Sashe 32
Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Sunana Hajiya Turai shugabar Jam'iyyar matan Arewa ta ƙaramar hukumar Bakori, tare dani akwai Hajiya Tabawa shugabar jam'iyar matan Arewa ta ƙaramar hukumar Faskari.
Waje yayi tsit, ni dai sai kallon matannan nake, ina jin inama zan iya zama ɗaya daga cikinsu, jibesu tsab_tsab dasu, kuma duk mata ne cikakku da suka san ƴancin kansu. Uwar gidan mai gari ta miƙe tace.
"Ina godiya da wannan karramawar da akayi mun. Sannan ina godiya sosai, kuma ina farin cikin shigowar wannan jam'iyyar matan Arewa cikin wannan gari namu, wani babban alkhairi ne ya shigo mana, Allah ya jiƙan Laila dogon yaro. Allah ya saka ma da (MARYAM ABACHA DA ALKHAIRI) ni a tunanina da nazari na, ina ganin babu wacce ta dace da wannan matsayin kamar Laila Uwar gidan sarkin Mafarauta, dan ta kasance jajirtacciya, mai haƙuri da rashin raki. A garinnan babu iriyar tsangwamar da bata shiga ba, amma sau ɗaya bata taɓa zuwa gaban mai gari ta durƙusa da sunan ƙorafi ba, haka muma da muke sauraron ƙararrakin talakawa, bamu taɓa cin karo da Laila ta kawo ƙarar kowa ba. Kuma matar Malam ta tabbatar mun da haƙuri da juriyar Laila. Sai dai bani da masaniya akan iya rubutu, da karatunta." Gabana ne ya yanke ya faɗi, wani tsoro yayi tsalle ya dira a ƙirjina, nan take sai nake jin kamar numfashina yana kakkatsewa tsabar farin cikine, ko tsabar kaɗuwa, na kasa banbancewa. Wannan baiwar Allahn ta bani damar miƙewa dan jama'a su ganni da kyau. Jikina har wani kakkarwa yake yi, idanu muka haɗa da Shehu wanda ya ɗaga hannu halamar yana da magana.
Mrs Bukhari ce
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: GAWURTATTU UKU
MRS BUKHARI
LAMBA TA ASHIRIN DA HUƊU.