← Book details Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 40

Sashe 33

Mata Iyayen Giji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Laila: Mai gari yaba Shehu damar yin magana. "Mai gari, wannan matsayi da ake tunanin ba Laila ta kaishi ina? Sannan ba wannan ba, Laila bata iya karatu da rubutu ba sam. Ina ganin ga Asiya a bata, dama ta saba karɓar kuke." Matar mai gari tace. "Shehu kaba baƙi damar gudanar da abinda ya kawo su, dan sauri suke yi, sannan Laila ai tana da bakin magana ko, kana tunanin ja da hukuncinane?" Gum Shehu yayi, Asiya sai mugun kallo take danƙara mun. A sannaye nace. Na iya rubutu da karatu ranki shi daɗe" Ɗaya daga cikin matan jam'iyyar matan Arewa ta miƙo mun form tace in cike ta gani." Hannuna yana kakkarwa na cike form tsab babu kuskure, na miƙa mata. Kallona tayi ta girgiza kai da taga shekaruna. Juyowa tayi tace. "Daga yau Laila ta zama shugabar matan Jam'iyyar matan Arewa na cikin wannan ƙauyen. Dukkannin wani tallafi da zai shigo ƙauyannan zai shigone ta hannunta. Zamu naɗa wacce zata taimaka mata, dama mataimakiyar mataimakiyarta. Dukkan wani abun inya taso, kona taro kona tallafi, zan turo aimun kiran Laila. Zan ajjiye foms a wajanta, duk mai sha'awar shiga wannan jam'iyyar matan Arewan, sai ya amshi fom a wajan Laila ya cike, akan kuɗi naira biyar. Sannan tunda mun buɗe jam'iyyar matan Arewa a cikin ƙauyannan, ku kuma ku dage ku burunƙasa wannan jam'iyyar, sannan ku ƙirƙiri abubbuwa da dama dan taimakon kanku da kanku. Ga kayan abinci nan, zamu raba ga mata. Bayan uwar gidan mai gari ta kuma zaɓa mana waɗanda zasu taimaki Laila." Ni dai ina tsaye sai hawayen murna nake shatatarwa ba ƙaƙƙautawa. Da Asiya da Shehu kuwa, sun cika fashewa kawai suke jira. Sha'awa aka ciro a matsayin mataimakiyata, sai Iklima amaryar mai gari a matsayin mataimakiyarta. Daga nan suka shiga yi mana rabo. Harda keken ɗinki guda biyu sababbi, da keken saƙa shima biyu. Suka wakiltani akan, in kula a koyama mata sana'a da kekunannan, kuma in sha Allah zasu kawo mana tallafin kekuna masu yawa. Suka bani foms, tare da atampar jam'iyya mai tambarin Arewa a jiki, atampar bulu, Hajiya Turai shigabar jam'iyyar matan Arewa ta Bakori ta rubuta mun adireshin gidanta, sannan ta bani izinin duk wani abun daya taso, zan iya nemanta kai tsaye" A haka taro ya watse, masu taya ni murna nayi, ƴan baƙin ciki ma sunfi yawa. Sha'awace ta taimaka mun, muka shigar da kekunan gidan mai gari, da sauran mata ƴan uwana. Dan nace a gidan zamu gabatar da koya ma mata ɗinkin. Jiki a saɓule na shiga gidan. Sha'awa kuma ta tsaya a ɗakin Zaure inda Ɗahiru yake ciki. A tsakar gida na samu Shehu ya kai mari ya kai gwauro. Ina shigowa ya tare ni. "Ashe munafukace ke Laila, yaushe kika iya rubutu da karatu, ni mijinki ban sani ba?" Wani ƙudidune ya cakeni a ƙahon zuchiyata. Yaci albarkacin Karima data fito da ƙunshin kayanta a zane. Kallona ya koma wajanta, sai naga yaran su Iyami ma duk sun fito da ƙunshin kayansu, duk yanda akayi aikatau za'a tafi dasu birni. Yaran Asiya ma suna can, wata biyu kenan har sun soma yo ma Asiya aike, waccen cin kasuwar data wuce ma harta soma yi musu tarin kayan aure. Mazajen ƙauye da damansu