Amma Yaya itama Daddon ka barmu muyi zaman mu a can, ita saita kula da Laila, ni kuma inji da aikace_aikace koya kace Yaya, sabida Laila tana buƙatar kulawa kasan haihuwar fari ce?" Malam Zangina ya gyaɗa kai yace.
"Babu komai Laraba kuje ɗin." Kama hanya suka yi, Shehu na biye dasu a baya sai wani cin magani yake yi. A haka har suka isa Saleri yana zabga uban fishi da dana sanin auren Lailan ma baki ɗaya.
"Ahuwanku dai masu gidan" inji Laraba kenan. Matar malam wacce fitowarta kenan daga ɗakin Laila tace."
"Laraba sannunku da hanya, kun shawo rana, ku shiga ba insa a kawo muku ruwa." Da sallama su Laraba suka shiga ɗakin. Amman ganin irin halin da Laila ke ciki ya sake ɗaga hankalinsu sosai. Matar malam ce ta shigo da sallama, Baba mai riga na biye da'ita da kaskon wuta. A kusa da gadon Laila ta ajjiye kaskon, ta zuba tazargade a cikin kaskon. Jaririn ta ɗakko ta dinga busa mishi hayaƙin tazardagennan maganin mayo ne wanda ake amfani dashi a ƙasashen Hausa dan korar maye, kuma ana yima wanda ake zargin Mayu sun shafeshi.
"Mai riga ni ina ganin bai dace ace an bar yarinyar nan a gida ba, kamata yayi a tafi da'ita asibiti." Inji Laraba kenan. Matar malam tace.
"Ana ƙoƙari akan lafiyar tata, kinga kofin rubutu yanzu malam ya aiko, aka shafe mata jikinta dashi. Baban yara kuwa ya shiga jeji zai tsinko mata magani, ya farauto mata naman gashi, kar a raina ƙoƙarin Laraba ayi haƙuri" Baba mai riga tace.
"Kinsan ƴan birni duk inda suka kai suka kawo sai sun raina baƙauye. In banda raini Fulani Laraba, ina ke ina maganar asibiti a nan gidan na mafarauta, ƴan na gada ba ƴan haye ba. Daga nan cikin gida Shehu zai iya kiran zomo ko gada, kuma dolenta tazo, harmu za'aima zancan banza?" Laraba ta buɗe baki zata mayar ma da Baba mai riga martani. Daddo ta haneta ta hanyar girgiza mata kai, sannan tace.
"Mai riga ayi haƙuri kinsan sha'anin yara. Fatanmu Allah ya bata lafiya." Shehu ne yai sallama ya shigo.
"Matar malam, malam yace a bada jaririn, wanzami yazo zai dubashi ko da maganin da zai bayar." Laraba tasa hannu ta ɗakko jaririn taba Shehu. A mugun wulaƙance ya karɓi yaron, yana wani huhhura hancinshi, ala dole waishi an cuceshi."
Chapter 11 · 0% Book details