Sashe 19
Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894
*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*
[08/04, 19:57] Mrs Bukhari: MRS BUKHARI.
GAWURTATTU UKU
Lamba ta goma sha uku.
Saleri:
Musina:
Ina shiga ɗakina na soma sauke jerena kab ina ɗurawa a buhu. Duk wani kayan ƙawa saida na cire na zuba a buhu, matan gida sai leƙowa suke yi. A'i uwar gulma matar Jamilu wan Yawale tace.
"Musina kaddai rantsuwar da Kumatu tayi a tsakar gidannan akan sai Yawale ya sakeki, itace tayi tasiri? Kumatu dama tace saita ɗaukeki akan yaranki" Wani ƙunci da tashin hankali ne ya shigeni, maganar A'i tasa na kaɗu ainun. Dan bana fatan in tsallake in bar yarana su rayu babu ni a kusa dasu. Amma na sani Kumatu bata isa tayi mun abunda Allah baiyi mun ba, kuma duk abinda zai faru a kaina, rubuce yake a littafin ƙaddarata. Murmushi na ƙaƙaro nayi ma A'i kawai, na kasa ce mata komai dan in nace magana zanyi to kuka zai tawo mun dole A'i taga rauni da gazawata, banma kuma san me zance ma A'i a matsayin amsa ba. Buhun na ƙulle na dubi A'i da tai kasaƙe tana kallon ikon Allah nace.
Taimaka ki ɗaura mun a ka A'i" Baki ta buɗe.
"Kaddai a darennan kike shirin tafiya. Baba Hauwa suna da labarin ɗanyan hukuncin da Yawale ya yanke kuwa? Wallahi karki tafi ki zauna, Kumatu ce ta haɗa komai ni dai nasan baki ma Yawale komai ba, sai haƙurin zama dashi ma da kike yi, kar ki barma yaranki abun faɗe Musina. Kallon dana watsa mata ne yasa tayi gum da bakinta, ta taimaka mun na aza buhun a kaina. Fita nayi daga gidan. Na kaima Uwa mai siyan kaya,ta siya amma tace mun gobe da safe inzo in amshi kuɗin. Godiya nayi mata na koma gida. Ƙunxugu na sake, ina zaune ina jan carbi hawaye sai wanke mun fuskata yake yi, roƙona da burina shine, Allah yasa in rayu tare da yarana har zuwa matakin girma, da mallakar hankalinsu. Ba dan ko da wasa ina sha'awar zama da Yawale ba sam, sai ɗan ɗorewar farin ciki, gami da walwalar ƴaƴana dana kasance musu bango majinginarsu"
A'i:
"Jamilu Yawale fa ya saki Musina. Ita kuma ta hau dokin zuchiya harta soma kwashe kaya ta tafi gidama yanzu maganar da nake yi maka, abun ya bani mamaki gaskiya" Dena cin tuwo Jamilu yayi, nomar daya yanko ya ajjiye.
"Ya saketa fa kikace? Lallai Yawale bashi da hankali, akan waccen figaggiyar Kumatun ya saki uwar Ƴaƴanshi daga yin sabon aure? Da safe zan je in yima Baba magana, su Baba Hauwa ma banyi tunanin in sun sani ba. Duk da dai naga sunfi ƙaunar yarinyar da Yawale ya auro, kuma Baba Hauwa ba zata ga laifinta ba Ɗiyar aminiyartace. Amma bari inje in samu Mudi mu tattauna" yana kaiwa ƙarshen maganarshi, ya wanke hannunshi a cikin kwanon da aka zubo mishi ruwan wanke hannun, ya fice. A'i sai kiranshi take, ita bata so akaji mutuwar sarki a bakinta ba. Gulma kawai ta kawo ma mijinta, kuma bata zaci zai ɗau abun da mahimmanci haka ba."
Jamilu:
Har yana tuntuɓe tsabar sauri. Ƙofar ɗakin Mudi yaje ya kwankwasa. Mudi ya fito daga shi sai godon wanda, yana lashe hannunshi da yayi jaga_jaga da miya."
"Yaya Jamilu lafiya kuwa, naga yanzu muka rabu?"
