Sashe 10
Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
In dare yayi ko wacce zata dafo abincinta, sunan abin alibidi a yi taci a dakin amarya, samari su cika kowa da budurwarsa yaci abinci ya bata kudi juma'a. kafin hakan da safe zuwa dare dangi za su yita kawo gudummowarsu atara kaya a fitar da tsaraba kaya Lodi_ Lodi akai gidan su ango" Asabar: Yinin gidansu ango, za'a yanka tunkiya abawa "yan matan amarya wuya dashi za suyi abinci suci idan anzo cin abincin, sai asa zobe aqasan abincin aboye ana cikin cin abinci wacce ta zaro zobe ita za'ayita tsokana" Lahadi: kashe wuta, za,a kawo ma amarya sauran kayanta a wanke tukunyar da'aka,aro, baqi kowa ya tafi biki ya qare. Haka al'adar bikin aure a Saleri yake, har gobe, amma bamu san dame jibi zata zo ba. Haka ne ya gudana a bikin Yawale. Ni kuma inata faman jinyar kaina, na zama abun ƙyama babu mai raɓata, aka yi ta mun waƙe_waƙe a tsakar gida. Yawale kuwa bana ma jin ɗuriyarshi sam tunda ya tare a ɗakin amaryarshi. Sai a bakin matan gida nake jin sunan Amaryar Yawale wai sunanta Kumatu. Amarci Yawale yake ragargaza shi da Amaryarshi Kumatu, dan ina jiyo labarin yadda suke gudanar da amarcinsu a bakin matan gida. Ni dai ina ɗaki ina jinyar kaina, da zuchiyata, dan in nace bana kishi ma, na yaudari duk wanda zai karanta labarina. Ana washe gari sati biyu da zuwa na asibiti, na fito da zummar zuwa ɗakin amarya dan inyi magana da Yawale, ganinshi ma ai yafi ƙarfina a yanzu. Gabana sai faɗuwa yake yi, dan bansan yanda zamu kwashe da Yawale ba. Amma na shirya duk abunda zance mai, dan dai ya barni inje koyon sana'arnan. Assalamu alaikum' Assalamu alaikum" daga ciki na jiyo muryar kumatu tana cewa. "Wata sabuwar alaranmiya muka samu ne a gidan? Koma waye in zai shigo ya shigo. Yawale yace "Musina ce, uwar iyayi ake faɗa miki" Da ba dan ba dan ba da yau anyi badan, dan ji nake kamar in shiga in shaƙo wuyan Yawale inta jibgar matsiyaci har sai naga ya dena motsawa. Jiki a mace nasa kai na shiga ɗakin. Yawale yana shingiɗe a ƙasa anyi mishi shinfiɗa irinta sarakai. Yana kan faifan tum_tum, guiwar hannunshi dafe da tum_tum. Ga gashsshen zabo a gabansu suna ci, harda lemun lamurje a gabansu, Kumatu sai wani fifita take yi mishi, harda yi mai sannu, kamar wanda jaki ya ka dashi. Ɗakin nabi da kallo, caɓi lallai duk inda akayi Kumatu Mahaifinta tahirine dan an zuba mata dukiya a ɗaki. Gado biyu ne a ɗakin, maulidi da bono. Ga kwaba bango guda mai ƙofofin glass, can saman kwabar ma tangaran aka jera mata, cikin kwabar kuwa harda samira mai kala. Ga kwalla hawa kusan goma, ga fanteku suma hawa hawa, haka kumbo ma hawa hawa. Bango guda kuma akai mata jeren tasoshi sama da seti sittin. Ga tum_tum guda uku tare da faifain shi. Ga ƙore a rataye a ragaya fin goma, ga shinfiɗa mai taushi a ɗaki, sai ƙamshin turaren binta sudan ke tashi. Ita kuma Kumatu sai ƙamshin turaren jan miski take yi. Ajjiyar zuchiya na sauke, inajin nunfashina na bazaranar ɗaukewa. "Musina ya kamata ki faɗi abunda ya kawo ki ko? Sabida kar kiyi ma Kumatu fitsari a ɗaki." Cewar Yawale kenan. Buɗar bakin Kumatu tace. "Ga fitsarin manya da mugun zarni" Dauriya na aro na yafa ma kaina. Na cije nace. "Dama gobe ne ranar komawa asibiti. Kuma ita likitan tace daga gobe kullum zanje asibiti harna tsawon sati biyu..." "Bani da ko ficika Musina, ba kina da kayan jere a ɗakikin ba? Ki kaɗar dashi ki samu na magani, amma ni in ba wajan maganin Hausa za'ajeba. Ficikata Kwarankwatsa ba zatai ciwon kai ba." Murmushin takaici nayi na dubeshi nace. "Umarnin zama a gida nake son ka bani kawai, domun bani da ikon fita ƙofar gida ba tare da izininka ba. Ficikarka bana buƙata." "Umma ta gai da Asha, Allah raka taki gona, can dasu gada. Dama jarabarki ce tasa kika dawo gidan ma. Aini cewa nayi sai kin warke kya dawo." Da dai na riga naji abinda nake son ji. Ban jira ya haɗiye yawu ba nayi ficewata a ɗakin, zuchiyata sai suya take yi.