← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 40

Sashe 35

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MRS BUKHARI
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA ASHIRIN DA BIYAR

ƊANBO:

HINDU:
"Fatsima tasa aka sakeki kuma aka biki da mugun duka haka? Sakin har nawa ne, shegiya kike kuka zaki bada mata" Zainaba ta kalli Hindu tace.
"Saki uku tasa yai mun, wallahi Baba inason mijina nikam" Tsabaragen takaici Hindu rufe Zainaba da mugun duka tayi, tana dukanta tana kuka, itama kukan take yi. Daƙyar su matan gida suka ƙwaceta. Suna cikin haka Audu ya shigo jikinshi a mugun mace mus da takadda a hannunshi. Jagwab ya zauna yana zabgama Hindu wani irin mugun kallon tsana, Zainaba yabi da kallo, yaga bakinta yana zubar da jini. Hawayene suka soma sakkowa a kumatunshi. Bai yi magana ba, ya fice a ɗakin zuwa turakarshi. A canma jagwab ya zauna ya shiga zurfin tunani.
Haƙiƙa shi kanshi yasan yayi zalunci ga Shamsiyya da yaranta, ta yaya zai iya kare kanshi akan abinda yara sukai ƙararshi akai? Shi kanshi ya shiga kogin dana sani, mara madafa, dan yasan Shamsiyya ba zata taɓa mancewa da irin azabtar da'ita da yayi ba. Tunano baya ya soma yi, a lokacin da yake zuwa ƙofar gidansu taɗi, da irin musayar kalaman soyayya da suke yi a tsakaninsu. Abubbuwa iri_iri yaita tunanowa, Hindu da dai taga shirin yayi yawa, sai tabi Audu ɗakinshi, a kwance ta sameshi idanunshi jawur.
"Malam ince dai lafiya ko? Naga ka shigo jiki a mace baka ce mana komai ba, kuma kana ganin Zainaba mijin yayi mata makirin duka, ya rangaɗo mata saki har uku. Ni fa wallahi bazan yarda ba Malam. Dubanta yayi da kyau yace.
"Ai bazan daki ƴar mutane ni ince nawa yaran su sha ba. Gwargwadon yadda zan cutar da ƴar wasu, gwargwadon yanda za'a cutar da nawa yaran. Ta gode Allah ma, da har ta gane gidansu ma. Ki fita ki bani waje ina son hutawa, kuma ki shirya zaman kotu, ki sanar da Shazili ma, su Zaliha sun doka mu a kotu." Wata zabura tayi tasa hannu aka tace.
"Ni Hindu naga ta kaina, kishiya tara rana ɗaya, ta goma na ƙofar gida. Kotu fa kace, anya yarannan yaran sunna ne kuwa? Kai ɗin suka maka a kotu? Nan cikinta ya juya ba shiri ta tsure sai zawo, Audu dai baya iya cewa komai.
Anyi roƙon duniya akam Shamsiyya ta janye ƙarar amman su Shatu sunce basu amince ba. Hindu da Shazili suna cikin tashin hankali.
KOTU:
SHAMSIYYA:
Muna zaune a bakin kotun, muna tsumayar a gama shari'ar dake gaban tamu kafin mu shiga. Hindu da yaranta da ƴan uwanta, suna gefe guda. Nima muna gofe guda, da yara dasu Goggo Rakiya. Audu yana gefe guda shi da abokinshi, ya zabga tagumi. Yayi matuƙar rama, kamar bashi da lafiya ne ma, dan ina gani abokinshi ya zaunar dashi zaune. Saida aka ƙare shari'ar da akeyi sannan alƙalin ya nemi ganawa damu a ofishinshi.
