← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 40

Sashe 28

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Laila:
Da idanu nabi Shehu ina karantar yanayinshi kawai.
"Laila tunda babu gaisuwa ina wuni" murmushi nayi mishi, na miƙa mishi Ɗahiru, yasa hannu ya karɓeshi yana kallonshi, take sai fuskarshi ta sauya, daga fara'a zuwa akasin hakan.
Ina Wuni Shehu, kazo lafiya?"
"Lafiya lau Laila. Kuma na fito jeji lafiyar Allah, harma an zaɓeni a matsayin wanda za'a bama kujerar sarkin mafarauta, har an saka rana. Sai dai ina fargabar abunda kaje kazo, sabida wannan yaron naki, zai iya kawo mun cikas a mulkina. Hakanne yasa zan ƙara aure Laila, harma an saka bikin namu, saura kwana goma cib." Banyi mamakin auren da Shehu yace zauyi ba, maganganunshi sunfi bani mamaki gaya. Auren mace sama da ɗaya haka addininmu yazo dashi, muddin in miji zai iya adalci a tsakani. Malam bahaushe yana girmama lamarin ƙarin aure sosai, musamman ga mu ƴan ƙauye, dan ɗan ƙauye iyakar jin daɗinshi ya ƙare a kwanciyar aure da mace ne, shi yasa suke girmama dare. Balle Shehu da yafi ƙarfina, dan nayi imani Shehu yafi ƙarfin mace biyu ma. Amma aurennan babu makawa zaiyi ne danya mayar dani bora, an gama canfani cewar ni mai farar ƙafa ce.
Allah ya sanya alkairi. Na taya ka murnar cin nasarar zama zakin mafarauta. Aure kuma Allah ya bamu zaman lafiya. Ina neman alfarma Shehu."
Jin ban ɗaga hankalina ba yasa Shehu ya sassauto.
"Ina jinki Laila" Nisawa nayi cikin ɗacin rai da ƙunan zuchiya nace.
Saura kwana goma muyi arba'in ina son ka ƙara mun kwana goma akai, sabida zanyi ziyare_ziyaren dangi na. Har can Dutsin ma nake son zuwa wajan Baba Kande." Kai ya sosa yace.
"Babu komai, zaki iya ƙara kwana goma akai ma, baki da matsala. Karɓeshi ki kwantar dashi, ni zan koma." Hawayen da nake dannewa ya zubo mun, ganin yanda yake nuna halin ko in kula akan Ɗahiru. Nasan ni da Ɗahiru cikin garari zamu yi rayuwa a hannun Shehu, ga aure zaiyi sabida ya samu kwanciyar hankali a wajan matar da zai aura. A tunaninshi ma na gama tashi a aiki, tunda ya gama buɗani, ya nakasa mun ƙafata, tawa ta ƙare ko? Hmm maza mutanen mu ( Allah ya gafartama Aisha Ɗan kano) Kallona yayi yace.
"Hmm Laila kenan, ashe ba zaki godemun ba dana zaɓi in ƙara aure ba tare dana sakeki ba? Kinsan irin iftila'in dazai shafeni a sanadiyyar wannan abun da kika haifa kuwa, baki da labarin yanzu haka a gida, amma daina sayen kayan siyarwan da su Baba suke sayarwa, sabida baza'a iya aiko yara ba, shine har kina da idanun kuka dan zan ƙara aure, me yasa mata baku da adalcine ku, baza ku tausaya ma maza ba?" A al'adance laifine babba in ɗago in kalli Shehu ma a yayin da yake cikin fishi, in kuwa na mayar mishi da martani, tamkar na aikata wani zunubine mai girma. Dole na haɗiye maganganun da Shehu ya dinga yaɓa mini, a wajen ya fita ya barni, Ɗahiru na rungume a hannuna. Ina jiyo Shehu na gaisawa da Malam daya shigo yanzu.

Shehu:
"A Shehu kaine a tafe da rana haka?" Cewar malam. Shehu cikin girma da ladabi ya gaishe da malam, yake kuma labarta mishi batun zaiyi aure nan da kwana goma. Su Daddo suna tsakar gidan suna jiyo su. Malam yace.
"Naji labarin a wajan Buba, dan jiya na shiga Dutsin ma ɗin naje cin kasuwa. Kuma ya labarta mun komai. Fatanmu yarannan Allah ya basu zaman lafiya a tsakaninsu kawai. Ina taya ka murna Sarkin mafarauta" Dariya da Shehu da malam suka saka, yayi musu sallama ya fita.

