Sashe 27
Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Audu:
Yana zaune yana shan fura, Hindu kuma tana gefenshi sai sake zuga shi take yi akan lallai, ko a cikin gidanne tunda da samari, ya tursasa musu su auri su Shatu kowa ya huta."
"Damma baka zuwa sha'ani, da kaji yanda ake zagin Shamsiyya da ƙattin yaranta. Kuma abun takaicin, zagin har takan nawa yaran yake sakkowa. Yanzu Hannatu, mane minta cewa fa yayi in da gaske su Shatu yayyenta ne, bazai iya aurenta ba. Cikin dabara yanzu nake son tayi mun kiran yaron mu zauna mu tattauna" Audu yace.
"Shawararki mai kyauce sosai Hindu, ni kam nayi dacen samun mace mai hangen nesa. Aini ban tuno da samarin gidan ba, da bazan fita har dawa ina shelar masu aurensu ba." Sallamar Salame suka jiyo a ƙofar ɗakin. Hindu ta amsa mata."
"Baban Shatu, mai gari ne ya aiko ayi kiranka. Manzannin suna waje"
"To gani nan Salame" Miƙewa yayi, yasa babbar riga, ya kifa hularshi.
"E bari inje ɗin Hindu, ƙila an samu wanda ya daki ƙirji zaiyi jahaɗin auren ɗaya daga cikin yarannan ne" Yana kaiwa nan ya fita. Hindu ta sauke ajjiyar zuchiya na cin galaba akan raba Audu da yaran Musina data yi." Zainaba ce ta shigo cikin ɗakin hindu da kururuwar ihu, fuskarta duk a kumbure, da halama duka taci sosai."
"Ma'aikin Allah na madina ni Hindu. Haɗarin Bodi kuka yi ne Zainaba?" Cikin kuka tace.
" Fatsima ce tasa Tanimu ya rubuta mun takaddata saki uku. Kuma yace in tawo da yarana baya ƙaunar mu. Bayan tasa yayi mun mugun duka." Ɗiyar Zainaba ce ƙarama ta shigo mai sunan Hindu. Ga goyo ɗanye a bayan Zainaba."
MRS BUKHARI[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA ASHIRIN"
INA MIƘA ƊUNBUN GODIYATA S GAREKU MASOYA RUBUTUNA. HAƘIƘA WANNAN LABARIN YA KAINI WANI MATSAYI DA MATAKIN DA BAN TAƁA TUNANIN ZAI KAINI BA.
HAJIYA TURAI NAGA SAƘO INA GODIYA MAI TARIN YAWA.
YAWALE:
Ƙarema yarana kallo yake yi. Masha Allah ko wanne cikinsu ya ginu da tarbiyya, gasu da mugun haɗin kai da soyayyar junansu. Gashi kowa yana da abun hannunshi. Yaran mowa Kumatu kuwa, Saminun ne dama dama a cikinsu, amma du sauran basa sana'a sai yawon ɓel_ɓel da bin inuwa. Muttaƙa kuwa yayi nisa baya jin kira. Yanzu haka yana can a kulle a kurkukun bayan gari, mai gari yasa an kamoshi shi da abokan satar tashi, ya garƙamesu a mari. Babu irin bori da tumamin da Kumatu bata yi ba a tsakar gida."
"Musina nayi mamakin abunda kike shirin sa yarana suyi. Wata kam ba kya ƙaunar kiga muna zaune lafiya. Shin me Kumatu tayi miki da kika ƙi jinin yaranki su haɗe kansu da yaranta? Duk abinda yaranki suka kawo miki sai dai kici ke kaɗai. Kin nuna musu banda galihu a wajanki, kuma baki basu tarbiyyar su kula da Yadikkonsu Kumatu ba. Wai dam ɗiban albarka har Jamilu ya mallaki garjejen fili a ƙauyannan amman ni ubanshi banda labari Musina, ga gonakai daya mallaka da sa hannun mai gari amman ni ina nan hoto jibi yanda na dawo dan tsabar wahala komai nawa ya ƙare, dan baƙin hali yarana dana arziki amman kin hana su taimaka mun. Wallahi zan kafa dokoki a gidannan kuma dole abi, zaman zai sauya ko dan haɗin kan yaranmu. Ni dai bance uhm ba, bare um_um jira nake ya gama zazzago duk abinda yake cikinshi tukunna, su Jamilu sunyi tsuru_tsuru suna kallon mahaifinsu, ba'a taɓa yin zama irin wannan ba a gidannan sai yau.