"Barista Zaliha tayi mun bayanin komai, na zaɓi mu tattauna a ofishinane dan kar duniya ta zagi Audu. Amman Shamsiyya zanso ki bani labarin irin zaluncin da Audu yai miki, karki rage komai, hakkinku dana yaranki za'a kwato miki. Numfasawa nayi, na dubi Audu wanda yake mun kallon inji ƙanshi. Hindu da Shazali kuwa sai zazzare idanun tsoro suke yi, Shagari, kuwa yayi shiru sai faman jijjiga kai yake yi. Nan na soma zayyanema alƙali irin zaman da mukayi da Audu, da Hindu, da irin zaluncin da sukaimun. Ofishin ya ɗauki shiru, sai hawaye muke sharewa ni da yarana da ƴan uwana. Alƙalinnan na kalla nace.
Ni na yafe musu, ai musu sassauci, babu komai ai duniya ce. Shatu tace.
"Ina da ja ya mai shari'a. Mu munason a kwato mana hakkinmu a wajan mahaifinmu, na kasa kula damu da yayi" Zaliha tace.
"Gaskiya ne yallaɓai muna son a ƙwato mana hakkinmu" Idanu na lumshe, Audu kuwa gabaki ɗaya ya galabaita, sai runtse idanu yake yi. Alƙali ya gama rubuce rubucenshi ya dubi Audu yace.
"Me zaka ce Audu, kana da ja, ko ƙarin bayani a bisa bayanin da Shamsiyya tayi?" Murya na rawa yace.
"Bani da ja yallaɓai. Wallahi duk abinda ta faɗa nayi mata, da sa hannun wannan algungumar matar tawa, wacce take sani a keken ɓera, ta haifamun kangarurrun yaran da suka gagaremu daga ni, har ita. Tabbas bansan komai nasu Shatu da ƴan uwanta ba. Sai dai tsana da tsangwamarsu kaɗai na sani. Bani da bakin da zan roƙi gafararku ƴaƴana, amman ku gafarceni nayi kuskure." Hawaye yake sharewa, harda dafe ƙirji, da dukkan halama ciwo yake ji a zuchiyarshi. Hindu da Shazili suma sai haƙuri suke bayarwa. Alƙali ya umarci Audu da biyana duk wahalhalun da nayi akan ci da sha, da ilmantar mishi da yaranshi da nayi. Sai ai mishi afuwa, ita kuma Hindu tayi alƙawarin ba zata kuma ƙulla wani makircin ba. Shazili kuma akace zaiyi zaman gidan kaso na wata biyu, tare da cin tararshi na dubu talatin. Audu ya amince zai bani gonakanshi duk biyun daya gada. Tare da yin alƙawarin bazai kuma cuta mun ba. Haka dai alƙalinnan mai adalci yai mana sulhu a tsakaninmu. Muka dawo gida. Audu ya ɗebo duk takaddun kadarorinshi ya danƙama su Zaliha. Suka sa hannu suka amsa, sannan suka ɗaukeni daga gidan.
Bamu sake waiwayar ƙauyannan ba, har sai da sha'anin bukukuwansu Shatu ya taso, ni kuma nace dole sai dai ayi bikinnan a gidan mahaifinsu. Shine muka dawo gidan, munzo mun tadda Audu cikin jinya, wujiga_wujiga, duk ya rame ya ƙanjame, sai an tayar sai an ƙwantar. Ina hawaye na dubi Hindu nace.
"Tun yaushe yake fama da wannan ciwon Hindu?" Cikin kuka Hindu tace.
"Watanshi shida cur a kwance, Usman ya koma wajanki a birni babu jimawa ciwon ya kwantar dashi, dama a tsaitsaye yake ta fama da ciwon, tun lokacin da wannan abun ya faru yake fama, kuma barinki gidan ya kuma ɗaga hankalinshi sosai. Wallahi bashi kaɗaiba Shamsiyya ni kaina gidan da ƙauyan baya mun daɗi. Tunda jama'ar ƙauyannan suka ganoni, shikenan fita wannan ta gagareni. Ku yafeni Shatu na tuba. Hawaye na share, na dubi Mariya ƴar gidan Hindu wacce take gidan aure.
Mariya ganin gida kikazo yine, na ganki da yara?" Hindu tace.
