← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 40

Sashe 40

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Musina
Wajajen magriba Idi ya shigo da kayan shayi niƙi niƙi, ga gashashshiyar kaza, ga figaggiya gyararriyar kaza cikin leda mai zane. Kayan shayi da gashashshiyar kazar ya dure a gabanmu
Cikin ladabi ya gaisheni. Ƙannenshi suka gaisheshi.
"Uwo ga kaza na siyo muku. Farfesu kikeso ko a miya kike son a saka miki?" Sai kallon Idi kawai nake yi. Na rasa me zance mishi tsabar daɗi.
Allah yaima albarka, kaima Allah yasa yaran daka haifa su ma haka. Nagode_nagode. Kaimun duk yanda kake so. Alawiyya karɓi ki gyara."
"A'a Uwo wannan ladan nawa ne, ni kaɗai zanyi. Ƙasimu, zo muje madafi. Tawo da ledar kayan shayinnan, in haɗa muku. Zubaida ke kuma zoki karɓi faranti ki baje muku gashasshiyar kasar" Miƙewa suka yi dukkansu suka bi bayanshi. Kwallar data taru a idanuna na sharce. Tare sukaita hidima dani. Idi bai huta ba, har saida yaga halamar bacci nake ji.
Washe gari da farfesun kaza da biredi mai laushi, muka karya. Nan ya samu a mota ya dinga zagaye damu. Atampopi ya siya mana masu tsadar gaske. Ya kaimu wajan tela mace ta gwadamu dukkanmu. Ni dai sai hawaye kawai nake zubarwa. Mun dawo mun samu Hadiza da yara sun dawo, harda Yayar Hadizan. Nayi farin cikin ganin jikokina ainun. Suma da dukkan halamu sunyi murna. Abunda ya kashe mun jiki shine irin rashin tarbar dana samu a wajan Hadiza.

"Hadiza zo mana" Idi ya jata gefe, na ga dai yana nuna mata ɗakunan da ya mayar mata da kayanta. Hannun jikokina naja muka shige ciki.

Hadiza:
"Me kake nufi, kana son kace nan ɗakunan a ciki zan zauna, ita mahaifiyarka ka bata wancan ? Amman Idris kamar bakai mun adalci ba" Ranshi ya kai ƙololuwar ɓaci sosai, dannewa yayi yace.
"Tafi ki cancanta da ɗakinne, nan gidan ɗanta ne, ke kuma nan gidan mijinkine, zan iya sallamarki, ita kuma sai dai ta sallameni. Ki nutsu Hadiza ina girmamaki sabida alkhairin iyayenki gareni." Yawu ta haɗiye, idanunta fal hawaye, tace.
"Yaya Halima aurenta ya mutu, zata zauna damu anan"
"Bazan hanata zama ba, ga ɗakin su Mamana saita dinga kwana dasu"
"A cikin yara zata kwanta fa kace?"
"Bata son kwantawa a cikin yaran ta kaso auren nata? Ki shiga ciki ku kuma gaisawa da Uwo, ita kuma kin barta tsaye, ta shiga ɗakin su Mamana mana. A wajan ya barta, ya wuce ciki. Halima ta iso da sauri.
"Wai waɗannan bataliyar ƙauyawan daga wacce shiyya suka zone? Meye naga kina shirin kuka?" Hannunta Hadiza taja zuwa ɗakinta. A bakin gado suka zauna.
"Wai mahaifiyarshi da ƙannenshi ya kwaso suka dawo gidannan da zama kab ɗinsu. Sannan dan wulaƙanci ya fito mun da kayana daga ɗakina ya dawo dani wannan ɗakin. Halima tace.
"Ki rufama kanki asiri ki rungumi aurenki, kinga dai wuyar da nake sha. Nabi Baban Fatima, na bishi ba wani canji, yaƙi ya dawo dani. Daga ƙarshe har yayi aurenshi, yana morewa da matarshi. Ni bazanma zauna ba ace ni na zigaki. Kinga tafiyata" Kayanta ta ɗauka ta fita. Hadiza ta raushe da kukan takaici, ko abinci ta kasa ci. Idi bai shiga daƙinta ba sai wajajen sha ɗayan dare. Tana zaune dirshen ya shigo. Baiko kalletaba, ya rage kayan dake jikinshi, ya hayo gadon, yana kallonta ƙur, yanayinta yake karanta.
"Me yasa kika ƙi zuwa ɗakin Uwo, kinzo kin ƙunshe kanki a ɗaki?" Baki ta taɓe tace.
"Wai kar in takura muku ne" murmushin cusa haushi yayi mata yace.
"Kuma hakane, dan muna tattauna abinda zai amfanemu a gaba ne." Juya baya yayi abunshi, dan zuchiyarshi ma tafasa take:.

