← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 59

Sashe 9

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dasauri Ilham tace "wa? Allah yasawaqe, Dida ce take sonsa,danni kona aure shi idan mamansa tamin ramawa zanyi saide yasake ni aranar, shiyasa duk family dinnan Babu Wanda nakeso, gara kowa yayi harkar sa karma mufara soyaiya kayimin fada in rama azo ana cewa nacika rashin kunya"

Dariya Diyana tayi "aini yaya fawaz yana birgeni, akwai hutu da gayu, danni duk Inda gayu yake ina nan" 🤣

Ilham ta kalleta da mamaki tace "kirasa wazakiso sai Mashayi?" 😳

Nihla tace "Ilham yayan naki kike cewa Mashayi?"

"to Nihla kowa yasan yaya fawaz mashayi ne, Dan qwaya, Dan yana yayana sainaqi fadar gaskya?shiyasa ai ake ganin laifi na ace inada rashin kunya, bayan gaskiya nafada"

Diyana tace "keni can ta matse muku, anata zancen aure aure inma Allah yakawo mazajan auren yazo haka za'ayi shi sulu, wannan tsohuwar dukta hana komai" 🤦🏻‍♀️

Dariya suka saka dukansu, suna wannan firar suna aiki ahaka suka gama suka adana komai Inda yadace sannan suka dawo falo suna kallo, Momy ce tazo tabawa Nihla key "Nihla riqe wannan key din na dakin Abba ne,nasa masu aiki sun gyara, amma kije kiduba kigani idan akwai abinda baiyiba saiki gyara" karbar key din Nihla tayi, ita kuma Momy tayi ciki

Dida tace "Allah sarki Momy, dukta hana kanta sukuni saboda Dan autanta zai dawo"

Ilham tace "ai yanzu saide yayi hakuri dan Nihla ta qwace kujerar" 🤣
Tana fadar haka tamiqe tace "natafi nayi wanka na shirya, berage awa dayaba jirginsu yasauka"

Suma su Dida da Diyana tafiya sukai domin shirya wa, ita kuma Nihla tawuce dakin da'aka nuna mata tun farkon zuwan ta gidan cewar na Abba ne, key tasaka tabude dakin, ahankali ta tura ta shiga

Qamshin Air freshner ne yadaki hancinta, ta lumshe idonta sanan tabude, shigewa tayi ciki, dakin yayi kyau komai yaji, daga kan labulen dakin har komai da Komai naciki duk launin blue ne, gadon da aka lailaye ta kalla tasaki murmushi tareda fadawa kai, juyawa tayi tana kare wa dakin kallo, anan taga pictures dinsa manya manya guda biyu, cikin sauri tatashi ta qarasa wajan photon, zuba masa ido tayi, haka yaya Abba yakoma? Photon yayi kyau sosaai, daya ya dauka da qananun kaya, sun karbi jikinsa sosai, shagala tayi da kallan pictures din tanajin wani irin dadi da batasan dalilin sa ba, gyara zamanta tayi awajan kawai tana qare masa kallo, kira Momy ta qwala mata hakan yasa tatashi Dasauri ta gyara gadon sannan tafuto

"kin gama ganin komai yayi? ''

" eh Anty komai yayi "

" to shikkenan kije kiyi wanka kishirya, su Alhaji sun tafi su dauko su"

Cikin murna tace "to Anty" sannan tayi cikin daki

Wanka tashige, tana qalqale jikinta Kamar ba gobe, ta dade tana wankan sannan tafuto

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Acan filin jirgin Aminu kano kuwa, zaratan samarin gidanne sukaje dauko 'yan'uwansu

Usman, farouq, Aliyu, Fawaz, da kuma Adam

Basu dauki lokaci wajan jiran su ba, jiriginsu yasauka
Farouq ne yafara hango su yace "yawwa gasu nan" nan yafara daga musu hannu

Gaba dayansu hankalinsu suka maida wajansu, Sunqara kyau, fatarsu ta goge, kana ganin jikinsu kasan hutu Yazauna

Suna qarasowa wajansu suka saki ihun murna duk suka rungumesu, hankalin mutane yadawo kansu gaba daya, mutanan wajan suka fara kallansu

Usman ya kallesu yace "Aliyu, yarafa sun girma, babu abinda zamu jira saide kowa yakawo matar dayake so, musha biki"

Cikin aji Abba yadubi Usman "Aure kuma yaya?"

Dasauri farouq yace "aikai banda kai, nadade da yima mata, yanzu saura Aslam da, Fawaz, dakuma Adam"

Daria Fawaz yayi, shida arayuwarsa mace ma bata gabansa, harkar qwayarsa kawai yasa agaba, yaushe zaiyi wani aure, ahankali yace "Aure, Aure tab"

Aslam ya kalleshi yace "Guy yatake ne? Kaida nayi tunanin ma kafin mudawo har anwuce wajan?"