"Ummm inji mai ciwon baki. Mijinta ne ya rasu, takaba take yi. Bata gama takabar ba, dangin mijin suka raba gado, aka tasheta a gidan. Tuminin takabarta kawai suka bata, hakkin yaranta na hannun wan mahaifin nasu. Duk haka muke zaune, ga Zainaba Hannatu ta samu tayi aure da ƙyar, wallahi wuya take ci a gidan Auren. Duka kuwa wane Audu. Ga mijii ba lafiya, yara mazan kuma. Shagari ta ƴaƴanshi kawai yake yi, wallahi hatsin da zamu saka a bakinmu gagararmu yake yi. Matarshi ta gama asirceshi, sai abinda tace yake yi. Ƙiri_ƙiri take hanashi kulawa damu. Shazali kuma ba sana'a yake yi ba. Gashi da iyali. Shi kuma Muttaƙa ya jijjiga wata sata a birni, shi da abokanshi, yanzu haka maganar nan da nake miki yana gidan gyaran hali a birni. Wai saiya shekara ashirin za'a sakoshi." Kuka suke yi dukkansu, suna roƙon gafarar ƴan uwan nasu. Ajjiyar zuchiya na sauke.
Allah ya kyauta, yanzu shi Audu an kaishi asibiti ne?" A kunyace Hindu tace.
"Ina wanne asibiti Shamsiyya, ana maganar abincin da za'aci kina maganar asibiti. Ruwan kokkone a cikinmu dukkanmu. Hankalina ya tashi, lallai Allah, Allah ne. Shatu da ƴan uwanta suka kinkimi Audu zuwa motar da Shatu ta sai mun. Suka wuce asibiti. Ni da su Hindu kuma muka hau keken shanu, xuwa Bakura. Gado aka ba Audu, munje mun samu har an ɗaura mishi ruwa. Kwananshi bakwai ya soma murmurewa, harya kuma roƙon gafararmu. Takaddun kadarorinshi na maido mishi. Da ƙyar ya karɓa. Sati biyu Audu yayi yana jinya, kafin aka sallamemu, muka dawo gida, da goma sha tara na arziki. Saida Audu ya nutsu na sanar dashi zancen biki. Aikuwa gadan_gadan Audu ya shiga shirin biki. Gonarshi ya siyar, ya bani nera dubu saba'in kuɗin kayan ɗakin su Shatu. Anyi biki amare sun tare a gidajensu. Suna zaune lafiya, sai ƴan matsalolin rayuwa da ba'a rasasu, in dai da rayuwa. Tsufa yaci gaba da saukar mana, yaranmu suka ci gaba da hayayyafa, suna kulawa damu. Audu yaga ranar ƴaƴa matan daya wulaƙantani sabida haihuwarsu. Shagari kuma saida matarshi ta tatikeshi tas, sannan ta nemi saki, dole ya saketa, rayuwa ta tagayyarashi, a sakamakon bijirema iyaye da yayi. Hindu kullum cikin istingifari take, burinta ta kyautata mun. Su Zainaba da Mariya, sunyi aure, suma dai wuyar suke ci. Wata ranar asabar, aka wayi gari da rasuwata."

Audu:
Ya jijjiga da mutuwar Shamsiyya, yayi kuka har saida ya kwanta ciwon da shima saida aka kusan rasashi. Su Shatu ba'a maganar tashin hankalin da suka shiga ma. Haka suka dage suka gina masallaci da sunan ladan ya dinga isa kabarin mahaifiyarsu, masallaci lafiyayye suka gina, mai kyau. Audu yana zuwa kai ziyara kabarin Shamsiyya akai akai. Rayuwa kenan. Haƙiƙa wannan labarin akwai ɗumbun darasi mai tarin yawa. Shamsiyya taci ribar aure, tunda ta samu yaran da suke mata adda'a ba dare ba rana. Ta samu mijin da yake raba dare yana roƙa mata rahamar mahaliccinta, yana yi yana kuka. Haƙuri yayi a rayuwa, Allah ya datar damu. Inaima mabiya wannan labarin, da iyalan malama Shamsiyya ta'aziyyar mahaifiyarsu Allah ya kafarta mata. Anan na kawo ƙarshen labarinsu Shamsiyya.

Bari mu leka Saleri, gidansu Musina kuma:

MRS BUKHARI

[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: *_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
Chapter 35 · 0% Book details