← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 40

Sashe 7

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_

*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_

*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_

_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_

1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._

_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171

*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*

_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_
MATA IYAYEN GIJI

BADI'AT IBRAHIM (MRS BUKHARI)
( GAWURTATTU UKU)

*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*

SAMFOTI

LAMBA TA SHIDA

Da ƙyar ɓarawon bacci wahalalle ya kwashe ni.
Kamar a mafarki naji ana tokarata da ƙafa ana shureni. Da sauri na farka tare da saurin zama. Yawale na gani a tsaye a kaina, hancinshi a toshe.
"Kinji kunya wallahi Musina, fitsarin kwance da girmanki, jibi yanda fitsarinki ya fita har waje yana gudana. Da sakel gaskiya." Tsaki yaja ya tsallakeni ya tafi sallar asubahi. Cikin hanzari na miƙe, kayan fitsarin na haɗa dana jiya du na wawwanke na shanya. Ruwa na samu na wanke ɗakin tasa na goge, turare ɗan goma na yayyafa a ɗakin. Sannan nayo wanka da ruwa mai ɗari. Ina idar da Sallah, Ƙasimu ya farka da kuka. Nima hawayen nake ta zubarwa. Nono na zura mishi a baki. Babu ko sallama Yawale ya shigo. A kaina ya tsaya ƙiƙam kamar ɗan doka, sai toshe hancinshi yake yi, yana mun muzurai.
Ina kwana Yawale?
Baice dani komai ba, ban daddara ba nace.
Zuwa ƙarfe nawa zamu tafi can ruggan?" Ananne na fusata shi ainun, dama mai neman kukane aka jefeshi da kashin awakai.
"A haka zamu je rugga muna tafe kina fitsari kamar wata tunkiya kenan? Allah ya tsari gatarina da saran shuka. Ke bari kiji abunda nake so dake shine. Ki shirya tsab ki tafi gida, ayi miki magani a can ala bashi in kika warke sumul sai in je in ɗakko ku. Bazan iyaba, kinji zarnin da ku ke yi daga ke har yaron kuwa?" Yana kaiwa nan ya wuce wajan kwalla inda anan kayanshi na sawa suke. Kaya ya sake ya fice. Baima kalleni ba balle ya tausaya mun. Murmushi kawai nayi. Na jima da fahimtar halin maza, lafiyar mace da ƙuruciyarta kawai suka iya cinyewa. Da zaran ciwo ko girma ya saukar mata, shikenan a wajansu ta zama bola, daga wannan lokacin zasu iya wanko budurwa tsarar jikarsu ma su aura, tunda su tsufa bai fiye shafarsu kamar mu mata ba. Barinma mazan ƙauye, wanda ƙashinsu ya ginu da tuwon dawa, da zogala, da yaɗiya. Ƙasimu na saɓa a bayana, na fita tsakar gidan. Kai tsaye shiyyar su Baba Hauwa na nufa. Bayan na gaisheta ne, na shiga yi mata aikace_akace kamar yadda yake bisa al'ada da tarbiyya irinta malam bahaushe. Na gyare mata ɗakinta tass. Na fito da wankin kayanta kala uku na wanke mata tas. Sannan na koma ɗaki na sake ƙunzugu, na wanke wanda na cire na shanya. Madafi na nufa wajan facalolina. Bayan mun gaggaisa kuma sai muka shiga aikin ɗunamen tuwo da dama ruwan kokko. A'i tace.
