← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 40

Sashe 5

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

LAMBA TA HUƊU
"Shamsiyya kece kika fige kika dawo haka, uwa wacce ake gutsuran namanki?" Baba Shatu tace.
"Haba Rakiya, mai makon ki tausheta kuma, sai kike ƙoƙarin ingizata inda bai dace ba." A zafafe tace.
"Amman Shatu kina gani Audu ya ɗakko shirin nakasa mana yarinya? Dubi yanda jini ya taru a idanunta fa, ga tsohon ciki a jikinta, ina ganin rashin tausayin ai kamar yayi yawa ko?. Ya kamata a tsawata mishi, kawar da kai da muke yi, baya nufin bamu damu da Shamsiyya ba, muna yin hakanne dan siya mata mutunci da kima a idanun surukanta, da facalolinta." Buɗar bakin Baba Sahura kishiyar Baba Shatu tace.
"To kema kinsan ba zamu kasa tsawatar mishi ba, albasace ba tai halin ruwa ba, kinsan yaranmu na yau, ganinmu suke yi mu iyayensu mata kamar ba abakin komai ba, to yaro tun yana cinyarka za'aita zaginka, ana wulaƙantaka a gabanshi, sai kiga sun taso basa bamu daraja. Amma ai kamar yadda mahaifiyarta tayi haƙuri da dukan mahaifinta, itama ya kamata tayi koyi da mahaifiyarta ko?" Naji ciwon maganar Baba Sahura sosai, haka hawaye yaita sintiri a kuncina. Hannun Goggo Rakiya naja muka wuce ɗaki, dan ta kasa haƙuri sai zazzagama Baba Sahura jaraba take yi, ni kuma ina gudun abunda zai jawo mun abun faɗe a wannan ƙauye namu. Muna shiga na fashe da kuka, nan Goggo Rakiya ta shiga lallashina.
"Goggo Rakiya dama ashe haka auren yake, ashe haka maza suke, shine ake tururuwar yin aure, ashe babu komai a cikin aure, sai ƙunci da tashin hankali? Tun muna yara muke ganin mahaifiyarmu na kuka, wata rana muna jiyo yanda mahaifinmu ke zaneta tamkar jakar daya ɗauro ma kaya, taƙi tafiya. Yau gashi nima na faɗa irin taskun da mahaifiyata take ciki. Kuma nasan a haka zanta zaman haƙuri, har ranar da Allah zai kawo mun ɗauki." Goggo Rakiya tace.
"Da zan fasa miki irin haƙurin da Ta Annabi tayi a zaman aurenta ko da zaki kwashi abubbuwa da dama Shamsiyya. Mahaifiyarki bata taɓa gudowa gida da sunan yaji ba, kuma bata taɓa kawo ƙarar Babanku ba. Sai ranar da muka gani da idanuwanmu, a lokacin ta haifeki da ɗanyen jego a jikinta, ranar sunanki da safe. A jikin ƙarfen gado mahaifinki ya ɗaure Ta Annabi, ya riƙa tabka mata dorina tana ihu. Suna cikin wannan halin muka shigo muka same su, maƙwanta sun shigo kawo mata ɗauki. A ranar maƙwabtanta suka labarta mana irin ayar da mahaifinki yake gasa mata a hannu. Karki manta a lokacin akwai yayyenki maza biyu a gabansu. Yau gashi ankai wani matsayi da matakin da Ta Annabi itace hasken cikin gidan mahaifinki, tayi haƙurine ba dan komai ba, sai dan ku data haifa dan bata ko sha'awar tsallakewa ta barku." Tsabar tashin hankali da kaɗuwa take naƙuda ta kamani. Kafin Magriba ta rufa, na santalo yarinyata mace. Babu irin zagi da ɗiban albarkan da Audu baiyi mun ba, akan haifar mace dana kuma yi.
Ranar suna yarinya taci suna Tahira. Ashe a ranar aka ɗaura auren Audu, ni ina ɗaki bansan wainar da ake toyawa ba.
Zaman doya da manja muke yi tsakanina da Amaryar Audu Hindu. Audu ya tare a ɗakin amarya, anata ɗonan romon Amarci, ni kuma ina daga gefe ina kula da yarana.
Gorantama Audu aka soma yi a gidan dambe, har anayi mishi kirari da ragon namiji. Ranar kuwa nasha zagi a wajan Audu. Hindu tace.
"Ka sha kuruminka goga na Hindu, ga cikin magaji nan a jikina. Nice zan haifa maka magaji da yardar Allah. Tun daga wannan rana, Audu ya ƙara ƙaimi wajan kulawa da Hindu, har zuwa lokacin data sintilo ɗanta kyakkyawa namiji. Ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Audu. Muttaƙa, ana kiranshi da Baban gida. Sai da Hindu ta Haifi yaronta na biyu, Audu ya dawo ɗakina kafin Hindu ta gama biki, dan rabon kwanan da yake yi mana na rashin tsoron Allah ne. Zai iya kwana bakwai a ɗakin Hindu kafin ya dawo ɗakina, wani lokaci daya kwana ɗaya zai koma ɗakin Hindu, a hakan na kuma haifan Basira, harda ƙaramin ciki a jikina yanzu haka.. Ashe dawowa ɗakina da Audu yayi hakan ya ƙona ran Hindu ainun. Har ɗakina ta shigo ta dinga tsiwa akan Audu, tana yi mishi ɗiban albarka. Daya fusata ya shiga jibgarta kamar anyi mishi wahayi. Baki na taɓe, ai miji madoki baya dena duka, har sai ranar da tsufa ya rufan mishi.
"Allah ya isana, shege mara mutunci, tsinanne azzalumi. Inji Hindu wacce bakinta yaƙi rufuwa. Duka har tsakar gida. Baba Shatu, da Baba Sahura suka tawo a guje, suka riƙe Hindu wacce take ta kutuntumawa Audu zagi, bakinta duk ya fashe yana zubar jini.
"Shege ɗan gidan taƙi zama."
Wani irin naushi Audu ya kai mata, Baba Shatu ta tare Hindu, ai kuwa Audu ya sauke mata naushi a bakinta. Ji kake gib. Take bakin Baba Shatu ya fashe, yawu da jini, da haƙora biyu suka zubo. A take ta hangure ( suma).

