← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 40

Sashe 18

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da farko zaki samu ruwa ki jiƙa costic soda ɗinki ya kwana. Saiki samu manki ki zuba a roba mai faɗi in kika zuba, saiki samo muciya ko bulugari, kina zuba ruwan costic soda kina juyawa a hankali, in kika gama zubawa sai kita tuƙawa a hankali a hankali har ya haɗe jikinshi. Saiki juye a mazubi, ki barshi ya kwana, saiki yayyanka dai_dai na siyarwa. Shikenan sabulunki ya kammala, kuma bugu da ƙari gashi da kumfa. Yanzu zamu yi muku wannan sabulu ido da ido ku koya." Muna zazzaune a tabarma, matannan su uku suka haɗa sabulunnan abun gwanin sha'awa. Duk abunda suka ce ni kuwa saina rubuta, danma ajin baya tafiya, muna yawan fita fitsari. A haka muka gama ajin yau.
Tafe_tafe dai haka rayuwa tai ta tafiya, har muka gama ajinmu na koyon sana'a. Alhamdulillah na gane komai na rubuta komai. Sun yaye mu, sun rarraba mana kemikal kyauta. Masu kuɗi sun kuma siye. Nima na siya, kuma sunce da mun shiga kasuwar gari, muka tambaya ɓangaren ƴan kemikal za'a nuna mana. Jikina yayi sauƙi sosai, fitsari saura kaɗan_kaɗan. Mako ɗaya na roƙi malam ya ƙaramun akan dana gama ganin likita sai in wuce. Maganin gargajiya malam ya sa aka dafa mini, na dinga sha shima. Cikin kwana uku da soma shan maganin fitsari ya dai_daita har inajin taruwarshi a marata, sai naje na tsugunna nayi nishi sannan ya zubo. Bani kaɗaiba duk wani masoyina nasan ya taya ni farin cikin samuwar lafiyata. ( Musamman maman khairat, maman Yaseer, ummu Inteesar, Deezatu, da Ɗambatta. )Ina fatan Allah ya bama waɗanda basu warke ba lafiya. Waɗanda kuma lafiyarsu ƙalau Allah ya ƙara musu lafiya da imani. Ranar da mako ya zagayo na koma asibiti, likita tayi farin ciki da samuwar lafiyata, ta ɗaurani bisa wasu shawarwari, har kyautar sutura tayi mun kala uku masu kyau da tsaɗa. Na dinga mata godiya. Ina fitowa na koma gida na soma tattare komatsaina. Har zuchiyata ta jagule na soma hawaye. Malam ya bada kuɗi da hatsi a bani. Suma su Inna suka ɗan haɗomun tsarabar mata. Ina kuka na fita, sai haƙuri suke bani, banza nayi dasu, dan da suna ƙaunata ba zasu ce in koma ma Yawale ba. Sati na uku a gida, ko sau ɗaya baizo ba. Babu wanda ya biyo sawuna a gidan, amma ansa in koma babu ko rakiya, ba dole ma Yawale da Kumatu suita mun wulaƙamci ba. Gani suke yi kamar bani da gata. Har aka isa Saleri ban fasa kuka ba, saida na iso ƙofar gida na share fuskata. Da sallama na shiga gidan.
Gabaki ɗaya matan gidan suka zuba mun idanu cike da mamakin dawowata. Su buɗe baki su amsan sallamata, abun ya gagaresu. Kumatu wani turus tayi ta dinga bina da idanu. A'i shugabar munafukai ce tayi magana.
"Musina kece tafe da yamma sakaliya haka, ashe zaki dawo? Murmushin tura haushi nayi nace.
Mai zai hana ni da gidan mijina, kuma uban ƴaƴana, ko an faɗa miki sakina Yawalen yayi? Nan na shige ɗakina dana ganshi a wangale,na bar Kumatu da cizon yatsa. Ganin ɗakina a buɗe nanma raina ya kuma ɓaci ainun. Kayana na dure na fito, sai kallon ƙafata da hannayena suke nasha ƙunshin saleteb wanda Inna Lami ta kusan raba dare tana jera mun. Gashi ya turu kamar jinin kare. Naje gidan aminiyata Ma'u ta yarfa mun kitso, ta kuma bani shawarwari masu tarin yawa, ta yanda zan kula da mutuncina in kame girmana. Ɗakin Baba Huwaila na soma shiga muka gaisa. Sannan na shiga ɗakin Baba Hauwa. Itama muka gaisa, anan take faɗa mun Yawale sunje aiki a gona da yaran gidan. Ina komawa ɓarayinmu, na soma firfito da kayan ɗakina ina kwalima. Saida na wanke ɗakin tas sannan na mayar