Sashe 30
Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
LAILA:
"Laila ki buɗe kunnanki da kyau kiji me Daddonki zata faɗa miki. Kuma kiyi haƙuri da dukkannin abunda zaki ji." Innata tana kaiwa nan saita fice. Ni kuma jikina har rawa yake yi tsabaragen kaɗuwa, dama a daren jiya da aka ɗaura auren Shehu banko iya runtsawaba. Yanzu na gane dalilin matan da suka kasa tawakkali dan mijinsu ya ƙara aure, suyi hauka. Zafi da ciwon kishi, iyayen gida ne kaɗai ka iya ɗanɗana harsu gane abunda nake nufi ( Su maman Khairat,Deezatu ai baza su gane me nake nufi ba. Maman Yaseer ce kaɗai za tai mun uziri)
"Laila" Daddo ta kirayi sunana da harshe rarrauna."
"Shehu yayi aure har ya wayi gari a ɗakin amaryarshi. Abunda zamu ɗauraki akai shine haƙuri da juriya. Mai haƙuri shi kan dafa dutse har yasha romanshi. Ni da gyatumarki kina gani babu abunda yake shiga tsakaninmu na husuma. A tsakanina da'ita girmamawace, dan sanda aka auroni, shekaruna goma ina cikin na sha ɗaya. Ita da mahaifinku suka taru suka raineni. Kinsan dama ko mu jima, ko mu daɗe Shehu dole zai ƙaro aure. Ballema da kika haifi Ɗahiru kinsan yanda ƙabilarmu ta malam bahaushe ta canfa yara irinsu Ɗahiru. Babban abunda zan daɗa miki dashi shine, ki rungumi yaronki karki hofantar dashi, dan babu mai kula miki dashi, saike. Ki dage ki ta mishi adda'a ko Allah zaisa rayuwarshi tayi albarka. Ba kowa Shehu ya aura ba face Asiyan Kande ƴar uwarki. Amman ki daure ki jure zama da'ita Ta Asibi tace in horeki karki kuskura ki lalata musu zumuncinsu." Hawaye ya gama wanke mun fuskata har ɗiga yake yi. Sai yanzu nake tuno irin kallon da Shehu ke jifan Asiya dashi, sau tari ina kama Shehu na jifan Asiya da murmushi. Kasancewar ƴar uwatace ban taɓa kawo komai a raina ba ashe Shehu aurenta yake son yayi. Naji zafi ainun dan kwanana biyu ina cikin ruɗu da damuwa. Saida malam yaita mun nasiha sannan na dangana. Yaya Nafi matar wanmu ita taita zagawa dani yawon arba'in. Munyi ziyare_ziyare sosai. Bayan mun dawo kuma na soma shirin komawa, duk da a cikin fargaba nake, dan bansan me zan tadda a gidan ba. Na shirya tsab, Goggo Laraba da Yaya Nazeefa da Anty Nafi sune sukai mun rakiya. Ina sa ƙafa a cikin gidan gabana ya yanke ya faɗi, su Iyami suka shiga jaye yaransu ƙananu. Su tsaya ma mu gaisa, sai daga nesa_nesa. A ɗakin Baba mai riga muka yada zango.
"Kune a gari Laraba, sannunku da zuwa"
"Yauwa sannunmu Mai riga, ga Laila mun dawo muku da'ita yadda kuka bamu haka muka dawo muku da'ita. Ya akaji da taro?" Baba mai riga ta yashe baki tace
"Taro ya watse lafiya. Sauran dangin mahaifin Shehun ma suna can ɗakin matar Malam basu tafi ba. Laila ya Ɗahirun?" Yaya Nazeefa tace.
"Me gidanki lafiya lau, yayi mul_mul dashi. Ni dai kaina a ƙasa har muka miƙe. Ɗaki_ɗaki na leƙa aka sake gaggaisawa. Sannan muka shigo ɗakina.
"Yanzu Laila ni inaga bari muyi miki kwalima, tunda sai gobe zamu juya, mu sake miki fasalin ɗakin. Saiki sake labulen da Inna tayi miki. Ni dai ina zaune sai tunani nake faman yi. Su kuma gadan_gadan suka shiga aiki. Sai bayan Isha suka game komai. Har zuwa lokacin Shehu bai leƙo ɗakin ba. Kuma ina jiyo muryarshi, yana kaɗa yara. Idanu na lumshe, a yanda naga rana haka naga dare. Sai jefin asuba na samu nannauyan bacci ya ɗebeni. Da sassafe su Yaya Nazeefa suka soma shirin tafiya. Goggo Laraba tace.
