← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 40

Sashe 15

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_

_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_

1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._

_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*

_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
(GAWURTATTU UKU)

Lamba ta goma sha ɗaya

ƊANBO:
"Ka kashe uwar taka Audu, sakamakon baƙar zuchiyarka. Bala da kai dashi ku kamata a kaita ɗakinta. A kirawo mai magani kuma". Audu sai Huci kawai yake yi, suna shiga da Baba Shatu ya fito, bai bari an yayyafa mata ruwa ta farfaɗoba ma. Gadan_gadan ya nufo Hindu wacce take zaune a inda aka barta. Ya shiga gibgarta kamar Allah ya aikoshi. Ni kuwa wucewa ta nayi ɗakin Baba Shatu.
Gabaki ɗaya halittarta ta sauya, fuskarta ta kumbura. Da ƙyar mai magani ya buɗe bakin Baba, tana buɗewa wasu haƙora biyu suka sake zubowa. Kurkura mata magani akayi, nan ma haƙora biyu suka kuma biyo ruwan maganin, ya bata wasu saiwu yace a dafa mata."
"Shamsiyya karɓi kije ki dafo mata." Karɓa nayi na fice. Dai_dai da fitowar Hindu da goyon jaririnta, tana jaye da Shagari ta fice tana kutuntumawa Audu ashariya manya_manya irinna cikakkun sokotawa. Baki na kwaɓe danni Hindu tayi mun dai_dai data nuna ma Audu iyakarshi, kuma bakinta yaƙi mutuwa dole shine ya haƙura ya barta. Na kuma ji daɗi daya dakata ta gane duk irin son da Audu yake yi mata, zai iya mata hukunci irin wanda yake yi mini, ko babu komai na tabbatar, dole rawar kanta ta sauka, wasu abubbuwan zata sauke su.
Amma kash a daren aka dawo da Hindu, iyayenta kuma sukaita cin mutunci kafin su tafi, suna goyon bayanta, ashariya buhu _buhu haka su kaita zazzagarwa a tsakar gidannan, ashe ko wanne tsuntsu kukan gidansu yake yi. A daren a ɗakin Hindu Audu ya kwana, ni kuma suka barni da cizon yatsa.
Washe gari, Yaya Bebi tazo ta dinga zagin Audu, babbar yarsu ce ita, taji labarin duk abinda ya afku, har Hindu bata bari ba saida ta zage. Amma Hindu saida tayi ma Yaya Bebi rashin kunya. Kuma itace babba a gidan, har iyaye mata basu cika tsallake maganar da Bebi ta zartar ba. Baba Sahura tace.
"Amman Ƴannan baki da mutunci baki data ido. Yayar mijin naki kike sa'in sa da'ita sabida ɗibar albarka, duk ɗiban albarkar da iyayenki suka zo su kai mana a gidannan bai isheki ba ko?"
Murmushi kawai nayi, dana tuno yanda suka dinga haba_haba da Hindu sanda tazo, musamman da suka ga ta haifi maza har biyu. Sai gashi rana guda suna Allah tur da ɗabi'un Hindu, dana iyayenta. Yarana na kaɗa muka shiga ɗaki. Haka Yaya Bebi ta tafi anata bata haƙuri a bisa fitsarar da Hindu tayi mata. Baba kuma haka ta dinga jinyar naushin da Audu yayi mata. Ya tare kacokam a ɗakin Hindu, baya raba kwana dani, baya bani kuɗin cefane, daga ƙarshe ma Hindu ta zuga shi yace kar kin kuma ɗibar mai abinci a rumbu, ina dafawa muna almubazzarancinshi. Da kuka na isa ɓayarin su Baba Shatu, na same su ita da Baba Sahura suna taɓa hira.
"A Shamsiyya lafiya ya da kuka haka meke faruwa?"
Baba Shatu, Audu ne yace kar in kuma ɗibar mishi abinci a rumbu in dafa, wai almusazzaranci muke yi mishi da abincin nashi, kuma wallahi ni ban taɓa dafa abinci na dafa yayi yawa harna zuba ma tumaki ba, Hindu ce ke dafa abinci da yawa ta barshi ya ɓaci ta zuba ma awaki. Ni na gaji ya sallameni kawai cin kashin yayi yawa" hawayene suka ci gaba da zurubtu a kumatuna. Baba Sahura ta sauke ajjiyar zuchiya tace.
"Tashi kije zamu kirawoshi mu mishi magana, ki dena kukan ƴannan, maganar ke kin gaji kuma fitsarace da rashin mutumci" Da kukan na kuma fitowa. Hindu tana tsakar gida tana daka ma Audu dawo tana waƙe_waƙen habaici. Ina kuka nazo na wuce matan gidan. Ina jiyo Shewar da Hindu ta saka. Shirya su Shatu nayi tsab nasa ta kama hannun ƙannenta nace suje gidanmu, da daddare Ƙanina ya dawo dasu." Hakan kuwa akayi, tafe_tafe har sati guda bata sauya zane ba. Ina tsaye yinwa na shirin kada ni, su Shatu kuwa suna gidanmu. Kwalla na buɗe na zaro joji da yadin banbalasta asalin mai maiƙo da nauyi. Mahaifina ne yayi mun a lokacin aure na, ya siya mun dan in ɗinka in samu na fita taron mata. Goya Tahira nayi, na jefa kayan a cikin goyon na rufu da mayafi na fita. Kai tsaye gidan Inna dillaliya na shiga na bata wannan kaya ta siye. Ta kuwa siya da daraja sosai. Gida na dawo na je ƙofar ɗakin Hindu nayi sallama, Hindu ta amsa ciki_ciki tare da bani izinin shiga." Audu yana kwance babu riga, Hindu tana dama mishi dawo.