Musina:
Fitowa nayi tsakar gida da buta zan ɗauro alwala, danni ban saba da makewayi a ɗaki ba, gani nake yi ma ƙazantace zallah. Abunda kunnuwana suka jiyo sun girgiza duniyata baki ɗaya. Take hawaye suka soma shatata a kumatuna. Hadiza ce ke magana da kuka"
"Allah yana gani, ni bazan iya zama da suruka ba, sannan bazan iya zama da danginka ba. Idris kar in rufeka, gara kaji gaskiya. Bazan iya zama dasu ba." Kuka ta kuma raushewa dashi. Muryarshi a daƙile kamar kuka yake haɗiyewa yace.
"Sune rayuwata, duk fafutukar rayuwa da kika ga inayi, dan su samu farin ciki nayi shi. Uwata ta fiye mun kowa da komai, tayi wahala damu, ta kasance tamkar kendir, ta ƙona kanta, danta haska mu. Babu wata mace da zan iya zama da'ita alhalin tana gudun mahaifiyata. Dan haka na sakeki saki ɗaya"
Idanu na runtse, inajin kalmar sakin na kaɗa ƙararrarawa a kunnuwana. Ihun Hadiza ne ya dawo dani kan doka da oda.
"Ni ka saka Idris, ka mance da duk alkhairin da iyayena sukai ma a rayuwa?"
"Baya nufin zasu fi iyayena daraja a wajena. Iyaye dabanne Hadiza, zan zauna in kula da uwata da dangina, dan nine gatansu." Da ƙyar naja ƙafata zuwa ƙofar ɗakinsu. Kai nasa na shiga. A tsaye dukkansu na same su"

MRS BUKHARI
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: GAWURTATTU UKU
MRS BUKHARI
LAMBA TA TALATIN
ƘARSHE.

"Likita mahaifimu ne malam Yawale, wanda aka kwantar a babban ɗakin maza. To yaune labarin rashin lafiyar tashi ta riskemu. Kuma na tambayi ƙanina kan ko akwai wani bayani da kayi musu. Yace A'a.
Likitannan ya ɗago yace.
"E hakane banyi musu bayanin komai ba, domun sai yau bincikenmu ya kammala. Mahaifinku yana ɗauke da cutar sankarar mama ne, na maza. Duk da dai ba'a cika samun maza da cutar sankarar mama ba. Mutane da dama basu san maza na kamuwa da cutar sankarar mama ba.
Ba a san takaimaiman abin da ke sa maza ke kamuwa da sankarar mama ba, amma dai haɗarin kamuwa da ita yana ƙaruwa ne sabida.