da gadajen da kwabata da babu komai a cikinta. Na kunna turaren wuta, ko ina ya ɗauki ƙamshi. Sannan na fito na wuce sakaki. Kumatu da su A'i sai aikin kallona kawai suke ta faman yi. Ni dariya ma suka bani. Ina fitowa daga sakaki, na ɗaura alwala nayi shigewata ciki. Sai da daddare can na haɗa sabulu na, na juye a mazubi, na barshi a saman kwaba. Sannan nayi bacci. Ko ƙeyar Yawale ban gani ba. Washe gari da yamma na yayyanka sabulun na fito dashi wajan matan gida. Hmm a daren ranar kusan raba dare Yawale da Kumatu suka yi suna rikici.
Ni kuwa sabgar Yawale bana fatan kuma shiga. Sana'a kawai naba mahimmanci. Da sannu matan gidan suka gane na warke, sai kuma muka ci gaba da aikin girki tare kamar yadda akeyi da.
Rayuwa haka tai ta juyi dani, yau fari gobe ɓaki. In Idi yazo haka zan haɗa mai kayan abinci, in ɗauki kuɗi in bashi, sabida bana son yana yawon barace_barace. Ashe daya je malaminsu yake amsar kayan abincin, yasa manyan almajirai su lalubeshi ya karɓe kuɗin, kuma ya sashi a mari. Ranar da Idi ya faɗamun wannan maganar bacci ma kasa yi nayi. Haka dai rayuwar taita Tafiya. Mu kaita haife_haife ni da Kumatu, rayuwa kenan.wata rana wacce bazan taɓa mancewa ba. Ina zaune a tsakar gida, ina yanka Sabulu. Alawiyya tana gefe tana wankin ƙannenta, sauran mazan gidan kuma duk sun tafi almajirci, iyakar yaranmu mata ne kawai a gabanmu. Kwatsam sai gasu Idi sunzo ganin gida. Nayi farin ciki sosai dana ganshi, amma ya rame sosai, kuma idanunshi naga yayi jawur. A guje ƙannenshi suka suka je inda yake suna murna. Sauma'iyya ƴar gidan Kumatu ma sake wankin da suke yi da kumatu tayi, a zuro a guje. Kumatu ta ɗago cikin jaraba tace.
"Dan ubanki kina mace, kike gudu kamar wata jaka?" Murmusawa kawai nayi. Idi kuwa cikin fara'a ya tsugunna a gabana.
"Uwo barka da gidan, mun sameku lafiya?"
Lafiya lau wannan yaron, ya karatun?.
"Alhamdulillah, kafin ma in tawo saida na biya wajan Ƙasimu, da su Jamilu na dubosu, sunce in gaisheki. Juyawa yayi wajan Kumatu yace.
"Ina wuni Baba Kumatu?" A daƙile ta amsa mishi. Ana cikin haka, Saminu ɗan wajan Kumatu ya shigo da buhun kayanshi, makarantarsu ɗaya da Idi. Sai lokacin Kumatu ta soma washe baki. Baba Hauwa ce ta iso wajan.
"Ah mai gida takobin yaƙi kaine a tafe? Ɗan nema shine saida ka soma zuwa wajan uwarka tukunna ko?" Kai na sauke kawai. Idi yace.
"To ai dole inzo in nemi albarka kafin in je wajan tsohuwar matata ko? Dariya suka yi dukkansu.
"Meya same ka naga ka rame idanka yayi ja da yawa?" Ajjiyar zuchiya na sauke, dan tambayar da zanyi mishi kenan, Baba Hauwa ta iso wajan.
"Idanuna ne suke ciwo, har asibiti ma na kwanta, gidan da nake ɗan musu aikace_aikace su suka kaini asibiti. Amma da sauƙi, sai dai idanun ya samu matsala, in rana ta take bana gani sosai, amma ina shan magani, sunce wata mai zuwa in koma asibitin, in banji dama ba, zasu yanka mun tabarau." Hawayene ya subto mun. Babu shiri na miƙe na shige ciki. Leda Idi yaba Alawiyya ta tabami. Sannan ya miƙama Sauma'iyya nasu. Baba Hauwa kuma ta jashi suka tafi.
Bani na samu keɓewa dashi ba, sai bayan sallar isa ya shigo.
"Uwo saura shekara guda muyi sauka in sha Allah" murmushin din daɗi nayi nace.
"Amma idanun naka da sauƙi ko? Nayi imani malaminku ne ya kashe ma idanu, amma bani da yanda zanyi ne"
"Ai ko a asibitin ma likitoci sun faɗa Uwo. Amma babu komai, bayan wuya sai daɗi. Muna ta tattaunawa, ledar tsarabar daya bamu ya jawo. Atampace, da takalmi, da mayafi. Ya ware a gefe yace ga nawa. Sai atampa da man shafawa yace na Alawiyya da Kulu. Albarka na sanya mishi. Yai mun sallama ya fita.

