← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 40

Sashe 25

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Musina:
Rayuwa kenan, a kullum inna zauna, sai inta kallon rayuwa, da yanda lamarin duniya ke tafiya, lallai tsarki ya tabbata ga ubangijin kowa da komai. Yanzu yanda muke jin zafin mutuwar iyayenmu da duk suka rasu, suka kwanta dama, haka muma wata rana yaranmu zasu tsinci kansu cikin maraici. Su Baba Hauwa an kwanta dama, mahaifin Yawale ya jima shi kam da rasuwa. Baba Sahura ce kaɗai ta rage. Ita kanta cikin ciwo take sai an kwantar sai an tayar. Yara duk sun zama samari, matan an auradda wasu, daga cikin mazan ma wasu sunyi auren. Awaliyya ta wajena, yanzu malamar asibiti ce, ɓangaren ƴan haɗari. Tana aiki a babban asibitin dake jihar Bauchi. Haka kullum take zuwa ta dawo. Kulu kuwa karatunta iya sakandare ya tsaye, akayi mata aure, danta nuna mun auren ya fiye mata. Naso tayi karatu mai zurfi, amman bata bani haɗin kai ba. Tana aure a nan kusa damu. Kattume ma tayi aure, iyakarta itama sakandare, tana aure a can jama'are. Jamilu kuma manomine babba, dan Allah yasa albarka a hannunshi, duk abinda zai shuga, zai samu albarka mai yawa. Ƙasimu kuma, yana aiki a Azare, a wani kamfanin buga bulo. Mustapha kuma maginine, sai ƴar auta ta Zubaida. Itama da halama tana da burin yin zurfin karatu. Tana ajin farko a jami'ar A T B U nan Bauchi. Tare suke fita da Alawiyya. Sai dai wani sa'in Zubaidar tana zama a ɗakin ɗalibai, musamman in jarabawa ta matso."
Kumatu kuma Saminunta yayi aure, Yawale ya bashi fili a cikin gidan yana zaune da matarshi. Zakiya tayi aure a Kaduna, ta auri wani ɗan uwan Kumatun, hamshaƙin mai kuɗin gaske ne. Kamar dai yanda nake ji a bakin Kumatu da matan gidan kenan. Sauma'iyya kuma tayi auren amma yanzu zawarci take yi, auren ya ƙare. Muttaƙa kuma ya zama ɗan sara suka, sune ɓarayin kaji, da agwagin mutane. Su A'i duk sun aurar da yara. Sai ƴan tsirari da suke gabansu, amma ana shirin kawar dasu suma.

Ina zaune a tsakar gida ina yanka sabulu, Jamilu na ƙirgama wata wacce tazo sari a wajena. Ƙasimu yana gefen wajan ɗakina yana yi mun miyar kuɓewa bushashshiya, nayi tuwon tun kafin in zauna aikin yankan sabulun. Alawiyya da Zubaida kuma sun shiga cikin gari. Mustapha ne ya fito da wankin kayana a hannunshi. Jamilu na ganinshi da kayan ya tashi a guje ya nufi Mustapha, sai kace wani ƙaramin yaro.
"Wa ai wallahi baka isa ba. Gyaran ɗakin da kayi bai isheka ba, saika shigar mun aikina? Aini nake yin wankin duk sati inya taru." Mustapha na dariya yace.
"Amma naga kana taya Inna aikin sabulu, ga masu sari sunzo. Kaga ga wata ma ta shigo" Fur Jamilu yaƙi yarda saida ya fisge kayannan a hannun Mustapha ƙarfi da yaji.
Haihuwa mai rana. A rayuwar gidan Yawale da nayi sam babu daɗi. Amma gashi yau na haifi yara, sun share mun duk hawayena, suna bani dukkannin wata kulawar daya dace. Damuwata ɗaya ce, rashin waiwayarmu da Idi baiyi ba, sama da shekara ashirin da biyar, wannan itace kaɗai damuwata. In aka cire wannan, bani da wata damuwa da take damuna sam. Girgiza kai nayi nace.
