Sashe 34
Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
daɗe sosai a asibiti, dan sai da ya warke tsab ya dawo cikakken namiji, sannan aka sallamemu, muka dawo gida. Haka rayuwa taita garawa, abubbuwa da dama sukaita faruwa, Su Karima sun dawo ganin gida, bayan shekara guda. A lokacin nace ma Shehu yarana bazasu koma birni ba. Yanzu ina da arzikin da zan iya tallafin ƴaƴana. Dan jam'iyyar matan Arewa tayi mun dukkan alkairai, ta dalilin wannan ƙungiyar, naga gwamnonin jihohi da dama, kuma sunyi mana alkhairai masu tarin yawa. A yanzu na zama fitilar dake haskaka gidan Shehu, yaran Asiya duk biyun da ciki suka dawo daga gidan aikinsu. Ni naja gaba aka ƙwato musu hakkinsu, mune har kotu, sun haihu, Asiya taci gaba da rainon yaran shege a gabanta. Rayuwa kenan, haƙuri shine jigon rayuwa, mai haƙuri shike dafa dutse yasha romonshi. Iyayenmu duk Allah yayi musu rasuwa, mun zama dattijai a cikin gidan. Ɗahiru ya zama babban ɗan kasuwar da ake ji dashi, ƙaton shagon atampopine dashi a babbar kasuwa, ya tamfatsa katon gida a cikin ƙauyan unguwar alƙali. Ya ja Su Sabitu ƴan uku, suke taimaka mishi a kasuwa, dan shi kullum a cikin tafiye, tafiye yake. Karima da ƙannenta mata sunyi aurensu, Karima a cikin garin Katsina tayi auren,tana zaune lafiya sumul a gidan mijinta.ƙannen nata kuma duk a ƙauyukan dake maƙwabtaka damu su kai auren. Suna gidajen aurensu cikin rufin asiri. Yaran Asiya mazan na roƙi Ɗahiru ya buɗe musu ƙaramin shagon siyar da takalma a gefen shagonshi. Tunda basu da aikin yi, ga iyalai suna dashi Asiya ranar tayi kuka bana wasa ba, ni naita rarrashinta. Rayuwa tayi mun kyau tayi haske. Ɗahiru yana daga cikin masu taimaka ma matan ƙauyanmu, da Azimi layi sosai ake ja a ƙofar gidanmu, dan Ɗahiru na raba gero da Suger. Ni kuma ina rabon kayan abinci a ƙarƙashin jam'iyyar matan arewa. Babbar matsalata shine, duk su Sabitu sunyi aure, sun hayayyafa. Amman Ɗahiru fur yaƙi yarda yayi aure, yace zai mutu yana bauta mana, musamman ni. Ranar wata juma'a muka tashi da tashin hankali, Kawu Ɗahiru ne ya fito tsakar gida tsirara, yana ihu yana fisgar gashin kanshi. "Kayanasu karka kasheni kuskure nayi, nabi Allah na bika, na bika kayanasu" Abunda yaita maimaitawa kenan. Shehu da Lauwali sunyi cirko cirko, sun rasa me zasu yi ma kawu Ɗahiru. Haka muna ji muna gani Ɗahiru ya naɗe kamar alkaki, jini ke zuba a bakinshi dalala. Zaratan yaranane suka Shigo Ɗahiru yana gaba, suna biye dashi a baya. Kamarshi sak da Shehu. "Baba lafiya meke faruwa haka? Cewar Ɗahiru kenan, yana tambayar Lauwali. Bayani yayi mishi cewar muma gani kawai muka yi yana ihu.' Ihun Ɗahiru ƙaruwa yayi, sai fisge duk wani gashin jikinshi yake yi, wajan na jini, Hannu Ɗahiru yasa ya ciske jelarsa ta fice daga jikinshi. Take ya shiga wani gurnani a take ya mutu, mutuwar tozarci da wulaƙanci, tsirara a gaban kowa da kowa. Su Tani hannu suka ɗaura aka, sukaita xunduma ihu. Ɗahiru ya ja hannuna zuwa cikin ɗakina, dan baya ƙaunar abunda zai ɓata mun rai. Zaunar dani yayi yace. "Ummi ki dena kuka, bana son ganinki a cikin ko wacce irin damuwa.Bari inyi miki albishir ko zaki ji sanyi. Dan Kawu Ɗahiru kowa yasan mushirikine, ni bazan halarci sallar gawarshi ba ma. Meye bayyiba a gidannan. Babu irin surkullen da baiyi ba a tsakar gidannan. Ajjiyar zuchiya na sauke, haƙiƙa yau zuchiyata ta tsinke, na sake girmama ƙudurar uban giji. "Ummi bana dani, dake, da Baba da Baba Asiya zamu sauke farali, zakiyi sallah a masallacin ma'aiki. Tsabar farin ciki, hawayene ya soma zuba a idanuna shatata ina godiya ga mahaliccina. Na dubeshi nace. Allah yaima rayuwarka albarka, ubangiji ya kareka, ya tsareka, Allah yaima albarka, Allah ya sada fuskokinmu a aljannatul firdausi. Amman babban farin cikina shine kayi aure wannan yaron. Shine farin cikina." Hawayenshi ya share yace. "Ummi wa kike son in aura?" Jamila yarinyar Yaya Jamila, ita nake son ka aura." Ajjiyar zuchiya ya sauke. "An gama zanyi aure, amman ku yarda ke da Baba ku tare a gidana dana gina." Nan take na amince mishi. Mutane ƙalilinne suka sallaci gawar Ɗahiru, domun gari kowa yasan Ɗahiru bokanci yake yi. Ya mutu ya bar yaranshi da abun faɗen da baza'a dena faɗeba, sai sanda duniya ta naɗe. Lokaci nayi muka ziyarci ma'aikin Allah. Muna dawowa Ɗahiru yayi aure. Kafin mu dawo Ɗahiru yasa ƙannenshi sun gyara mana waje a cikin tabkeken gidanshi, mai yalwar ɗakuna, anan muka tare, harda Asiya. Amman yaranta maza da iyalansu, suna tsohon gidanmu, da iyalan nasu, sai dai su shigo su gaishemu.Yara matan dake gaban Asiya suma sunyi aure, sabida sun tuba sun nutsu, amman sun jima basu auruba, sun garu, duniya tayi musu atishawa. Rayuwa tayi kyau tayi albarka. Ƴaƴa rahama ne. Kullum Shehu a cikin rarrashina da tarairayata yake yi. Na zama babbar mace hamshaƙiya. Yaranmu sai jikoki suke tara mana, zuriya tana ta girma tana burunƙasa.