← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 40

Sashe 37

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Musina, musina!! Wata mata ce take kiran ƴarta da babbar murya"
"Na'am Mama, yanzu zamu gama, Alawiyya nake jira. Ƙasimu yaƙi ya canja rigarshi mama" Musina duk ita kaɗai tayi wannan maganar, mahaifiyarta Hadiza ta shigo ɗakin tace.
"Kun fiye nawa in dai zaku fita, ga kuɗin kitsonku ku biyu, wannan hamsin ɗin kuɗin askin Ƙasimu ne. Ki kula dasu Musina, kuyi maza ku dawo, kunga gidan babu abunda muka yi." Tana cikin maganane mahaifinsu Musina ya fito daga uwar ɗaki, cikin shirin zuwa aiki.
"Abban Musina yau da wuri zaka fita haka?" Kallon yaranshi yayi, ya musu murmushi, duk suka zube suka gaisheshi cike da ladabi. Da fara'a ya amsa, tare da jin lafiyarsu ɗaya bayan ɗaya. Saida yaga fitarsu ya dubi Hadiza yace.
"Ba kasuwa zani ba, yau shago sai dai Aminu ya buɗe, Bauchi nake son in gangara, Amman bazan kwana ba a yau zan dawo. Shiru tayi tana dubanshi, sannan tace.
"To Allah ya tsare, buhun shinkafarmu ya ƙare. Wake da garin tuwo ya rage mana kawai. Sai maganar gudunmawar da zan yi ma Fatima na biki, yanzu yarannan da sun dawo kitso, zamu tafi lalle, gobe kuma in muka tafi gida, sai bayan biki zamu dawo. Ajjiyar zuchiya ya sauke yace
"Sau nawa zan faɗa miki ne Hadiza a dena bari sai abinci yayi ƙaranƙab za'a faɗamunne? Wallahi bana jin daɗin hakan. Zan sa Aminu ya kawo buhu ɗaya a shago, ya kawo. Gudummawar da zakiyi dubu ashirin ta isheki?"
"Abban Musina da wai dubu hamsin nake so, sabida kaga nice babba a gidan."
"To inna dawo zan baki, zan bada buhun shinkafa ki kaima su malam a ƙara a gara, Aminun zai kawo miki dubu hamsin ɗin kawai, ni na tafi" Da adda'a ta bishi harya fice. Motarshi ya hau, ya kama hanyar Bauchi. Cikin awa ɗaya da rabi ya shiga Bauchi. Azare ya nufa, daga nan ya nufi Saleri. A gefen ƙofar gida ya ajjiye motar tashi, ya fito ya buɗe bayan motar, tsaraba ce ta kayan marmari yayo, da shaddajin maza, da takalman maza. Saminu yana zaune a ƙofar gida a cikin abokai. Zabura yayi da ganin Idi ya fito a cikin mota, yayi wani mugun fari, yana sanye cikin kayan kamala,
"Yaya Idi kaine ka dawo, ko dai gizo kake yi mini? Murmushi Idi yayi yace.
"Nine Saminu, kira abokanka su shiga da kayannan ciki." Da sauri ya jiya, Idi kuma ya girgiza kanshi, yana tuno sanda mahaifinshi a ingizoshi dai_dai inda yake, yayi mishi jina_jina. Ya tafi ya bar mahaifiyarshi a cikin zulumin rayuwa yake yi ko mutuwa. Harsu Saminu suka kammala shiga da kayan yana tsaye.
"Yaya Idi mun gama shigarwa" Murmusawa yayi kawai, ya nufi cikin gidan bakinshi ɗauke da sallama. Da Kulu ya soma cin karo, hannunta riƙe da kwanukan wanke wanke. Ihu tayi ta watsar da kwanukan.
"Uwo kizo ga Yaya Idi ya dawo uwo"