"Hmm Mudi kai dai bari wani labari A'i ta tare ni dashi. Wai Yawale ya saki Musina, harma ta tafi gidansu a darennan, kuma da kaya. Banyi tunanin yarinyarnan laifi tayi mishi ba. Tunda wannan laluri ya sameta, Baba Hauwa da Yawale suka ɗauki karen tsana suka ɗaurama Musina. Sannan munafukar amaryarshi ita take kuma ingizashi, tunda tasan tana da fada a wajan Baba. Baba Huwaila dai ita baka gane a ina take kasan ita in dai abu baiyi mata ba tana faɗe. Baba zamu je mu samu a turakarshi da safe, sai a kirawo Yawalen ya sanar damu dalilin da yasa ya saketa, mu kuma zamu je mu dawo da'ita. Kaje ka kwanta da safe ma tattauna." Mudi yace.
"To Yaya sai da safe. Amma abun baiyi daɗi ba gaskiya"
Musina:
A zaune bacci yai awon gaba dani. Sai cikin dare dana farka na gyara kwanciyata, bayan na ba Ƙasimu ruwa da nono.
Washe gari da sassafe na gama komai, na ƙulle ƴan kayana a ɗan kwali, na fito na kulle ɗakina. Kai tsaye na nufi ɓangaren su Baba Hauwa. Da Idi na haɗa idanu, ya sakar mun murmushi. Yana zaune yana cin tuwo.
"Ina kwana Baba?" Baba Hauwa tace.
"Lafiya, ina kuma zaki da sassafennan ina da zuwa gida?" Kai na kuma saukewa ƙasa. Shin wai me naima rayuwa ne ta juya mun baya? Yawale ya raboni da dangina, ya kawoni cikin nashi dangin. Ya juya mun baya, iyayenshi da ƴan uwanshi kab bana jin daɗin zama dasu, me nayi ma Yawale da rayuwa ne?"
"Ba magana nake yi miki ba, kin wani zo kin zauna mun ke da kike yoyyon fitsari, sale_sakin ki mun fitsari a filin ɗaki ko me? Yau ga hauka da naɗe_naɗe wai mutuwa taga ladani. Idi na kalla shima ni yake kallo. Ƙwalla ce take shirin zubo mun nayi saurin mayar da'ita.
Gida zani sai nan da sati biyu zan dawo. Yau zanga likita, kuma daga yau har zuwa sati biyun kullum zamu je" Baki ta taɓe tace.
"Da zan baki shawara da kinyi zamanki a gida, in kika warke fes saiki dawo ɗakinki, tunda yanzun ma ba rabon kwana akeyi dake ba. Jibi fa yanda kike zarni Musina" Kaina na ƙasa harta gama faɗan abunda yake ranta tas. Sannan na tashi na fita. Ƙunshin kayana na ɗauka a bakin ƙofar ɗakin, na fice a gidan. Ajjiyar zuchiya na sauke da naji iskar waje ta doki gangar jikina. Tsabar takura ji nake yi kamar iskar waje data gidan Yawale akwai banbanci. Ina tafe ina tunanin rayuwa, da irin yanda Yawale ya soni kamar zai halaka kanshi, a lokacin har tausayin irin son da Yawale yake yi mun nake yi, dan gani nake yi in mutuwa ta ɗaukeni da ƙuruciyata, Yawale zai iya tagayyara. Hmm ashe shigo_shigo babu zurfi ne kawai, gadar zare ya saƙamun na faɗa ya barni da wayyo Allah.
Jamilu:
Sallama Jamilu yayi a bakin turakar mahaifinsu shi da Mudi, suna jiran a basu izinin shiga.
"Jamilu shigo mana, ina kishingiɗe jikinnne ba daɗi. Shiga suka yi, suka tadda mahaifin nasu a kwance, Baba Huwaila na gefenshi. Baba Hauwa ce ta shigo da sallama. Amsa mata su ka yi, kana ta nemi waje ta zauna. Saida aka gama gaggaisawa, Jamilu yaima mahaifinsu malam Idi bayanin abunda yaji daga bakin A'i. Zama malam Idi yayi, saida ya jingina kafin yace.
"Shi Yawalen ne ya saki Musinar, to akan me, wani abunne ya haɗasu? Jamilu yacr.
"Baba bamu sani ba, amma a daren jiya tabar gidan ta kasa bari gari ya waye." Baba Hauwa tace.
"Wai wacce Musina ake magana, matar Yawale? Yanzunnan fa muka rabu da'ita akan zata je gida sai nan da sati biyu zata dawo. Sakinta ashe yayi?" Jamilu yace.
"Ha'a nifa tun daren jiya A'i ta faɗa mun ita da kanta ta taya Musina ɗaukar kaya." Malam idi Yace.
"Karawo shi Yawalen shi kaɗaine zai faɗa mana gaskiya, amma wallahi in kuwa sakin yarinyar nan yayi ni dashi ne a gidanan"