"Musina sai kika ji tafiya ta kama su Yawale da jamilu ko?" Tsabar takaici E kawai nace mata naci gaba da abinda zai fishsheni. Damuwar dake gabana ma tafi ƙarfina, dan haka bazan ɗaura damuwar Yawale a raina ba. Rana fatse_fatse ina shirin kulle ɗakina zan tafi gida. Sai kawai na jiyo ihun yara a waje, ana cewa.
"Ga almajirai sunzo ganin gida, ayi noma a koma makaranta, dan damuna tana dab da tsaiwa, harma munje munyi sharar gona. A guje suka shigo gidan tuɗuɗu. Ina gani su A'i suka rungumi yaransu, amma irinsu Laure dani masu na fari ba damar ko kallo ka yawanta yi. Yanzu sai ace kayi fitsara, kai da ɗanka, sai a iya zazzaginka ma, a gaban yaran. Shi yasa yaranma suke tasowa basa ganin girman mu, yaro a ƙauye uwarshi zata iya cewa yayi mata abu, ko yaje mata aika, kakarshi wato uwar miji tace bazashi ba, a gabanshi kuma. Da sun girma kuwa sai abinda iyayensu maza suka ce dasu, shawara ma yaro bazai naima a wajan uwarshi ba. Banyi aune ba Idi ya tawo a guje ya ruƙunƙunemun zane yana dariya. Kallonshi nayi da kyau, yaro ɗan shekara Shida, wanda bai wuci inyi mishi wanka, da wankin kashi ba, shine ɗawainiyar kula da kanshi ta rataya a wuyanshi, kaico. Hannunshi na jaye na ɗan tureshi gefe badan raina yaso hakan ba, sai dan gudun matsalar da kaje kazo tai sanadin auren nawa baki ɗaya ma. A guje yayi cikin gidan yana kwaɗama Baba Hauwa kira, dama a ɗakin yake. Inba dai idanuna basu suna mun dai_dai ba, sai naga Idi kamar ɗingisa ƙafafunshi yake yi. Kulle ɗakina nayi na wuce shiyyar su Baba Hauwa.
Sallamu Alaikum, sannu Baba." Da harara ta bini.
"Lafiya da dawowar yaro zaki shiga yi mun sunturi a ɗaki, menene to rasa kunya ɓeran danga? Wallahi ki kiyayeni Musina, inba haka ba kina dab da barin gidanma baki ɗaya" Kai na sauke ƙasa kawai, inason kallon Idi ko zanji daɗi amma babu wannan damar.
Gida zani shine nace bara inzo inyi muku sallama "
"To ki gaida magabata" Tuwo ta tura ma Idi a kwanon samira. Tashi nayi na fita. Naje naima Baba Huwaila sallama, sannan na kama hanyar zuwa tashar bodi. Ina tafe harna kusan isa tashar, sai kawai naji an riƙe mun mayafina ta baya. Juyowar da zanyi muka haɗa idanu da Idi. Murmushi muka sakarma juna dukkanmu, hannunshi naja zuwa gefe can.
Yaya karatun kana taɓawa ko, kuma kana maida hankali a karatun dai ko?" Hawaye ya soma sharewa, gefe da gefen bakinshi duk ya fashe, ga wani ƙaton makero a kanshi sai ci yake. Tsugunnawa nayi nace.
Ya'isa me yasa kake kukan to?"
"Baba kice ma Baba ya cireni a makarantar, kullum da duka da ruwan sanyi ake tashinmu, kullum bana samun abinci inci da daddare. Malam Zulƙe kuma yaita samu a mari, ƙafata ciwo take yi, in ranar labara bamu bada kuɗin laraba ba, saiya samu a ɗakin duhu mu kwana." Hankalina naji ya tashi ainun, da rai na yarona yana kwana da yunwa, ya kwana a mari, da ɗakin duhu. Inna ci gaba da zura idanu inaga kamar banyi ma shi kanshi Idin adalci ba. Tuno da zafi da azabar dake cikin naƙuda nayi. A lokacin dana Haifi Idi saida na kwana biyu cir jiri na ɗibata bana iya gane kowa. Amma yau dubi halin da mahaifinshi ya sashi a ciki. Ƙafarshi ya nuna mun, ƙarfen mari duk ya fasa mai idanun sawu.