Musina

Kamar a mafarki nake jiyo wannan kiran, da sauri muka taso dukkanmu muka fito. Kumatu da su Sauma'iyya ma a guje suka fito. Mudi, Jamilu duk sunyo waje, su A'i uwar gulma harta iso gaban Idi. Muna haɗa idanu na fashe da kukan jin daɗi. Shima hawayen naga yana zubarwa. Kumatu kuma jikinta ne ya shiga ƙyarma. Su Zubaida da Alawiyya sun zagayeshi, shi kuma ya riƙe hannayensu.
"Idi kaine yau a tafe, maraba lale" Inji Mudi kenan. Tsugunnawa yayi ya dinga gaishe da iyayen nashi ɗaya bayan ɗaya. Kumatu a daburce ta amsa mishi gaisuwarshi. Ƙasimu ne ya shigo a guje, dan da dukkan halama labarin dawowar Wanshi ta isar mishi. Juna suka rungume, suna ta dariyar farin cikin ganin juna, juyawa nayi na koma ɗaki. Su Kulu ne suka shigo da Idi ɗaki. Kafin kace me, abinci har daga maƙwabta akaita kawowa, gida ya cika fam, Idi ya kasa samun keɓewa damu. Jamilu ne ya jashi suka tafi masallaci dan gabatar da sallar la'asar. Basu shigo gidan ba, sai wajajen yamma sakaliya.
"Uwo ki shirya kayanki tsab, inason mu wuce da yammannan ne" Dubanshi nayi nace.
Ɗannan daga zuwanka, bazaka bari gobe muje Azare ba, suma su ganka ba? Sannan bamu zauna munyi hira ba ma" Murmushi yayi mun.
"Hakane Uwo da yake na ɗokanta inga na ɗaukeki a gidannan ne, ina da gida a birni na siya. Ƙasimu yace.
"Aure fa Yaya?" nima tambayar da nake son yi mishi kenan.
"Nayi Aure harda yarana uku. UWO, ƘASIMU, ALAWIYYA sai mahaifiyarsu Hadiza. Mahaifinta shi ya zamemun uban gida, bayan korata da Baba yayi. Babban shagon hatsi ne dashi, a ƙaramar kasuwar ƴan tifa, ana kiran shagon da suna shagon ɗan Aljanna. To ganin gaskiya da amanar dana riƙe mishi ne, yasa ya bani auren ƴarshi Hadiza, nima a hankali saina buɗe shagon saida hatsin a kasuwar. A cikin wannan sana'ar na samu rufin asiri, na sai gida, ina tuƙa ƴar motata. Uwo su sunyi Aure ne?" Kulu ce ta shiga bashi labarin abubbuwan da sukaita faruwa bayan tafiyarshi, da halin da suke ciki a yanzu hakanma. Kuka ya dinga yi kamar ƙaramin yaro.
"Uwo kiyi haƙuri nayi jinkirin zuwa, wallahi duk neman da nake yi, sabida ku nake yi, shiyasa banzo da wuri ba, amman komai yazo ƙarshe, gabaki ɗayanku daku zan tafi, su Kulu kaɗai zan bari anan tunda aure suke yi. Jamilu naji daɗin yanda kuka kula da Uwo kuka share hawayenta. Amman tunda nine babba, ni zanfi so dukkanku, in tafi daku birni. In yaso in damina tazo, saimu ɗungumo muzo muyi noma mu koma. Ni dama hatsi nake sayarwa, kaima Jamilu haka. Sai mu sake buɗe wani shagon a kasuwa, kai da Mustapha ku dinga zama, ni kuma da Ƙasimu saimu zauna a nawa shagon. Alawiyyata kuma, zan nema mata gurbin aiki a babban asibitin juth, ita Zubaida kuma saita koma jami'ar Jos. Jamilu yace.
"Shikenan Yaya ni hakan yayi mun wallahi sosai, kuma ina da hatsi a rumbu mai yawan gaske, sai a kira akori kura ta kwashe tas ku tafi dashi, amman bazan biku ba tukunna, saina girbe amfanin gonana, sai in biyo sawunku. Ƙasimu yace.
"Yaya shawararka tayi kyau, gara mu tafi kawai, zanje inyi sallama da yarinyar da zan Aura, dan inna tafi, sai lokacin bikin zan dawo, ana ɗaura Auren, sai in ajjiyeta in koma. Sai a lokacin nayi magana.
"Kana da wajan da zaka ajjiyemu mu duka ne, ba zamu takurama mai ɗakinka ba kuma? Kai kuma Ƙasimu ban yadda kayi aure, ka ajjiye matarka aƙauye ba, sai dai ka tawo da'ita" Idi yace.
"Uwo kenan, takurawa kuma? Ina da ɗakin da zan ajjiyeku, babu damuwa in sha Allah, sannan su Ƙasimu akwai shago a ƙofar gida, sai su dinga kwana a shagon, zansa a gina musu makewayi a cikin shagon, tunda yana da girma. Uwo ai na isa da gidan nawa, kune kuma gatana." Albarka na dinga sa mishi, ina share hawayena. A haka Yawale ya buɗe labule ya same mu, shigowa yayi, su Jamilu da Mudi suka biyo bayanshi. A bakin gadon bono suka zazzauna. Idi ya matsa kusansu, ya sake gaishe da su Mudi, sannan ya gaishe da Yawale.
"Idi kaine a gari, ya gida ya iyalai?" Inji Yawale kenan.
"Lafiya lau Baba, iyalai suna gida."
"Ai da kazo mana dasu, mun gansu, sunga danginka suma ko?" Girgiza kai Idi yayi yace.
"Da yake naso komawa yaune shiyasa." Jamilu ya washe baki yace.
"Komawa a yau daga zuwanka, sai kace muna korarka?"
"Kawu aina jima da zama korarre, kowa da mahaifinshi yake alfahari, amma ni da mahaifiyata nake alfahari. Har abada bazan iya mance azabtarmun da Uwo da Baba yayi ba." Kai ya girgiza, ya jawo ledar tsaraba ya bisu da shaddoji, yadi goma_goma da takalma.
"Inason zuwa gobe zamu tafi, zan tafi da mahaifiyata kamar yadda nayi alƙawari, ƴan uwana ma zan tafi dasu, dan bazan iya tafiya in barsu a cikin ƙauyannan ba. Amman Jamilu zai tsaya saiya gama girbe amfanin gona tukunna. Kawu Jamilu, Kawu Mudi, muna neman alfarma dani da ƴan uwana Baba ya saki Uwo ta samu salama, musam mun fita hakkinshi bata tafi da aurenshi ba. Tun ina yaro nasan Uwo bata zuwa turaka, ma'ana ba'a rabon kwana da'ita. Ƙannena an samesu ne a bisa ƙaddara suma. Munga abubbuwa kala_kala. Lokaci da yoyyon fitsari ya kama Uwo a sakamakon goduwar naƙudar haihuwar Ƙasimu, a lokacin Baba ya dace ya kula da Uwo, amman a lokacin ne yayo Aure ya tare da amaryarshi. Wuya babu irin wacce bata ci ba. Kuma kuna gani, babu wanda ya taimaka mata, ko da, da tarbiyyar yarane. Dan haka ya saketa kawai." Ni kaina sakin nake nema dan na gaji da Auren, nafison inje in nutsu a wajan yarana, in mutu a ƙarƙashin yarana.

MRS BUKHARI

[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: *_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
Chapter 37 · 0% Book details