Sashe 13
Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saleri:
Laila.
A hankali na buɗe idanuna da Goggo Laraba na soma haɗa idanu, idanuna sai ruwa_ruwa suke yi.
"Alhamdulillah Daddo Laila ta farka. Sannu Laila kinji, yaya kike ji a jikin naki" Cikin ƙarfin hali da tawakkali nace.
Bana jin komai sai rashin ƙarfi" Daddo tace.
"Sannu ƴannan Allah ya ƙara sauƙi."
Yunwa nake ji Goggo."
Da sauri Goggo Laraba ta fita, bata jima ba ta dawo da tuwo mai zafi yana ta turiri. Yaji ta baɗa mun da man shanu. Jikina har yana rawa, duk yawan tuwon sai da na cinye shi tas. Saina soma jin sanyi_sanyi na shigata. Jaririna nake ta kallo a hannun Daddo tana bashi ruwa. Matar malam ce ta shigo.
"A abun yayi kyau. Sannu Laila, yaya jikin kuma, ta farka kenan?"
Da sauƙi matar Malam.
Zuchiyata sai tunano mun wannan magen dana gani take yi. Amma nasan jaririn dana haifa mayu basu shafe shi ba. Dan ɗan gidan mafarauta ne, a zauren shigowa zauren gidannan akwai kafin Mayu a sagale a jikin azara, kusa da inda tsetsewalu suke guje_gujensu. ( Irin ƴan ƙananun tsuntsayennan da suke karakaina a zaurukan ƙasar Hausa ada) Adda'a nayi akan Allah yai mun tsari da dukkan abunda zai zama sharri a gareni.
"Ungo Laila ɗan sa mishi nonon ya ɗan dinga zuƙa. A haka har ruwan zai kawo. Hanuna har rawa yake yi dana karɓeshi. Tausayi da ƙaunar jaririn sai ƙara burunƙasa yake a zuchiyata. Lumshe idanu nayi, hawaye suka surnano mun. Nonon na zura mishi a baki, carab ya soma tsotsa, a fakaice na dubeshi, kamanninshi ya fito sak da Shehu. Matar malam tace
"Ki shirya ayi wanka, duk da magriba ta kunno, amman baza kiji daɗin jikin naki ba." Fita tayi, bata jima ba ta dawo.
"Laila maza fito muje kar ruwan ya huce." Kwantar da yaron nayi, na yafa fallen zane na fita. Muna shiga sakaki matar malam ta tura mun wani kwaɓaɓɓen magani a gabana tace.
"Mayar da ɗan durus ɗinki" mayarwa nayi. Ruwannan da mugun zafi haka matar malam ta dinga yaɓamun tana zaneni da ganyen darbejiya. Ta dinga zuba mun ganyen darbejiyannan a tudun cikina. Jini kuwa ya dinga fita, ina jin daɗi, jikina sai warwarewa yake yi. Hannu matar malam ta saka ta kwakwule maganin data cusamun. Ta bani ƙatuwar butar ƙarfe cike da itatuwa tace in wanke gabana. Na dinga wankewa a hankali, ina gamawa matar Malam ta rufeni da zani. Gudu gudu na koma ɗaki. Gaushi ya gama ɗumame ɗakin sai naji ni sawai iska mai daɗi na busani. Tsakin magani matar Malam ta zuba a wuta tace.
"Maza tsugunna Laila yanzu ƙarin da akayi miki zai haɗe." Tsugunnawa nayi maganinnan yana shigata ina mugun jin zafi da raɗaɗi,jini sai ɗiga yake yi a cikin garwashin, saida na haɗa zufa sharab sannan matar Malam ta ɗagani, na samu na sake kaya nayi ƙunzugu. Bacci nannauya ne ya kwasheni.
Daddo:
"Laraba yarinyar nan fa da ganinta tana cikin damuwa mai yawa. Jiya da daddare uban ya korota tayo yaji. Wallahi haka muka rasa sukuni ni da Ta Asibi a cikin gidannan. Tunda akayi auren Laila bata taɓa zuwa ganin gida ba. Jiyan da zata fita sai naga tana ɗingishi, amman na ɗauka nauyin cikine. Sai naga abun kamar fa ba hakan bane Laraba. Kuma tunda muka zo gidannan babu wata facala data shigo ɗakinnan da sunan dubiya. Sai Iyami da matar Malam kawai suke suntiri. Shehun ma sai ciccika yake yi. Ni jikina bai bani ba Laraba." Goggo Laraba tace.