Ta Asibi:
"Malam ni na kasa gane wannan zarwancen da kuke yi da Shehu fa" Murmushi Malam yayi, tare da nufosu. A gefensu ya samu waje yaima kanshi mazauni.
"Auren da Shehu Zaiyi ba kowa zai Aura ba, sai Asiya ƴar Kande ƙanwarki Ta Asibi. Malam Buba mahaifin Asiyan ya shaida mun, wai sunfi shekara guda suna nema. Shehun ya auri Laila da kaɗan suka soma nema. Abunda Allah ya nufa, Annabi sai ceto. Daddo tace.
"Asiya dai ɗiyar ƙanwar Yaya uwa ɗaya uba ɗaya, ita Shehu zai aura Malam? Ai ana barin halas dan kunya, duk matan da suke a gari, baiga wacce tayi mishi ba sai Asiya, yarinyar da taje birni ta gama buɗe idanunta a gidan aiki da aka kaita. Ta Asibi tama rasa tacewa, ta rasa dalilin da yasa ƴar uwarta bata ƙaunar farin cikinta, gashi su biyu rak iyayensu suka haifa. Taso ta Auri malam Zangina dan taso ta ribaceshi ya jiya ma Ta Asibi baya. Amma da yake yafi sha'awar mace mai alkunya ne yasa yaima Kande tawaye. Da bata samu hakan ba saita ƙulla zazzafar gaba da ƙiyayya a tsakaninta da ƴar uwar tata. Ta Asibi kasancewar itace babba, sai taita yin haƙuri da halayyar Kande, taci gaba da janta a jika, taci gaba da ziyartarta tana kuma yi mata alkairi. Shine daga baya ta saki jikinta, ashe ta ciki na ciki. Baƙin ciki Ta Asibi ta dinga haɗiya. Malam yace.
"Ta Asibi naga kin ƙume, abinda nake so dake shine. Kuyi haƙuri ku duka, kuma ku taushi zuchiyar Laila ta daure tayi ma Shehu biyayya akan auren ƴar uwarta da zaiyi. Taci girma ta kame kanta a matsayinta na babba. Kuma, ku daure karku nuna ma Kande wani abu na sosuwar rai, gudun lalacewar zumuncinku, da Laila da Asiya duk naki ne. Abinda Shehu yayi ba laifi bane, tunda ba Allah ya saɓa ma ba. Sai dai yin hakan ya kaucewa al'adar malam bahaushe mu da aka sani da yakana da alƙunya. Kande zata zo yau haka Malam Buban ya faɗa mun." Yana kai aya ya kurkure bakinshi da ruwan buta yaja langar abincinshi, ya soma cin gwaɗon zogale. Bai idasa gama cin zogalennanba saiga sallamar Kande da ɗan buhun kayanta a ƙunshe, Asiya na biye da'ita. Ta Asibi ta kallesu dukkansu tana jin wani zafi da zugin Kande. Malam Zangina ne yai mata ido, saita ɗan saki fuskarta.
"Kande kune tafe a kwanɗeɗiyar ranar nan? Maraba lale, sannunku da zuwa Asiya" Cewar Daddo kenan dan Ta Asibi ta kasa iya sarrafa harshenta balle tayi musu sannu da zuwa. Kande ta ya da buhun kayanta, tana faɗin.
"Wash Allah makashin kakata Rakiya. Malam Zangina yau baka fita kasuwar bane?" Cikin girma yace.
"Nafita. Abinci dai nadawo inci, sai in koma Jafaru shima saiya je yaci. Sannunku da Hanya." Gaggaisawa akayi dukka. Malam Zangina ya wanke hannunshi, yai musu sallama ya fice."

Laila:
Ina tsaye ina share hawayena, na jiyo shigowar Inna Kande, kasancewar tana da ƙarfin murya. Da sauri nashare hawayena. Na shinfiɗe Ɗahiru na fita.
Inna kune a tafe? Asiya hmm ai nayi fishi wallahi kuwa" Kusa da Inna Kande naje na zauna,muka gaggaisa. Baki ɗaya saina kasa gane ma Asiya dan ko fara'a taƙi yi mun. Saɓanin da, da in muka haɗu tamkar zamu cinye junanmu, hira kuwa sai mun raba dare munayi. Saita tunomun zance da take rakani wajan Shehu in yazo, muita wasa da dariya. Maganar Inna Kande ce ta katse mun tunanina.
"Laila ashe mata maza kuma muka samu? Kaik abun baiyi daɗi ba. Dan samuwar yaronnan zai iya taɓa duniyarki, an riga an canfa irin haihuwarsu." Dam gabana ya faɗi har nake jin hawaye na shirin subce mun. Daddo tace.
"Wannan duk canfinmu ne Kande na malam bahaushe. Ba wani abunda zai samu Laila sanadin haihuwar yaronnan sai alkhairi. Ke Laila shiga ɗaki jikinki ɗanye ne. Yanzu ma zanzo muyi wanka. Kici gaba da kwanciya a gadon ƙasannan." Jikina a saɓule na miƙe, kobi ta kan Asiya ban sake bi ba.

Ta Asibi:
"Sai muka ji biki Malam yana shaida mana, ashe Asiya Shehun Laila zata aura? Shehunma bai jima da tafiya ba. Allah ya sa gidan zamanta ne" Cewar Ta Asibi kenan. Kande duk rashin kunyarta sai taji nauyi ya rufeta, nan ta shiga kame_kame dasokiburutsun zance"
"To ya zanyi. Buba ne ya ɗaure mata gindi. Har duka nayi mata, amman ta kafe sai shi. Wai tun lokacin bikin Lailan suka soma maganar aure. Yaya Abinda Allah ya nufa saiya faru. Masu iya magana sukance matar mutum. Shine na tawo da'ita zan kaita wajan Laraba ta zauna a can, ta dinga yi mata ƙunzugun lalle. In yaso in bikin ya rage kwanaki, saiki tawo da'ita Yaya" Da Daddo da Ta Asibi sun sha ruwan mamaki. Amman haka suka kanne, Kande ta kwana washe gari ta juya. Ta Asibi ta ɗauki Asiya ta kaita gidan Laraba. Kwananta bakwai a gidan Laraba, ana takwas ne Ta Asibi dasu Nazeefa suka ɗunguma zuwa Dutsen ma dan gudanar da biki. Laila tana nan gaho bata san wa Asiya zata aura ba. Har sai bayan da aka kammala biki Amarya ta tare a ɗakin angonta. Sannan suka zaunar da Laila dan faiyace mata halin da ake ciki.

Laila

Mrs Bukhari

[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: *_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
Chapter 28 · 0% Book details