← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 40

Sashe 36

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_

*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_

*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_

_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_

1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._

_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*

_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: GAWURTATTU UKU
LAMBA TA ASHIRIN DA BAKWAI
MRS BUKHARI

SALERI:
Zufa ce ta shiga yanko musu dukkansu. Haƙiƙa sunsan sun cutar da Musina da yaranta. Kuma haƙiƙa Idi gaskiya ya faɗa, Musina bata da wani amfanin da take ma Yawale, tunda ba rabon kwana yake yi da'ita ba. Kuma ba ciyar da'ita yake yi ba. Bata da maraba da me zaman kai. Jamilu ne ya daure yace.
"Haba Idi bai dace kace hakan ba, ba daidai bane ka kashema Musina aurenta ba. Yawale dai mahaifinku ne, kuma mijin musina ne, ni ina ganin ayi sulhu, tunda dai mun gane kuskurenmu, shi kanshi Yawalen zai sauya." Jamilu na wajena yace.
"Kawu rabuwar ita muke fatan ta zama alkhairi in sha Allah, ya saketa kawai, ta tattare kayanta mu baku iska." Ƙasimu yace.
"Nima ina bayan ƴan uwana, sakin dai muke nema. Ɗaya bayan ɗaya yarana duk suka ce saki suke buƙata. Ni dai ina gefe ina jin bidiri, lallai yara ni'ima ne babba, duk uwar da take da yara. Ta tsaya tsayin daka dan ganin ta basu tarbiyya mai kyau. In sha Allah gaba zata yi dariya. Yawale yaƙi magana fur, sai su Jamilu ne suke ta ba da haƙuri. Daga baya Yawale yace.
"Kuimun afuwa yarana, Musina ki gafarceni, tabbas ban cancanta inta riƙe igiyar aurenki ba. Amman rabuwa dake zai iya zamemun sular lalacewa, domun kece filita madubi a rayuwata. Amman in dai kin zaɓi yaranki akan aurenki, zan baki iska yanzu." Nafi minti uku banyi ko tari ba. Idanun yarana sai yawo suke yi a jikina, dan duk sun kafa mun idanu. Sai naji tausayinsu, da ganin nabi umarninsu.
Farin cikinsu shine nawa, dan sune uwa, uba, dangi a gareni. Dan haka ka sauwaƙe mun, kaje ka rungumi yaranka da matarka abun soyuwa a gareka." Yawale yana hawaye yai mun saki ɗaya. Wallahi sai naji na sauke nannauyan ajjiyar zuchiya, ji nake tamkar an sauke mun wani ƙaton dutse a ƙirjina ne. Farin ciki ya ziyarceni. Yarana sukaita lallashina. Da yamma lis Idi yasa ƙannenshi a gaba zuwa gidan Kattume dan ya ganta, su sanar mata halin da ake ciki.

Kattume:
"Kai Yaya Idi, a gaskiya naji daɗin hukuncin da kuka yanke sosai. Uwo wallahi tausayi take bani. Tasha wahala sosai duk sabida mu. Amman Alhamdulillah gamu mun rayu, kuma muna tsantsar jin sonta da tausayinta. Wallahi duk ɗan ragowar kuɗin cefane inna rage, Uwo nake hidimtawa dashi, duk dan in bata farin ciki. Baba Kumatu kuma in sha Allah ƙarshenta ne yazo"
Sun jima suna tattaunawa, sannan suka jira mijinta ya dawo, dan suna son Kattume ta bisu, tayi sallama da Uwo. Izinin binsu mijinta ya bata, yaronta na goye kawai ta goya suka tafi.

Saleri:
Yawale:
Jiki a mace mus Yawale ya shiga ɗakin Kumatu. Tattaunawa ya samu sunayi ita da yaranta. Kumatu tabi kayan tsarabar da Idi ya ba Yawale da kallo.
"Malam sai yanzu ka shigo? Kayan hannunshi ka karɓa kai ka mance Idi Ɓarawone, kasan ko sana'ar sata yake yi a birni? Ance fa harda mota yazo." Yawale ya zauna a ƙasa, ya ajjiye kayan a gabanshi, ya dubi Kumatu yace.
"Kece kika haifi Ɓarawo Kumatu, Musina bata haifi ɓarawoba, amman ɗanki me yake yi inba sara suka ba? Duk garinnan ansan ɗanki sara suka ne, tunda har zaga gari akayi dasu, yara na jifansu, sakamakon nakasa ɗan mai gari da suka yi. Kumatu kin cutar dani gaskiya da yawa. Idi yasa na saki Musina, wallahi kwarjinin yaranta ne yasa dole na saketa. Kema na sakeki saki biyu, ki tattare ki koma gidanku.'" Hannu Kumatu tasa aka, taita kururuwa tana ihu.
"Yawale ni ka saka, bayan ka gama cinyemun ƙuruciyata? Ina zanje to? Narantse da Allah babu inda zanje, zanyi zaman ƴaƴana, tsofai_tsofai dani, iyaye duk sun kwanta dama kace ka sakeni." Yawale yace.
"Kamar yanda kika sa ƙuruciyar Musina ta ƙare ba tare da taji daɗin aure, da ɗaɗin miji ba ba. Ai kukan kurciya jawabine, mai hankali yake ganewa. Kayan daya shigo dashi ya ɗiba ya fice a ɗakin.

MUSINA:
Washe gari da sassafe Jamilu ya jibga mana kayanmu a mota. Haka na dinga bin maƙwabta ina sallamarsu. Maƙwabta suka rakoni har gaban mota, suna ɗagamun hannu.
Kallon gidan da aka kawoni tun ina yarinya nake yi, gashi na bar gidan ina da girman shekaruna. Tun ina hango gidan harna dena gani. Tunanina bai tsaya ba har saida muka iso Azare. Nanma haka naita sallama da ƴan uwana. Sukaita taya ni murnar ganin Idi. Ina kuka wiwi na rabu da dangina, muka nufi Jos. Tafiyar awa ɗaya da rabi muka yi, sai gamu a Jos garin sanyi, garin dankalin turawa, da kayan lambu.

Mrs Bukhari
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: LAMBA TA ASHIRIN DA SHIDA
GAWURTATTU UKU
MRS BUKHARI

JOS:
Chapter 36 · 0% Book details