"Daga yau duk abinda yaran wajanki suka siyo suka kawo miki, na ci, ko sutura, to dole su siyo da Yadikkonsu, in basu da halin yi muku duka, sai suyi haƙuri. Nan Alawiyya take wucewa da babban buhu shaƙe da kayan alatu, bushashahen kifi a miyarki kamar zaiyi magana, amman baki basu tarbiyyar su kula dani ba. To itama duk wata inya ƙare duk abinda ta siyo a raba da Kumatu. Jamilu da yake ɗiban hatsin da bai wuce rabin buhu ba ya bamu, shima na soke dole ya raba duk hatsin daya samu gida biyu, rabin a rumbunki, rabi a rumbun Kumatu bayan ya ware na siyarwa. Kema Kulu inajin labarin jar biya da kike kawo ma uwarki cike da zabi duk wata. Daga yau ko ki haɗa da Kumatu ko ki bari.Ita kanta Kattume ƴar gatan uwa da tana wajan zamannan wallahi saina bigeta ma, dan inajin hidin_dimun da take yi ita da mijinta a gidannan, amman dai_dai da hatsi baki taɓa bari ta auno bata Kumatu ba. Sannan Alawiyya da Zubaida duk su fitar da mijin Aure na gaji da ganinsu a gabana anayi mun ɗan kallo a gari. Wani iri numfashina yake yi, da ba dan yara ne a gabanmu ba, da yau Yawale yaga hau irin namu na masu haƙuri. Waigowa yayi wajan su Jamilu da suke jere da Saminu.
"Kai Jamilu na haɗaka da Zulai ƴar wajan Yayana Jamilu ka aureta, mun gama maganar da Yaya Jamilun, tuwona maina. Kai kuma Mustafa sai ka auri marka yarinyar Mudi duk a haɗe ayi auren dana Ƙasimu. Ke kuma Sauma'iyya mun gama magana da Zaidu zai aureki ya haɗaki da Harira zaki ci gaba da zama a cikin gidannan. Gida bai ƙoshi ba baza'a kaima dawa ba. Alawiyya, Zubaida, ku fidda mijin aure nanda mako guda in ba haka ba. Akwai samari fal gidannan zan tilasta musu su aureku, duk da baza su so auren fitsararru irinku ba. Ƙasimu ka samu Saminu zai yankar maka fili, kuma Jamilu ku sameshi a yanka muku." Kallon Yawale kawai nake yi, ko kunya baya ji sai hukunci yake zartarwa akan yarana dana gama wahala akansu. Har yake tunanin haɗa Jamiluna da Zulai yarinyar data zubar da ciki watan jiya, yawon bin maza take yi kwararo_kwararo. Ita kuma Marka ba ƙaramar fitsararriya bace, dan ko aiki,ko aike uwarta bata isa ta sanyata ba, sune za'a aura ma yarana, dan anga Allah ya tallafi rayuwarsu komai ya wuce rayuwa tayi mana shar. Su Jamilu sai kallona suke yi, kallo irinna kiyi mana rai. Ni dai Yawale da Kumatu nake kallo kawai, cike da maɗaukakin mamaki.
"Sannan Kumatu zanci gaba da muku rabon kwana ke da Musina, kuma duk nauyinta dake kaina zan sauke mata, fatana ku zauna lafiya.'
Kutumar bura ubanka, Yawale kaine kake faɗen haka da bakinka?" Bansan sanda bakina ya subce na narko wannan ashariya a gaban yara ba. Duk suka kalleni, nayi maza na sauke kaina. Yawake kuwa sai murmusawa yake yi, babu halamar fishi ko tunzura akan ashariyar dana narko mishi. Kallon su jamilu yayi yace.
"Ku tashi ku tafi, na sallameku Allah yayi muku albarka, ayi haƙuri kuma a yafi juna. Komai ya wuce yaran kirki" sai washe baki Yawale yake yi, nasan dukiyar hannunsu yake kallo kawai. Ina kallo yaran suka watse, ai fitarsu ke da wuya na miƙe.
Yawale bari kaji in faɗama, aure ni da kai ya ƙare daga yau, yau kaji kana son ka sake mayar dani matarka, sabida yarana sun samu arziki. Ni kuma ina baƙin ciki kaci dukiyarsu. Har hake cewa wai duk abinda suka kawo mun su ba Kumatu. Da kai da Kumatu Allah ya tsine muku albarka, ƴan iska, ƴan kutumar uba. Kuma wallahi babu ɗana guda ɗaya da zaiyi aure a zuriyarka. Yarona daya salwanta sanadiyyar sharrin da Kumatu tayi mishi. Bazan yafe ba, sai wutar Allah ta ciku." Da Yawale da Kumatun duk baki suka buɗe suna kallona. Dan na fusata ainun, shi kuma Yawale sai lallashina yake yi, sabida yana son cin banza. Kumatu tace.
"Musina Yawalen kike zagi haka? Wani mugun kallo na jefa mata nace.
"Dake dashi kun yayimi ƙwanyar bura ubanku, wakilin ɗaurin aurenku yaci uwatai. Haka na fice a ɗakin kamar kububuwa, ina huci dan jikina har kyarma yake yi mun, na koma nawa ɗakin. Duk yaran suna tsaitsaye sunyi cirko_cirko. Su kansu basu taɓa ganina a cikin irin wannan yanayin ba. Hakanne ya tilasta musu yin shiru, gudun karsu faɗi wani abun da zai kuma tunzurani. Kulu ta kasa tafiya gidanta, da dukkan halamu kwana zata yi, matan duk suka baibayeni"
Mrs Bukhari
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: GAWURTATTU UKU
Lamba ta Ashirin da ɗaya
BAKORI: