← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 40

Sashe 17

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

MUSINA:
Ina sauka a bodi na nufi gida a jiƙe sharab. Da malam naci karo a zaure.
"Musina ince dai lafiya na ganki da kaya niƙi_niƙi a ɗaure, karki sake ki cemun yaji kikayo"
Babu komai malam, a asibiti ne ake buƙatar in dinga zuwa kullum daga yau har nanda mako biyu. Shine Yawalen yace in dawo gida tunda kusa ne" Nazarina yake tayi, kafin yace.
"Kin tabbatar shi yace ki zauna har sai kin kammala da asibiti, kuma kin tabbatar ba matsa mishi kikayi ba, hakan kuma bazai zama kin shiga hakkinshi ba?
E Malam " Kawai na iya cewa, tsorona kar malam ya rubto ni.
"Ki shiga ciki, to ki ajjiye kayan ki sake wasu, saiki tafi asibitin. Ajjiyar zuchiya na sauke banyi zaton abun zai zo mun da sauƙi haka ba. Baba Lami na ɗaka na shigo. Na iske Inna bata nan.
"Musina kece da kaya, kaddai sakinki Yawale yayi?" Harta soma fitar da kwalla.
A'a inna Lami ba sakina yayi ba. Sabida yanayin asibiti ne, kuma Malam ya amince." Baki ta washe, ta kunto Ƙasimu a bayana. Sakaki na faɗa nayo wanka da ruwan sanyi naji daɗin jikina. Kaya na sake nayi ƙunzugu na fito.
Inna Lami zan tafi, Ƙasimu zan barshi a gida, bashi da rigima, in yayi kuka a ɗirka mishi kokko. Murmushi tayi mun da halama taji daɗin dawowa gida da nayi. Tace.
"Amma fitsarin yana raguwa kuwa?"
"Sosai satin farko nasha wuya ko baccin kirki banayi, inda kika san ruwan jikina zai ƙare, ni kuma na dinga shan ruwa. A sati na biyu saina samu sassauci, in nayi ƙunzugu yana yin awa biyu bai jiƙe ba." Baki ta washe tace.
"In sha Allahu ba za'ayi miki aiki ba. Ko Hanne mijinta da malam ne sukai ajalinta, saida komai ya kwaɓe aka kaita asibiti. Maza jeki abunki." Fita nayi ina jin wani sanyi a raina wanda bansan ko na meye ba. Babu layi sosai yau a asibitin. Waje na samu cikin ƴan uwana masu irin lalurata, a haka har layi yazo kaina. Likita tayi murna da ganina, kuma na faɗa mata yanayin jikin nawa, tace.
"Jiki yayi kyau Musina, kuma babu maganar aiki. Zan ƙara miki sati biyu, daga sati biyu sai in baki sati ɗaya, kafinnan muna fatan fitsarin ya daidaita, ki dinga jin taruwarshi a ƙasan mararki. Ya batun koyon sana'ar fa?"
Daga nan can zanje Likita mijina ya amince"
"Naji daɗi, ki dage ki saka himma akan abunda zaki koya, ai zai taimaka miki sosai, kuma zaki kula da kanki da yaranki ma gaba in sha Allah. Godiya nayi mata na fita. Kai tsaye zuwa Azare firamare. Mata na hango danƙam, kai na girgiza.
Ashe haka masu lalurar yoyyon fitsari muke da yawa? Allah sarki mata, duk wata wahala a kanmu take ƙarewa, sufa maza ƴan gata ne. Sai dai su je nema, su kawo, su huta da mace, shikenan aikinsu. Mu tare ake yin nomar hatsin ma damu. Mata mu ɗauki ciki, muyi aikin gida, mu haihu, muyi reno, muyi tarbiyya, mu kula da mai gidan. Banda sauran ƙananun aikace'aikace na yau da kullum MATA IYAYEN GIJI ( YA ALLAH KA SANYA HASKE DA FARIN CIKI A ƘIRJIN KO WACCE UWA). Form na nuna ma mai tsare da ƙofar shiga makarantar, sannan ya barni na shiga. Na samesu anata ciki_cikin rarrabe ajujuwa. Ni faɗawa nayi ajin koyon mandula, da sabulun soda, da omon gari. Koda aka gama ware mu, lokacin harya wuce dole aka tsaida komai kan sai zuwa gobe, taran safe za'a soma. Tare da ja mana kunnen yin latti.
Washe gari da sassafe na taya su Inna aikace_aikace. Nayi wanka tsab, naba Ƙasimu mama yasha yayi gyatsa, na miƙama Inna Lami shi. Dan a ɗakinta na sauka. Ina shirin fita kenan Yaya Harira babbar ƴar inna Lami tazo ita da yaranta daga jama'are. A gurguje muka gaisa na fice.
Naje na samu dab za'a soma koyar da sabulun soda.
"Mata Assalamu alaikum barkan mu da safiya, yaya jikin naku?" Muka amsa mata da "Da sauƙi"
"To masha Allah. Ko wacce dan Allah ta nutsu, kuma ta saki jikinta, babu mai hantararta ko tsangwamarta, banda surutu kuma. Wannan sana'o'e zamu koya muku su kyauta ne, sabida matanmu na karkara suma su tsaya da ƙafafunsu, wata gidauniyar mata ce ta ɗauki nauyin yin wannan abun aikhairin, mai suna ( GASKIYA DOKIN ƘARFE, WANDA ANTY ZARATU FASKARI TAKE JAGORANTA. FARAR MACE ALKYABBAR MATA, UWAR GIDA SARAUTAR MATA )daga Faskari muke, mai gari shine mai masaukinmu. Da fatan zaku bamu haɗin kai.

Yanda ake haɗa sabulun soda.

Wannan manja ne na miya, wanda ake cireshu daga jikin kwakwar manja.
Wannan kuma costic soda.
Wannan ruwa ne
Waɗannan sune kayan da zamuyi amfani dashi.
Chapter 17 · 0% Book details