"Taso muje ɗakin Asiyan mu gani, tunda ita bata da kunya ta kasa yi miki sannu da zuwa" Idanu na gwalalo nace.
Goggo me yasa zamu je, ita da Shehun duk sun san mun dawo fa, amman ba wanda yazo ya duba mu." Sai tace.
"Ke dai ƴannan muje, ki daure ki cusa mata aniyarta." Haka suka sani gaba muka shiga, Asiya kamar babu wata dangantaka a tsakaninmu da'ita haka tayi mana. Goggo Laraba tayi mana nasiha, ni kuwa sai ƙarema Asiya kallo nake. Ashe banda komai ba. Wasa_wasa na zama bola a gidan Shehu, sai Shehu ya ishi Asiya yake zuwa ya nemi hakkinshi. Babu zancan rabon kwana sam. Ni kuwa haka na dinga kannewa inata jure duk wani abu dazai ɓullo. Ɗahiru kuwa na mayar da hankali kan renonshi. Tani da kishiyoyinta kullum a cikin faɗace_faɗace da gore_gore suke. Kawu Ɗahiru kuwa ya zama shahararren malamin da ake ji dashi, dan aikinshi tamkar yankan wuƙa haka yake. Kullum gidan a cikin baƙi mata yake, kullum sai an yanka kaji an soya anyi sadaka. Rayuwa taita tamaule damu, Asiya taita baza mulki a zuchiyar Shehu, dan ko fishi tayi dashi, ranar bashi ba sukuni sam. Ranar naɗin sarautar Shehu ta zagayo, amma ko labari banji da wuri ba, sai ana jibi za'ayi taron. Haka na auni alkama, da farar shinkafa, na kaima Sha'awa ƙawata, tai mun nakiya da alkaki, ko wanne fanteka ɗaya. Ranar naɗin sarautar naci ado cikin yadin banbalasta fari sol, nasha ƙunshi da kitso. Da safe bayan isowar su Yaya Nazeefa, saita raka ni naje har ɗakin Asiya na kaima Shehu tawa gudunmawar. Ganin haka sai yaji kunya, yana sanye cikin kayan saƙi, jikinshi cike da layu da guraye, Asiya taci ado da yadin tentalan, tana gefen hannun Shehu.
"Kiyi haƙuri Laila, Asiya zansa a naɗa a matsayin mai sauraron koken matan mafarauta, a matsayina na sarkin mafarauta, kinga ita ta'iya rubutu da karatu, ke ko ba ki iyaba. Naji ciwo, idanuna yai rau_rau, amman saina cije. Nace dashi.
Ai babu komai Shehu, duk dai abinda ka yanke yayi, kaine shugaba, Allah ya taya riƙo shine fatana." Yaya Nazeefa ta kamo hannuna muka fice. A taƙaice ƴar kallo na zama a filin naɗin sarautar Shehu. Munsha wasan mafarauta sosai ranar, anyi wasannin al'ada masu ban ƙawa. Da haka taron ya watse, Shehu ya zama sarki, Asiya shugabar mata. Har taro suke gudanarwa, duk ƙarshen wata. Dani da Asiya haka mu kaita hayayyafa. Yarana Huɗu cib, Ɗahiru, Karima, Dauda, Izzatu, Sai tulelen cikin nabiyar. Asiya kuma yaranta Uku namiji ɗaya mata biyu, sai ƙaramin cikin na huɗu. Faɗar wuyar da nasha a wannan shekarun, ba abu bane wanda zai rubutu, aimun afuwa.Amman kallo ɗaya kaimun kasan ina azabtuwa, na tsofe, na bushe, sai hidimar yara nake yi. Ɗahiru kuwa kullum yana ƙunshe a ɗaki, bana bari ya fita, daya fita yara suke tunkuɗeshi ya faɗi har sai yaji rauni, ko suita tuɓe mai wando suna ma halittarshi dariya. Kullum yana biye dani, ko kuma ya zauna a dokin ƙofarmu yaita kallon yara suna wasan ƴar gala_gala a tsakar gida, yaita dariya. Tausayinshi ya cika zuchiyata fam. Shi yasa gabaki ɗaya na maida hankalina zuwa kanshi. Sallar dare kuwa harya zame mun jiki. Babu da irin sharrin da Asiya bata bini ba, amma ina ganin falalar adda'a. Tunda na samu wannan cikin, Asiya ta murɗa kanbunta Shehu bai kuma tako ƙafafunshi da sunan shigowa ɗakin ba. Ga cikin yazo mun da wani irin laulayi, dan harma na gama fidda rai da rayuwar baki ɗaya. In Yara suka shiga ɗakin Asiya, sha Allahu da kuka suke fitowa, yaranta ƙananu harta koya musu, hantarar yayyensu suma.