zuchiyarsu ta mace mus, sam basa iya rungumar ɗawainiyar ƴaƴansu, maza a turasu almajirci mata a turasu aikatau, su zasu yi ma kansu kayan ɗaki. Karima tana kuka Shehu ya tusa ƙeyarta, ni kuwa tsabaragen baƙin ciki da takaici na kasa cewa komai, yana fita ya dawo yace ƙanwar Karima ma ta fito ai shingin kaɗan ta isa aure. Ni dai waje na samu na zauna, ina kukan zuchi. Ina zaune sai ga Tani da Zainabu sun fito. Sunai ma matan gida sallama, zasu birni daga can jirginsu zai ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki. Nan gidan ya kacame da murna, Amaryar Ɗahiru kuwa tana ɗaki ta kasa fitowa, sabida ba da ita za'aje ba, ya bata haƙuri kam sai wata shekarar. Ɗahiru yana shigowa suka fita, su Baba Mai riga da matar Malam sai binsu da adda'a akeyi, kamar basu san bokanci Ɗahiru yake yi ba. Shehu ne ya shigo gidan da sauri. "Laila ba zaki yi wannan shugabancin ba, na faɗa miki kenan. Ji mata marasa kunya masu yaƙi da maza, baki isa ki haɗa tafiyarki dasu ba. Shewar dila kake yi Shehu, in kaga banyi wannan tafiyar ba, bana numfashine a doron ƙasa. Au cigaban nawa ne baka so, sai ci gaban Asiya ƴar gwal ɗinka ko? To kasani nima uwace tai silar zuwana duniya" Kasaƙe Shehu yayi yana kallona, Asiya kuwa ta taso tana huci tace. "Ki fita idanuna in rufe, dan kinsan nafi ƙarfinki tunda har na sace zuchiyar Shehu a hannunki, kuma na shigo gidan na maisheki bora." Wani irin zabura da nayi saida yasa Asiya taja baya, mari na kawo mata, ta hankaɗo Shehu gaba, ban sani ba na zabga mishi mari. Nan su Baba mai riga suka shiga sallallami, kafin kace me, ita da matar malam, da Iyami, da Laure suka rufu a kaina da duka. Da ƙyar Sha'awa da sauran mata gida suka ƙwaceni, Asiya kuma sai riƙeta Shehu yake yi, wai saita rama mishi marin da nayi mishi. Sha'awace ta jani zuwa cikin ɗakina, ganin yaran du babu yasa na fashe da sabon kuka. "Haba Laila sai kace wata ƙaramar yarinya. Kiyi haƙuri ai in sha Allah wahalarki ta kusan zuwa ƙarshe, wannan ba komai bane face baƙin ciki, ki tura musu aniyarsu. Yara ki bisu da adda'a a duk inda suke adda'arki zata isa gareki, nima da nawa yara matan aka tafi birnin, to ya zamu yi, a dake mu a hana mu kuka. Ɗahiru kuma mun tattauna dashi, Laila al'adafa yaronnan yake yi, wata uku da farawarshi yace mun. Yanzu haka na baroshi yana murƙususun ciwon mara. Ni a shawarce ki miƙe ku tafi asibitin Bakori a duba shi, shi zaifi. Amman ki jiƙa manda ki bani in kai mishi." Hannu nasa a dai dai saitin ƙirjina na dafe. Dan ji nake kamar zai tarwatse, hawaye kuwa sai wanke mun fuskata yake yi. Namiji da ƙunzugu? Tsarki Allah ya tabbata ga Allah, ɗan Adam ba a bakin komai yake ba. Jikina sai rawa yake yi, manda na jiƙa na bata ta tafi kai mishi. Tana fita Shehu ya shigo wuf. "Ke Laila baki isa kiyi wannan shugabancin ba na dai faɗa miki, gabaki ɗaya ya dawo kamar wani mahaukaci." Da tsiwa nace. In kana ganin ba zaka iya barina inyi wannan shugabancin ba, ai saika sauwaƙe mun, kaga ko babu komai na baka filin ɗakin da zaka ƙara wani auren, ka haɗata da Asiya, wala Allah ai ma naɗin sarautar Katsina baki ɗayanta, a sakamakon rabuwa da mai farar ƙafa daka yi, mahaifiyar mata maza." Tsawa ya daka mun, na kalleshi na