← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 40

Sashe 26

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
[27/01, 11:04 am] BADI'T IBRAHIM: Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_

*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_

*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_

_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_

1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._

_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*

_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_

MRS BUKHARI
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI
GAWURTATTU UKU

LAMBA TA GOMA SHA TAKWAS:

Hawayene suke surnanowa ta gefen idona, suna sauka a matashin da kaina yake. Yau ni Audu ya daka a gaban yarana, da girmana yasa hannu yaimun dukan da har saida aka danganani da asibiti? Lallai na yarda Hindu ta shiga ta fita, ta cusa ƙiyayya mai ƙarfi a tsakanina da Audu. Duk da shima yana da nashi halin muguntar. Dan tun kafin Hindu tazo yake bani kashi. Shatu ce ta juyo, sai muka haɗa idanu. Kuka ta fashe dashi, wanda na kasa tantance na menene.
"Mama sannu kin farka? Basira maza kirawo mana likita, kice ta tashi. Jiki a saɓule Basira ta fita. Da idanu kawai nake binsu, ko ina ciwo da tsami yake yi mun a jikina.
Ina Usman Shatu?"
"Usman, yana gida, Kawu Ɗan lami yana jinyarshi, Shazili ya ƙarya mishi mishi hannu." Wasu irin hawayene masu ƙarfi suke ta ƙoƙarin makanta ganina. Har harshena yana sarƙewa nace.
Me ya haɗa Usman da Shazili, har abun yakai yake son durƙusarmun da yaro? Allah kana gani." Zaliha tace.
"Sabida ya riƙe hannun Baba sunyi kokawa, yana ƙoƙarin ƙwatarki, shine Shazili ya ɓalla hannun nashi. Kuma suka rufar mishi da duka, shi da su Yaya Shagari, da Auwalu. Yanzu haka mun shigar da ƙarar Baba Hindu, da shi kanshi Baban, da Shazilin. Kuma ni kotu zamu shiga. Zamu kwato muku hakkinku, kuma duk wani hakki da Baba ya tauye mana, zamu nemi kotu ta kwato mana hakkinmu. Lokaci yayi da baza mu iya zura idanu Baba da Hindu suci gaba da takaki ba. Ɗaukeki daga gidan zamuyi ma." Mari na dallama Zaliha, wanda saida yasa ta miƙe tsaye a zabure. Take tausayinta ya kamani. Nasan yarana sune gata na, na gode ma Allah daya bani aron lafiyar da na dinga neman kuɗi, badan komai ba, sai dan in haskama yarana hanya. Haƙiƙa ni kaina na ƙudurce a raina, ƙarshen zamana da Audu yazo kenan. Sai dai bazan so yaranshi su jashi a ƙasa ba. Duk lalacewar masa tafi ƙarfin kashin shanu.
Uban naku da matar uban naku, da ƴan uwan naku kuka miƙa sunayensu hannun hukuma? Ashe boko da sanin ƴancin kai shima hauka ne? Albaka nake fata kuyi a rayuwa, fatana ku rabu damu lafiya. Wannan jikin ya saba da wahalar Audu tun kafin kuzo duniya. Ku yi haƙuri ƴaƴana ku janye, in dai harni na tsugunna na haifeku." Basu da yadda zasu yi, dole suka ce dani sun janye. Kwanana shidda a asibiti aka sallameni. Babu laifi fuskar tawa ta ɗan saɓe. Kai tsaye su Zaliha suka wuce dani gidan da suke zaune. Suka kaini har gidan wata dattijuwa data kasance uwar ɗakunsu. Nayi ta binda da godiya. Muna zaune da daddare a falo, muna cin gashashshiyar kaza. Yarana sai jana da hira suke yi, burinsu suga ina walwala. Amman ina, sai dai na samar musu ƙirƙirarren farin ciki, badan yaudaraba sai dan in basu nutsuwa. Kwana na biyu a wajansu, muka dawo gida. Matan gida, da maƙota sai aukin sannu suke yi mini. Masu gulma nayi, masu zunɗe nayi. Hindu kuwa muna haɗa idanu ta fashe da dariya, ta shige ɗaki tana wani rausaya sai kace yarinya. Ɗakin da Usman yake jinya muka shiga. Yana zaune ana shafa mishi kitsen damo a hannun nashi. Ɗan Lami yana gefenshi. Sai aukin sannu muke ma juna ni da Usman. Saida mai maganin ya fita, Ɗan Lami ya faɗa ni da faɗa.
"Ke wacce iriyar shin me ruwa uku ce ( Sha_sha_sha) Yara suna son kwato miki darajarki, amma kina gwalesu. Kinfi sha'awar ciwon zuchiya yayi ajalinki kenan? Ya zama dole a shigar da ƙararnan. Dan wallahi abun ya isa haka tura kuma takai bango. To bari kiji abunda yake faruwa tun ranar da aka fita dake jina_jina a gidannan. Audu har fada yaje, ya bada sanarwar duk saurayi, ko tsoho, ko dattijon da ya shirya aure, ga yara a gidanshi kyauta, sadaki kawai za'a biya. Ba wannan bane abun mamakin ba. Wallahi har aka kwana aka wuni, babu wanda yace yanason waɗannan yara. Sai gulmace_gulmace aketa faman yi a gari, wai Shatu ta kawo daduro har gida. Hindu ta dinga bi gida_gida tana sake tabbatar ma da mata cewar kama Shatu akayi da daduro a ɗakin mahaifiyarta. Jibi abinda suka ma ɗanki, ke kanki jibi fuskarki. A wannan karon dole Audu ya sakeki." Goggo Rakiya wacce ta jima da tsaiwa a dokin ƙofa, kuma a kunnenta akayi bayanin komai tace.
"Ya zama dole ki yarda da abunda ƴan albarkar yarannan suka zo mana dashi. Da ba dan sunyi iliminba, da haka zaku zama ɗaya daga ke harsu, shin me ruwa uku kawai ( Sha_sha_sha) Zaliha kuyi abunda kuka saka a gaba. Allah yayi muku jagora, sai inda ƙarfina ya ƙare ni kuma" haka suka sani a gaba har saida na amince a maka su Audu a kotu ala tilas. Cikin kwana biyu, Zaliha ta dawo da takaddar sammaci. Ɗan lami, da Goggo Rakiya su suka tafi da sammacinnan har fada.
Ni kuwa koda muka dawo gida, jikina sam yaƙi daɗi, ga tunane tunane da suka addabi zuchiyata. Ga habaice_habaicen Hindu wanda ta matsa mun lamda dasu a kwanakinnan. Audu kuwa sai sabgogin gabanshi yake yi, shi da Shazili gani suke zasu ci banza. Ƙuta nayi nace.
Mu zuba, inda dane bani da ƙarfin ramawa, bani da muryar da za'a saurari kukana. Yanzu karana ya kai tseko"