Kai Mustapha tawo ka ƙirga mata, bar mishi aikinshi kaji. Ƙasimu sannu ɗan albarka"
Kumatu taja wani tsaki mai ƙarfi. Ni bansan ma ta fito ba, dan mu kaɗaine a tsakar gidan. Muttaƙa ne ya shigo a guje, ya bangaje Kumatu ta faɗi ƙasa warwars shi kuma ya shige ɗakinta."
"Wayyo hannuna, wayyo ƙafata" Da sauri na miƙe tsaye.
Kai Ƙasimu zo ka ɗaga Yadikkonku maza. Sannu Kumatu."
Da sauri Ƙasimu yaje ya ɗagata. Fadawan mai gari ne, suka shigo gidan da zabga_zabgar dorunanrsu.
"Muttaƙa muka biyo, kuma munga shigowarshi. Dan haka a fito mana dashi" Tsurewa Kumatu tayi. Ai su A'i iyayen gulma anajin haka sai gata ta fito tsulum.
"Bayin Allah ko me yayi haka, kuka biyoshi da waɗannan murtuka_murtukan dorunan? Kuma yana shigowa ya haure danga ya dire bayan layi" Cewar Kumatu kenan wacce take riƙe da hannunta da nake tsammanin zata iya samun tsagewar ƙashi tsabar buguwar data yi. Ni dai ina tsaye ina mamakin Kumatu yanda duk ta gurɓata ma yaranta kab rayuwarsu. Haka fadawannan suka tafi, bayan sun faɗama Kumatu, akuyar mai gari suka sace. Kuma duk inda Muttaƙa ya shiga a ƙauyan zasu nemo shi. Suka fita suka barta da borin kunya. Sai zage zage take yi, harda kuka, ga hannunta dake ta faman zugi.
"Wallahi ni nasan hannu akasa ma Muttaƙa amma ba yin kanshi bane. Allah ya toni asirin duk mai sa hannu akan lalacewar yaronnan. Baƙin ciki akeyi mishi, anga ya taso da ƙarfi." Tsaki naja, nayi zamana naci gaba da aikina. Yarana bayan duk sun gama mun aikina, sai kuma ko wannensu ya nufi wajan sana'arshi.
Da yamma ina zaune ina haɗa sabulu, Yawale ya shigo cikin gidan da leda cike da cefane. Ya miƙa ma Kumatu.
"Ki gyare kayan miyannan Kumatu, kiyi mana jar miya. Kazar wajan Sauma'iyya ki yanka mana ita asa a miyar. Zan bata kuɗin. Bakinane sam babu daɗi so nake inci wani ɗan abu mai galmi, kwana biyunnan bana jin daɗin jikina, kasala da na damuna, gashi mamana na gefen hannun dama ya soma damuna da ciwo fa." Yawale na kalla nace dashi.
Sannu da dawowa Malam "
"Yauwa Musina ya kasuwar Dai"
Alhamdulillah" Ina faɗin haka nayi shigewata cikin ɗaki. Tuwo na zuba, da miyar kuɓewa taji naman rago, gashi naman yayi laushi. Ina ci ina shima yarana albarka. Jamilu ne yayo Sallama ya shigo. Hannunshi riƙe da leda cike da lemon taba_taba. Yasan inason taba_taba sosai musamman manyan da suka yi jawur a bishiya.
"Uwo ga lemon taba_taba na sayo miki. Bari in ɓare miki. Zama yayi a gefena ya soma ɓare mun.
"Uwo waini ya batun maganar Auren Yaya Ƙasimu ne, ni ranar Alawiyya na bani labarin wai kinje gidansu yarinyar da zai auran. Kuma magana ta faɗa, har Kawu Jamilu yaje ankai sadaki"
Gaskiya ne. Iyayenta dai sunce a bari sai watan cika ciki, in Allah ya kaimu. To Kawunku sun shige gaba anyi komai, an biya sadaki, dan Babanku yace bazai sa hannunshi ba. Lokaci kawai muke jira. Inason in samu Babanku da batun inda shi Ƙasimun zai zauna. Ƙila ya taimaka ya yanka mishi guri a kusa da Saminu. Sai Zaidu ya gina mishi. Jamilu yace dani.