watsar, nan yaita zazzaga ruwan jaraba, har da mun fatali da kayayyakin aikina, yasa kai ya fice, sai zage_zage yake ta faman yi. Sha'awace ta shigo ta same ni ina kuka. Dafa ni tayi tace. "Laila ki dakatar da komai, ga kuɗi bari in ranta miki, ku tafi asibiti, ciwon sai tsananta yake, yanzu haka jinine ya ɓalle mai. A gigice na fito da mayafi a kaina, banbi takan kowa ba. Sha'awace ta fito da Ɗahiru, muka ɗauki hanyar Bakori a cikin bodi. Sai yamma lis muka isa asibiti, Ɗahiru ya jiƙe wandonshi sharkab da jini, hawaye naga yana fitarwa ma. Muna shiga asibiti aka ba Ɗahiru gado, ɗan kuɗin da yake hannuna dashi na buɗe fayil, likitoci har sun zo kanshi ana duddubashi, ni dai na haɗe hannayena da kumatuna, na zuba ma sarautar Allah idanu. Bacci yake yi fuskarshi tayi fayau. Wani likita ne ya dubeni yace. "Mama ki dena damuwa in sha Allah zamu shawo kan matsalar, amman dole zamu kwantar dashi muga yanda yanayin jikin zai kaya. Amman akwai kuɗin magani da zaku biya" A baya na bisu, na biya kuɗin maganin, sannan na nufi gida a ƙagauce nayi musu bayani, sai dai kash mahaifina na samu a kwance a tsakankanin rayuwa da mutuwa, su Yaya Nazeefa da Yaya Salamatu duk an aika sun zo. "Laila Jafaru harya tafi yayo kiranki, ashe kuma kuna asibiti. Muma asibitin zamu je, dan kwananshi bakwai baya gane ma wanda yake kanshi. Duk muka yi duru_duru, a wajan mahaifina ya cika, rai yayi halinshi. Zaiyana irin tashin hankali da damuwar da muke shiga ɓata lokacine. Kan kace me aka shiga yin shelar mutuwar mahaifinmu, Inna Laraba ce ta kwana da Ɗahiru a asibiti, mu kuma muka kwana munaima mahaifinmu da yayi kwanan keso adda'a. Washe gari aka kaishi gidanshi na gaskiya, da Shehu akaita zaman makoki, babu laifi wannan karon su Asiya da matar malam sun zo. Ana cikin zaman makokinne Baba mai riga Allah yai mata rasuwa itama, sakamakon ciwon ciki na dare ɗaya. Sake ɗunguma can akayi kuma. Ni kuma na koma asibiti. "Malama Laila wannan yaron sai anyi mishi aiki dangane da lalurar dake damunshi, in ba haka ba, zai dinga yin al'ada duk wata kamar yadda ko wacce mace take yi. Sabida yanayin tsarin halittarshi, a binciken da muka gudanar mun gano ya fi ƙarfi ta ɓangaren maza, Nera dubu talatinne kuɗin aikin. In kuɗin sun samu sai ku dawo mu rubuta muku takadda zuwa babban asibitin cikin gari. Mun sallameku, ya dage yasha maganinshi dukka." Na kiɗima sosai da wannan bayanin da Likita yaimun. Godiya nayi mishi, muka bar asibitin zuwa gida, nan muka ci gaba da karɓar gaisuwar Baba mai riga. Sha'awa da Iklima su ka ci gaba da gudanar da koya ma mata saƙa da ɗinki. Ranar arba'in ɗin mahaifinmu akayi mana rabon gado. Mun tashi da gonakai da shanu, da hatsi cikin rumbu biyu,banda kuɗi tsabarshi. Munyi koke koke sosai da sosai. Ban baro Bakori ba saida na koma asibiti suka rubuta mun takaddar da in munje asibitin birni zamu nuna, sai dai sunce mun sai ƙarshen wata,ishirin ga wata zamu je. Gida na dawo, nan naci gaba da kulawa da matan da ake koyarwa sana'a. Wa'adin da aka ɗibar mana a asibiti yana cika, na ɗauki Ɗahiru muka wuce. Tare da Shehu muka je, nayi mamaki sosai da tsaiwar da Shehu yayi dangane da neman lafiyar Ɗahiru. Mun
Chapter 33 · 0% Book details