"Lafiya meya kawoki ba dai akan abinci bane ko? Almubazzara sabida baki san daɗin dukiya ba shine kike dafa abinci jingim ki barshi ya lalace ki bama awaki ko, dan na rufa miki asiri shine kika je kinaso ki shiga tsakanina da mahaifana. Ta Allah ba taki ba Shamsiyya." Murmushin takaici nayi, zuchiyata sai gashewa take yi, nace.
Inason ka bani izini inje gidan Goggo Rakiya ne dan Allah"
"Kiji daga yau har gaban abada, duk inda kika ji kina son zuwa, na lamunce miki, ai matar so irin su Hindu su ake yima kulle jar fata ba irinku ba. Fitarmun daga ɗaki" Hindu ta kalleni taimun gwalo. Miƙewa nayi na wuce can hayi gidan Goggo Rakiya. Ina shiga na ɓalle da kuka ga yunwa na shirin halakani. Zaunar dani Goggo Rakiya tayi, ta bani ɗunamen tuwo da ruwa mai sanyi, saida naci na ƙoshi, sai naji na samu sassauci yunwa masifa ce. Goggo Rakiya tace.
"Shamsiyya ni shawarar da zan baki shine ki soma sana'a. Zan ara miki jari, akwai wata tinkiyata mai ciki, zan siyar in dunƙuli kuɗin in baki, ki ja jari. Kina ganina babu ƙauyen da bana kutsawa aci kasuwa dani. Kuma kinga irin cinikin ƙuli da man ƙuli da nake yi ai? Ƙauye_ƙauye nake fita nemo gyaɗa fa ba'a bori da sanyin jiki. Musamman ma da yaranki suka kasance mata, kinsan dai Audu bazai ma yaranki kayan ɗaki ba ko? Ƙarshenta a ɗebesu zuwa birni a turbutsasu a gidan aiki. Ni kaina yarana biyu saida suka je su kai aikatau na shekara guda _guda da rabi, saida suka taro kuɗin kayan ɗaki kafin aka aurad dasu. Na baya_bayannan kuwa da sana'ata tayi ƙarfi ai kinga ni na aurad da abuna. Saifa kin tashi tsaye, kishiyarki irin mugayen makiran matannanne, amma da sannu zata girbe koma mai ta shuka. Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Goggo Rakiya bama sai kin sai da tunkiya ba, na ɗan saida suturuna kinga kuɗin, sana'ar da zan soma ce ban sani ba. Shine nazo kiyi mun ido, tunda babu ƙauyen da baki sani ba"
"Kinyi kyan kai, kawo kuɗin in adana miki, gobe asubar fari tayi miki a gidannan, dan gobe kasuwar ƙauyuka da yawa suna ci. Sai muje ki zazzaga ki sari abinda yayi miki. Amman ina zuwa" fita tayi ta nufi rumbu, ta haɗomun kayan abinci sosai, ta ɗakko muttala biyar ta bani, harda karar girki saida ta ɗaure mun. Godiya nayi sosai na nufi hanyar gida. Ina dawowa ban jima ba su Shatu suka shigo, suma da ƙunshin garin dawa da Inna ta ƙunso musu, harda kuka, daddawa, manda. Uwa mai daɗi kenan, Allah sarki, ni ina tausaya mata, ita tana tausaya mun, Allah kai mana mafita.
Washe gari asubar fari kuwa, na kama hanya, su Shatu kuma nace musu in haske yayi ta tattare ƙannenta su tafi gidanmu. Ina isa gidan Goggo Rakiya, a daddafe muka karya kumallo, nan muka ɗauki hanya. Da yake ban sababa nasha wuya sosai, a ƙauye na uku ne na yanke shawarar kayan koli zan sara kawai, tunda ko ledar yin ƙunzugun yara wuya take yi mana sosai, har sai mun dangana da Bakura tukunna.
Goggo Rakiya, na samu sana'a, kayan koli zan sara, musamman ledar ƙunzugun yara, da tawul ɗin ƙunzugun, sai in ɗan haɗa da ƴan kunnen yara da manya, da turaren tsinke, na rambo, da 999. Goggo Rakiya tace.
"Kin kuwa yi dabara kab ƙauyen babu wata mace da take siyar da kayan koli, sai tsaffi masu saida farin kwalli, da kuratandun kwalli. Maza zo muje in haɗaki da Ya gana, kin ganta can, sai muji yaya abun yake, tunda shi kasuwanci in daka aka shigeshi ana wahala, zo muje.
Wajan Yagana Goggo Rakiya ta kaini, taimun bayanin yadda koli take, kuma na gamsu da sa'ar koli. Anan na sassari abunda nasan babu a ƙauyenmu. Sai yamma lis muka nufi hanyar gida, da tarin tulin buhunhunan gyaɗa na Goggo Rakiya cikin bodi tab. Sai dab magriba na shiga gidan, sai wani gani_gani matan gidan keyi mini. Wucewa nayi ɗaki na ajjiye kayan sari na, sannan na fito nayo walwala na koma na rama sallolin da ake bina. Sannan na ɗauki ledar na nufi ɓarayin su Baba Shatu. Na nuna musu, suka sa mun albarka, sannan na koma ɗakina, dan a ƙoshe nake mun sha dawo a kasuwa. Sai da aka sallaci Isha Mamuda ƙanina ya rako su Shatu, kwanciya mu kayi dukkanmu. Da yake na gaji baccin nayi shi mai daɗi cike da mafarkai masu daɗi.

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*
Chapter 15 · 0% Book details