"Nima naga hakan Daddo, amma ni zan rutsata ta faɗi abunda ke damunta ko zata samu sassauci a zuchiyarta. Ni tausayi take bani. Wannan yaro data haifa nina tabbatar sanadinshi matsalolin gidan aure zasu matsa ma Laila lamba. Kinsan maza basu cika tawakkali ba."
Ɗahiru:
A tashar bodi aka sauke su, sai jan yaran yake, Tani kuwa ahankali take jan ƙafafunta, dan ji take uwa zata haife abunda ke cikintane yanzu tsabar wahala. A haka har suka iso gida, Ɗahiru sai zazzare idanu yake yi.
"Tani mu shiga can shiyyar su Yaya, ki daure sai rakin tsiya moi dalla." Ɗaga ƙafa ta shiga yi har zuwa shiyyar su Baba mai riga. Matar Malam ce ta soma ganinsu, fitowarta daga turakar malam kenan zata ɗebo mishi ruwa.
"Wa nake gani kamar Ɗahiru da Tani? Mai riga, mai riga, malam,Baban Yara ku fito ga Ɗahiru." Ba iyakar waɗanda Matar Malam ta ambaci sunansu bane kaɗai suka fito ba. Kusan rabin matan gidan sun fito, cikin al'ajabi da almara. Malam yace.
"Ɗahiru, Tani. Kune kuka dawo a cikin darennan?" Ɗahiru yayi dariya yace.
"Yaya ka manta sanda zamu bar garinnanma da daddare muka barshi, ta katanga ma bata ƙofa ba?" Ajjiyar zuchiya Malam ya sauke. Baban Yara yace"
"A tafiyarku baya haihuwa tayi ta tara tulin yara masu ƙiriniya sosai. Ɗahiru sai nake ganin kamar ka tabka babban kuskure da kayi tunanin waiwayar gida. Mai riga ki shiga da Tani da yara ɗaki. Tani wannan du yaranku ne? Ku da kuka tafi ku biyu, amma gashi kun dawo ku huɗu, da guxirin na biyar a ciki" Tani wacce take a galabaice tace.
"Ke dai Yaya Mai riga bari. Mun wahala a bariki sosai, duk da nasan dawowarmu tamkar wasa da rayukanmu ne." Matar malam da Baba mai riga suka shiga ciki da Tani da yaransu. Baban yara ya dubi Shehu yace.
"Kuje da Ɗahiru ɗakin zaure ku kwana tare Shehu." Ɗahiru yace.
"Au Shehu bai aure ba har yanzu? Naga ya zama babban mutun. Ina Lauwali ne?" Malam yayi dariya yace.
"Lauwali yana wajan tukuba yana gashi. Ga Iyami matarshi ita kaɗai nake tunanin ka sani a cikin surukan gidan. Lauwali yanzu ai da babban ɗanshi Jafaru suke shiga dawa farauta, kuma da gani zaifi ubanshi zamani. Shehu matarshi ce ta haihu, ƴan uwanta suna tare da'ita shi yasa ya koma ɗakin zaure." Ɗahiru yayi dariya. Nan surukan gidan suka shiga gaisheshi tare da wucewa ɗakin Mai riga dan gaishe da Tani. Shehu kuma suka wuce ciki da Ɗahiru.
"Zauna kawu bari insa Iyami ta kawo maka abinci da ruwa." Dariya Ɗahiru yayi yace.
"Shehu jarumin dawa, ka gagari kowa a dawa." Dariya Shehu yayi kawai ya fita.
Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.
Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻
07068606171
08104335144
08179523215
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._
*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*
*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_
*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_
*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_
_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_
1 500
2 700
3 1000
_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank
_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._
_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171
*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*
0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*
_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
MRS BUKHARI
MALLAKIN BADI'AT IBRAHIM
( MRS BUKHARI)
(GAWURTATTU UKU)2023
INA TAYAKI MURNAR ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWARKI. KIYI HAƘURI NAYI LATTI. ALLAH YA SAKE MA RAYUWA ALBARKA. KI DAƊE KIYI ƘARKO ( LAILA ALI OTHMAN) FARAR MACE ALKYABBAR MATA, SUKARI BAKIYI FARIN BANZA BA. 🤍🤍🤍💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*
*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*
_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
SAMFOTI
LAMBA TA GOMA