Kayi haƙuri zan roƙeshi ya barka a gida, yanzu ka koma gida kaji, gidanmu zanje. Bari in baka nera uku ka sai marau_marau nasan kana so." Abunka da yaro sai kuma ya washe baki, ina bashi ya kwasa a guje yana jujjuya kai irinna murnar yarinta. Murmushi nayi, tare da share hawayen daya gangaro a kuncina. Munyi tafiya sosai, sai wajajen la'asar na isa Azare. Gida na wuce, na riga na jiƙe sharab ruwan fitsari sai wanke mun ƙafafu yake yi. Ina shiga na zube a gaban iyayena mata.
"Lafiya Musina zaki shigo da kuka meke faruwa?" Cewar abokiyar zaman mahaifiyata, Innata tana zaune a turmi tana yanka kuɓewa zata shanya. Kallona kawai tayi, tana ganina tasan ina cikin matsala, amma sai cemun tayi.
"Ana miki magana kin tusa mutane a gaba kina kuka, ki sakko da goyon, ɗan baɗo yayi miki fitsari a baya." Ana cikin haka mahaifina ya shigo, shima ya tambayeni ko lafiya?"
Baba ciwon yoyyon fitsari ne ya kamani, kuma na roƙi Yawale ya kawo ni asibiti yace baida kuɗi, daga baya kuma yace in dawo gida, in ku kai mun magani na warke zai zo ya ɗaukeni." Inna Lami kishiyar mahaifiyata ta dubi mahaifiyata wacce suke kiranta Tarana tace.
"Tarana yau nake jin ɗan gatan uwa, wato mu nema mata lafiya, sai yazo ya ɗauki abunshi ko? Haka fa mijin Hanne yai mana sanadin mutuwarta." Inna dai bata ce komai ba sai haɗiyan ƙududu take. Malam Dauda mahaifina yace.
"Yawale baiyi laifiba ko a musulunci, da lafiya ya aureta, amman ku sani in wata lalura ta sameta yaji bazai iya zama da'ita, zai iya sauwaƙe mata. Lo kuma yaji bazai iya nema mata lafiya ba, zai iya turota wajanmu mu saimu nema mata lafiya, inta warke kuma yazo ya tafi da matarshi. Ku mata kun cika kacancana zancen da bai kai ya kawo ba. Ke Lami ɗauketa kuje asibiti muji me zasu ce, da kun gama ki wuce ki rakata ɗakinta, bata da wajan zama anan, nina haifeta bazan ƙi nema mata lafiya ba, amma bazata zauna mun a gida ba, hakkin cinta, shanta, makwancinta a wuyan Yawale kaɗai ya rataya." Inna Lami tace.
"Amma Malam ayi haka kuwa?
"Amma yi Lami, ga wannan jaka ɗaya ce ku tafi ku ga likita, ke kuma Musina ga muttala biyu ki riƙe, sai haƙuri. Ina kuka nace.
Baba dan Allah ka barni in zauna anan ɗin inna warke sai in koma" dubana yayi yace.
"Uwata in badan kinci darajar mai sunanki ba, dana baki kashi a gidannan ƴar jakar uba, ana nuna muku hanya kuna bauɗewa. Banyi zuchiya ba nace.
Baba wannan yaron ya dawo yau daga birni, amma yunwa tana damunshi, kuma idanun sahunshi du sun fashe sabida sashi a mari da akeyi a makaranta. Dan Allah ko zaka yi ma Yawalen magana yai haƙuri ya barshi a gida ya ƙara tasawa.
"Ke uwata tashi ki tafi. Yawale shi ke da cikakken iko a kanki da yaranki, ta yaro kyau take bata ƙarko, ke ashe in da kinsan wuyar da muka sha a almajirci zaki ɗauka baza muyi rai bane ko kiyi tunanin iyayenmu basa ƙaunarmu ne. Gatan da za'a nuna mishi kenan, ita rayuwa ƴar gwagwarmaya ce. Mu gashi yanzu mun gama tuni, kuma muna cin gajiyar almajirci. Lami ɗagata ku tafi. Abincinshi ya karɓa ya fice. Mahaifita ce ta bani kaya na sake, na sake ƙunzugu. Muna tafe ina kuka har muka isa asibitin, inna Lami sai rarrashina take yi, tana bani magana. Bamu samu likitan ƴan yoyyon fitsari ba, ranar Laraba kaɗai ake zuwa. Haka Inna Lami ta sani a gaba har gida. Bamu muka isa ba sai bayan magriba. Ɗakin Baba Huwaila ta kaini sabida tsabar kara irin ta iyayenmu. Sai Baba Huwaila ce tasa akayi kiran Baba Hauwa tazo.