Fada:
"Allah ya taimaki mai gari. Wannan takaddar sammacice daga kotun birni. Ta Audu ce mijin ƴarmu, da Shazili, da Hindu, Yaranshi ne suka doka shi a gaban kuliya, suna neman a ƙwato musu hakkinsu dana mahaifiyarsu. Tun daga lokacin da aka haifesu har zuwa girmansu. Domun baisan komai nasu ba. Kuma ya cuskuna ma uwarsu ainun. Dan haka suna neman hakkinsu a wajan Audu." Goggo Rakiya na kaiwa nan, fada ta ɗauki tafi da sowa. Saida mai gari ya dakatar dasu. Ya dubi Goggo Rakiya yace.
"Rakiya, ni ina ganin da anyi sulhu anan fada ta da zaifi. Duk da nasan dolen Audu da Shazili su amsa kiran kuliya. Amma ya yara zasu kai ƙarar mahaifinsu? Shifa tuwo ba'a sauya mishi suna.
Goggo Rakiya tace.
"Amma in ba'a sauyama tuwo suna, ai hannunka yana ruɓewa ka je asibiti a yanke maka ko? To da kabarshi mana kaga in baici gangar jikinba duka." Fada tayi shiru kowa saida ya kaɗu da wannan lamari. Aka saka su Zaliha a gaba akaita tattaunawa a kansu, cewar baza suyi albarka ba." Mai gari ya tashi fadawa biyu yasa suyi mishi kiran Audu."
Chapter 26 · 0% Book details