1 ƙwayoyin halitta da tarihin iyali, ko dangi, ciki har da gadon gurɓatattun ƙwayoyin halitta, rukunin BRCA1 KO BRCA2

2 Yanayin da zai sa a samu ƙaruwar sinadarin oestrogen a cikin jiki, ciki har da teɓa da lalurar hanta.

3 Idan an taɓa yin amfani da makamashi wajan ɗaukar hoton ɓangaren ƙirjin mut ( radiothephy)

Babu tabbas kan ko za'a iya ɗaukar wasu matakai na rage kasadar kamuwa da cutar, sai dai wata ƙila ɗaukar waɗannan matakin zai iya taimakawa:

1 Cin abinci mai gina jiki.
2 motsa jiki idan mutum yana da teɓa
3 kauracewa shan barasa da yawa.

Babbar hanyar magance sankarar mama shine gashi, ko ƙona ta da na'ura, ko yin tiyata, ko kuma cire ƙwayoyin halittar da ke haddasa ta. Mahaifinku yana kan matakin da sai an yanke mishi mamanshi." Iyaye_iyayene ba'a fishi dasu. Take su Idi hankalinsu ya tashi. Kuma suka bama likita umarnin aima mahaifin nasu tiyata. Cikin kwana biyu akayi ma Yawale tiyata aka yanke mishi mamanshi ɗaya. Ya jima ainun yana jinya.

Musina:
Ko da Yawale ya samu kanshi yaga kafatanin yaranshi, kewaye dashi, sai ya samu sassauci, daga raɗaɗin da yake ji. Gafararmu ya kuma nema, kuma duk muka yafe mishi. Harma Kumatu taci albarkacina nasa Yawale ya maidata ɗakinta. A jakata na bama Kumatu sadaki. Yawale ya warke, har mun mayar dashi gida. Bamu dawo ba, saida aka mayar da auren Kumatu da Yawale. Su A'i sai nan nan suke ta faman yi damu. Na zame musu wata abun sha'awa. Kullum cikin kaya mai tsada nake, ɗan kunne kuwa, zinare nake sawa a kunnena. Yaran gidan maza da mata kab sunyi Aure. Sauma'iyya muka ɗauka, mukaima kowa sallama, muka nufi Jos. Na jefa Sauma'iyya a UMMAHAT ni kuma na tafi jami'atul madina na haɗa digirina, na dawo a matsayin malama. Duk da tsufa ya kamani, amman da ƙarfina sosai. Yara kuwa sai hayayyafa suke ta faman yi, gida ya cika fam. Yawale suna ƙauye shi da Kumatu, Sauma'iyya tayi Aure abunta. Su Yawale sai dai su kawo mana ziyara. Yawale yayi_yayi in koma ɗakina, ni kuma naƙi fur, dan a yanzu nafi ƙarfinshi. Dangina kuwa ba ƙaramin taimaka musu yara ke yi ba. Gidanmu baya rabo da baƙin ƙauye. Su Kawu Jamilu da Mudi da anji dugu_dugu sai su shigo birni su huta, haka su A'i ma. Kulu, da Kattume kuma, sun kama sana'a sunayi, Yayunsu ko da yaushe a cikin ƙara musu jari suke, sun zama masu kuɗin ƙauye sosai. Dan kattume shanu ta ɗaure sama da goma, gata da ƙatuwar gonar shinkafa. Ita kuma Kulu ɗan ƙaramin kamfani sabulu ta buɗe, take horar da mata, sana'a, kuma tana yin na siyarwa, tana samun alkhairi sosai. Allah ya ƙarama rayuwa albarka. Anan labarina ni Musina yazo ƙarshe. Ina godiya ga masoyan wannan labari."

Alhamdulillah anan wannan littafin yazo ƙarshe. Ki bayyana mun ra'ayinki game da wannan littafin
Sannan wanne gidane yafi burgeki. A cikin mazan wannene dama_dama? Matan fa wacce tafi shan wahala? Wanne maki zaki ba littafin 🤣🤣

Ina godiya da ƙaunarku gareni ina alfahari da masoyana. Naga saƙwannin ku, naga kiranku. Naji daɗin addu'o'inku, Allah ya bani nafiya. Sai kun kuma jina tafe da wani jijjigegen labarin mai tarin darasi, da ilimin zaman rayuwa. NAGODE
Chapter 40 · 0% Book details