"Ga Musina na dawo da'ita mahaifinta yace aba Yawale haƙuri ya barta ta zauna, zamu nema mata lafiya in sha Allah, daga asibitin ma muka wuto nan, sai ran laraba zamu koma dan bamu samu malaman kiwon lafiyar ba." Baba Huwaila tace.
"Musinan ce ba lafiya Lami? Ai mu bamu da masaniya, kinga Yanzu Yawalen ya bar nan ɗakin dawowarsu daga tafiya kenan shi da wanshi." Cike da mamaki Inna Lami ta dubeni. Labarta musu lalurar dake damuna tayi. Nan suka shiga sallallami, buɗar bakin Baba Hauwa tace.
"Ni ko ina da shawara Lami. Da kun bar Musina a gida tayi jinya, nake ganin kamar zata fi samun kulawa a can. Yawalen ma bikinshi shingin mako ɗaya zai auri ƴar aminiyata a can rugar malam harɗo can hayi, yau ɗinnan wanshi ya rakashi aka tsaida ranar, ga can lefen ma. Wasu sababbin Kumbuna na gani masu hawa uku, da babba da mabi da babba, da ƙaramin na saman sai walƙiya suke yi. Muƙut na haɗiye kibiyar kishi, idanuna suka cika tab da hawaye, ita kanta Inna Lami jikinta ya mace, tace.
"Ayya Allah ya sanya alkhairi, wannan amarya tako yi goshi. Baba Hauwa tace.
"Ku buɗa kuga kayan ciki mana."
Inna lami ta buɗa kumbunannan, kayan alfarma Yawale ya zuba ma amaryarshi, su atamfa mai ɗawisu, goji, banbalasta, leshi, karen miski, ɗankwali mai geza, ɗan duros, fatari, rigar mama, jan baki, gazal, sarkar murjani, da tsakiya, agogo, da takalma masu tsini, da mayafai. Kaya rigijibjib dai, dan banma gama kalloba, Inna Lami sai ɗaga kayan take tana mamakin irin uwar dukiyar da Yawale ya narka, amma ya kasa nema mun lafiyata. Inna Lami tace. "Amma Hauwa yarinyar nan a barta a ɗakinta ta zauna, zan dinga zuwa dubata, biki kuma da Yawale zai ƙara Allah ya sanya alkhairi."
"To tunda hakan kika ce ai saita zauna." Har ɗaki Inna Lami ta rakani. Sannan ta dawo ɗakin Baba Huwaila ta kwana. Ni kuwa ina kwance a ƙasa Yawale ya turo ƙofar ya shigo. Kuka ya samu inayi.
"Baki ji abinda bace miki bane shine kika wani dawo ko? To ga ɗakinnan ki zauna na bar miki. Fuu ya fice a ɗakin, kwanan damuwa da baƙin ciki nayi dare yayi mun tsayi sosai. Washe gari da sassafe Inna Lami tayi mana sallama ta kama hanya. Ni kuwa da wankin kayan fitsari na tashi. Labarin lalurata ya bazu har maƙobta, sai jaje aketa yi mini, Baba Hauwa tace in dena zuwa madafi aiki har saina warke. Ina dai zuwa inyi mata gyara, akan po nake zama a koda yaushe, sai zuwa dare kuma sai inyi ƙunzugu, kafin gari ya waye fitsari har gudu yake.
Yau Laraba, yau zan koma asibiti, amma na ƙudiri niyyar kai tsaye asibitin zani, gidan ma bazan shiga ba tunda ba ƙaunata suke yi ba. Ina gama aiki na nufi shiyyar su Baba Hauwa, na gyara mata ɗaki. A tsakar gida naci karo da Idi, murya ƙasa ƙasa nace dashi.
Ka sameni a bayan gonar mai gari yanzu, karka faɗama kowa" Fita nayi a gidan na nufi bayan gari. Zama nayi a kan wani kututture ina jiran zuwan Idi"
Chapter 7 · 0% Book details