Mrs Bukhari ce.

Ai mun dai afuwa, yau lahadi oga na gida. Masu ƙorafin sun rikice kuma. Ya kamata ku gane wani ɓangaren labarin na taɓa. Dan labarin mata iyayen giji, bai ta'anlaƙa a kan tauraruwa ɗaya ba. Muna da taurari da yawa, kuma zamu shiga gidajensu da garinsu, mu taɓo rayuwarsu. Allah yasa kun fahimta?

Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_

*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_

*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_

_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_

1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._

_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*

_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
(GAWURTATTU UKU)

*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*

SAMFOTI

LAMBA TA BIYAR

Saleri:
Ƙarƙashin ƙaramar hukumar Azare, jihar Bauchin Najeriya.

Saleri ƙauyene ƙayayau, daga Azare sai an wuce rugage biyar kafin a iso Saleri. Kab garin Saleri, basu da katangar ƙasa, sai dangar kara. Gidajen ƙauyen a jere suke babu fasali, dan in ka shiga gida ɗaya, a cikinshi zaka iya ɓullawa gidaje sama da goma. Suna da makarantar boko, da malamai biyu, malamin lissafi, da malamin turanci. Wannan makarantar ada ana karatu a ciki, shima daga lokacin rani kawai, da zaran damina tayi, yara suna gona. Amma yanzu ba'a karatu a wannan makarantar, wani mahaukaci ne yake kwana a ciki. Babu asibiti, har sai sun hau Bodi ya fita dasu zuwa Azare tukunna. Babu wutar lantarki, rijiya ɗaya ce a garin jol, duk jama,ar Saleri a wannan rijiya suke ɗiban ruwa, sai rafi da suke zuwa wanki, dabbobinsu ma a rafin suke shan ruwa. basu da injina, Mata ke surfe hatsi su dake ya zama gari, sai su sarrafashi, in buski zasu yi kuma, a dutsin niƙa na hannu suke zuba hatsin su ɓarje shi. Suna noma ka'in da na in. Mata da yara in damina tayi, tare duk ake zuwa ayi noma. Mace zata iya hayan gona, ita da yaranta maza da mata su nome gonar. Mai garin Saleri wanda ya rasu yana da kambun baka. Da yaga saurayi ya taso da gaye, da jarumta, zaiyi tofin Allah ya tsine akan yaron. Da sannu sannu yaron zai kwanta jinyar da saita zama silar ajalinsa. Amma yanzu Allah yayi ma Mai garinnan rasuwa, har an naɗa wani.
Chapter 5 · 0% Book details