Ina zaune ina wankin yara. Shehu ya shigo cikin shiga irinta sarakan dawa yace.
"Ke Laila, wancan yaron ya fito, ga mota za'a wuce dasu birni almajirci. Asiya, kema ki kawo naki, Yaya Iyami, yaran duk su fito. Ƙirji na dafe nace.
Sarki shayi ne a jikin yaronnan, a hakan za'a kaishi almajirci? Jijiyar bata warke ba, jiya da yasa wando wallahi ya fame ta har saida tayi jini. Sarki karka tagayyara mun yaro" Nan su Matar Malam su kai ca a kaina. Inaji ina gani, aka fita da Ɗahiru, yana ihun kiran sunana. Ai take na durƙushe na soma naƙudar dole. A kaina aka rufu, nan naita abu guda, wasa gaske har washe gari ban haihu ba. Saida suka ga na kusan macewa aka sani a keken shanu, zuwa Asibiti. Amma Shehu yaƙi zuwa fur, Iyami da matar malam ne suka tafi dani. Ban kuma sanin ina kaina yake ba. Saina farka naga babu ciki a jikina, ashe tiyata akayi mun.yara maza har huɗu aka ciro mun, amman ɗaya ana ciroshi, ko kuka bayyi ba ya rasu. Da Shehu na soma haɗa idanu, yayi zuru yana kallon kyautar da Allah ya bani. Maganar wannan magen ta faɗo mun da tace " Laila uwar maza" har bayan suna muna asibiti, ƴan uwana suna faman hidima dani. Dan tunda Shehu yasa kai ya fice a asibitin bai kuma zuwa ba. Ranar sunan matar Malam tazo nan take shaida mun. Yaran sunci suna. Salisu, Tasi'u Sadisu
Allah ya raya su da imani" Shine abunda nace kawai. Kwananmu tara a asibiti aka sallame mu. Mahaifina shi ya biya komai daya shafi kuɗi, yaimun goma sha tara na arziki, Yaya Nazeefa kuma ta bani ɗiyarta Mama dan su taimaka mun, ita da Karima ta wajena da renon Tawayoyina,tare dasu muka koma gida. Cikin tashin hankali da damuwa naita rainon Tawayoyina, bana samun tallafi da kulawar kowa. Gasu da kuka sosai. Bayan Shekara da tafiyar su Ɗahiru, sai gasu sun dawo ganin gida, a lokacin Tawayoyina har sun soma gudunsu ko'ina. Ɗahiru yayi murna da ganin ƙannenshi. Ya sake yaita wasa a cikinsu yana dariya. Nima raina fari sol da naga Ɗahiru a cikin walwala. Haka rayuwa taita tafiya. Shekaru suka shuɗe sosai, su Tawaye har sun girma suma an kaisu almajirci. Asiya ta hana gaba ta hana baya, duk wata kyautatawa ta hana Shehu yayi mana ni da yara. Su tawaye sun sha azaba sosai a wajan Asiya da yaranta. Kullum a cikin duka da kyara suke.
Ina tsugunne muna dukan shinkafa zamu cireta daga samfurarerta. Sai ga Malam ya shigo.
"Iyami ki kwashi Su Laila ku tafi ƙofar fada. Akwai baƙi da muka samu daga jam'iyyar matan arewa. Suna buƙatar a taro kan matan ƙauyen. Tun ɗazu ake ta faman yekuwa." Ni dai inata aikina, dan duk wani abun arziki ba'a sani a cikinshi, nima bana cusa kaina. Ɗahiru ne yazo zai kama mana aiki, sai naga jini a bayan rigarshi. Gabana ya yanke ras ya faɗi.
Wannan yaron kaje maza ka sake kayanka" Da sauri ya wuce, ni kuma na bishi da idanu gabana na faɗuwa. Asiya ce ta fito cikin gwalli tace da Iyami.
"Nifa na fito kuzo muje, Yaya Tani kumujenku mana, Laila kema zaki iya tawowa." Ni babu tunani a jikina sam, amman haka na ɗauraye jikina na yafa mayafi muka tafi, na bar su Karima da sauran aikin.