Yawale:
Da sallama ya shiga ɗakin Kumatu, ya tadda Saminu a zaune.
"Au tare kuke ashe da wancan yaron Saminu"
Cikin kulawa Yawale yake magana da Saminu, harda tambayarshi yanayin birni, da kuma yanayin karatun. Can idanunshi suka sauka a kan Atampa da man shafawan da Idi ya ba Kumatu tsaraba."
"Wannan kayan fa Kumatu? Dama jira take.
"Hmm malam wai yaronnan Idi ne yayo mana tsaraba. Uwarshi kuwa nata leda guda, banda nasu Baba. Nifa Saminu yasha faɗa mun ana kama manyan kuɗi a jikinshi a makaranta. To Ta mai gari ma ta faɗa mun, kasan ɗanta Bala makarantarsu ɗaya. Ya tabbata dai Idi ɓarawo ne" Yawale ya dubeta da kyau yace
"Amma duk kina da wannan labarin kika kasa sanar dani, kina jira har sai ranar da yaronnan zaije yayo wata gagarumar satar da ƴan doka zasu zo su naɗeni ina zaman zamana ko?"
"Malam ka faɗa ace sabida ɗan kishiya ne" Ai bata gama magana ba, Yawale ya fice, sai ɓarayin su Baba. Yana shiga ya cukuma Idi, ya fito dashi tsakar gida, anan yaita tamaule dashi. Kowa ya fito, Su Jamilu, da Mudi suka tambayi Yawale me Idi yayi. Cikin kumfar Baki ya sanar musu.
"Sata yake yi a birni, har malaminsu na kama kuɗi masu gwaɓi a jikinshi." Suna jin haka kowa ya shiga salati, Yawale yaci gaba da jibgar Idi.

Musina:.
Kalmar sata da Yawale ya dangantata da ɗana yafi mun dukanshi da yake yi zafi. Zuchiyata sam taƙi nutsuwa, musamman da naji Yawale yana faɗin Idi yazo ya bar mishi gidanshi. Da gudu na isa shiyyarsu Baba. Amma ganin yanda Idi ya fita hayyacinshi ya ɗaga mun hankali, fiye da tashin hankalin da nake ciki kafin in iso. Idi ya dubeni yace.
"Uwo ni ba ɓarawo bane. Ki yarda dani.
Na yarda dakai, nasan cikinku babu wanda nayi mishi tarbiyyar da zai ɗauki abun wani." Marina Jamilu yayi har yana huci. Nan matan gidan suka hayayyaƙo mun, dole nayi shiru.
"Uwo ku dena kukan. Zan tafi, amman zan dawo in ɗaukeki a gidannan a lokacin da babu wanda ya'isa ya hanani fitar dake a cikin wannan ƙaddararren gidan da kike zaune dan sabida mu yaranki. Kuma zan kare mutuncin kaina" Inaji ina gani aka tusa ƙeyar Idi a gaba. Tun daga lokacin hawan jini ya kamani, dan na shiga damuwa mai tarin yawa. Ƙauye kowa ya ɗauka, dan Kumatu sai yaɗa abun take faman yi"

Bayan wasu shekaru.

MRS BUKHARI

*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*
Chapter 18 · 0% Book details