"Uwo Baba Kumatu bazata taɓa barin Baba yayi mana abun arziki ba. Ita fa so take yaranta ace su kaɗai suka mallaki dukiyar Baba, gado ma dan tasan dole a raba da mune, kinsan da bazata yadda a raba da ƴan ɗakinnan ba. Amman ga shawara Uwo. Wannan filin nawa na unguwar madaki, mai zai hana Yaya Ƙasimu ya gina, yayi zamanshi acan kamar zaifi ko? Kuma filin yana da girma, dani da Mustapha duk zai ishemu muyi gininmu acan. Kinga shikenan kema saimu maidaki can kiyi zamanki tare damu, kema ki samu farin ciki. Amma mai kike gani?" Shiru nayi ina nazari. Abunda Jamilu ya faɗa gaskiya ne. Kumatu ba zata taɓa bari Yawale ya yanka ma Ƙasimu fili ba. Alhamdulillah yarana kansu a haɗe yake, kuma Jamilu yana samun kuɗi sosai akan amfanin gonarshi da yake siyarwa. Banda hatsin daya cika mana rumbu dashi, banda wanda yake raba ma matan gida da maƙota. Yanzu haka yana da gonakai biyu daya siya, ɗaya yana noma shinkafa, ɗaya yana noman riɗi a ciki. Banda gonakai na haya da yake haya. Dan ƴan uwanshi suna taya shi noman, harda su Alawiyya duk suna taimakon ɗan uwan nasu.
Maganarka gaskiya ce. Banso suka san da wannan filin ba ma Jamilu. Amman kamawa tayi. Allah ya saka maka da alkhairi. Bari ya dawo sai in faɗa mishi, a samu a hankali a soma gini.
Ai kuwa hakan Akayi. Ko da Ƙasimu ya dawo, saina zaunar dashi na labarta mishi abunda muka tattauna da Jamilu. Duk sunji daɗi kuma sunyi na'am da shawararshi. Ba'a wani ɗauki lokaci ba Ƙasimu ya soma gininshi. Labari dai ya zagaye harya faɗa kunnen Yawale. Ranar afujajan ya shigo cikin gidan. Yana kwaɗa mun mugun kira. Saida gabana ya tsinke ya faɗi. Buzu_buzu ya shigo da uban gemu"
"Da gaske ne, Ƙasimu ne yake gini a unguwar madaki?" Murmusawa nayi nace."
E shine, Jamilu ne ya bashi filin ya gina iya inda zai zauna da iyalinshi" Ƙuta Yawale yayi yace.
"Duk girman filinnan na Jamilunne, ko iyakar inda yaba Ƙasimunne nashi? Kiyi magana mana, sai wani murmushin ɗaukar rai kike yi" Ai Kumatu na jin haka zuruf ta miƙe ta baro, ɓarzar dawar da take yi ta matso kusa da Yawale. Kallonsu nayi dukka nace.
Duka filin nashi ne, ai wannan ƙaramine ma daga cikin filayenshi, banda gonakai daya mallaka" Ba Kumatu ba ba, har Yawale saida ya kaɗu da abinda yaji nace, take ya soma kumfar baki.
"To baki isa ki raba mun kan yara ba wallahi. Duk ƙoƙarin da Kumatu ta dinga yi tun yaran na ƙananu dan ganin ta haɗe kansu, kinƙi yarda. Yanzu sabida kinason duniya ta zageni, wata na ya kama a ƙauyannan ace na kasa ba yarana fili suyi gini a gidana, saida suka je waje, shi yasa kika amince musu su fitan ko? Sabida munafukace ke ƴar iska, har yarona ya mallaki irin waɗannan uban kadarorin ace ni ubanshi bani da labari? Fili tabkeken gaske, wanda mai gari ne kaɗai yake da irinsu. Hawaye ya soma zubarwa. Kumatu ta cabke da cewa."
"Ka dena kuka Malam, Ai Musina bata ƙaunar zaman lafiya, shi yasa kullum cikin cusa ma baƙin ciki take. Yawale yace
"Dake da yaran naki duka, ina son ganinku a turakata bayan sallar isha" Wucewa yayi yana share hawayenshi. Girgiza kai kawai nayi na koma ɗaki abuna. Bayan sallar isha duk muka hallara a turakar Yawale, da yarana da yaran Kumatu.

[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: *_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
Chapter 25 · 0% Book details