Kafin Fawaz yabashi amsa Adam yace "kun Manta da wasiyyar kaka kenan, ba taron biki ba taron suna" 🤣

Daria suka sake sakawa gaba dayansu, Aliyu yace "tome muke jira? Muje gida kawai"

Motocin dasuka zo dasu guda biyu suka bude suka shiga, har sukaje gida suna ta surutu da raha a motar, bakin Abba nede gim baya tofa albarkacin bakinsa

Suna qarasawa gida kuwa sukaga komai ya canja, anqara gyara gidan Kamar ba gidansu ba, gaba daya 'yangidan suna tsaye a compound kowa yana jira sufuto amma banda Nihla,
Aikuwa suna futowa waje yakaure da ihun murna, Abba yana ganin Momy yaje ya rungumeta, cikin shagwaba yace "Momy i miss you"

Daria suka fara yimasa, Momy tace "gidanku Abba, bakasan ka girma bane yanzu?"

Dariya akeyi musu, Daddy yanata farinciki yayi gaba, sannan kowa yayi part dinsa cikin murna

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Hayaniyar dataji afalo ne yasa gabanta yafadi, kode har sun zo? Kafin tasamu amsar ta Tajuyo muryar yaya Usman yana cewa "Pilot, Pilot Shagwaba de tana nan "

"to waye kuma pilot?" ta tambayi kanta, kafada ta daga taci gaba da kwalliya

Gaba dayansu dining suka wuce, Daddy, Momy, Usman, Aliyu, farouq, Abba, abinci zasu faraci, Usman yace "Momy banga 'yarki ba, ko ita muke jira?"

Daddy yayi Murmushi yace "ai tunda tayi 'ya takafa mana doka agidan bazamu ci abinci ba kome take sai anjirata"

Aliyu yayi Murmushi "gaskiya ne Abba zaiyi kishi an qwace masa fadar sa"

Duk maganganun dasuke yana jinsu, Wacece suke magana akanta? Shida yadawo daga wata qasa ba'a jirashi ba sai ita, Wacece ita?

Tunanin sane ya tsaya jin Momy ta daga murya tace "Nihla! Nihla!!

Cikin zazzakar muryarta tace "na'am Anty, gani zuwa"

"Nihla" ya furta hakan cikin ransa, lokaci daya ya zubawa kofar dakin dayake tunanin daga ciki zata futo ido

Usman yazuba masa ido yanaso yagano yanayin sa, yayinda Aliyu yake murmushi

Ahankali tafuto daga cikin dakin, tana sanye da doguwar riga ta atamfa, daya daga cikin dinkin da ya Aliyu yayi mata, tayi kyau sosai acikin kayan, daurin dankwalin datayi ya baiyanar da dogon gashin kanta, dukda ta daureshi , yan madedetan Breast dinta shape dinsu yafuto sosai ta cikin breast cup din rigar

Dashi tafara tozali, numfashinta ne yakusa tsayawa cak, saboda wani irin mugun kyau daya qara, ya girma yazama Babban mutum, ga fatarsa taqara wani gogewa

Shima a nasa bangaren hakan take, idanu yazuba mata yana qare mata kallo,

Cikin ransa ya furta "tad'an girma kad'an, but still yarinya ce qarama "

"oyoyo ya Abba"

Maganar ta ce tadawo dashi daga tunanin daya tafi,
Usman yagama kallansa tsaf yasaki murmushi

Kai tsaye wajansa tanufa, taja kujerar datake gefensa ta zauna ta kalleshi dakyau
" Ya Abba sannu da zuwa, mekake cine haka, kaga yanda ka sauya kayi fari ka qara kyau kuwa?"

Murmushin kefen baki yasakar mata "kema haka"

Abinda yace kenan

Murmushi tayi "haba de ya Abba wace ni? Gashinan kana nema ka kamoni fari"

tafadi haka tana matso da hannunta me dauke da dogayen yatsu kusa da nashi hannun, Dan yagani ya ban bance

Bin farar fatar hannun nata yayi da kallo, d'an siriri dashi, Wanda yake tunanin idan yayi mata kyakykyawan riqo zai iya karya ta 😳🙆🏻‍♀️

Kafin yace mata wani abu, Daddy yayi gyaran murya ganin suna nema su Manta dasu awajan "Am yata zuba mana Abincin ko?"🤣

Tashi tayi tabude Abincin, babu kunya tafara Jan flet din gaban Abba tazuba masa, sannan tadauki na Daddy😃

farouq, Usman, da Aliyu gaba daya suka koma yan kallo awajan, Aliyu cikin ransa yace anya idan Nihla da Abba suka fara soyaiya Momy zata iya bude idonta? 🤔

Saida tagama zuba musu sanan tazuba nata Dan kadan, sannan kowa yafaraci

abinci takeci amma hankalinta yana kansa, tana kallan yanda yake cin Abincin cikeda nutsuwa, Miqewa tayi tsaye Ahankali, tadauki just din dake gaban ya Usman ta tsiyaya a glass cup sannan ta tura wa ya Abba agabansa, takoma tazauna tanaci gaba da cin abinci, Aliyu da farouq suka hada ido tareda Jinjina kai 🤣
Gaba daya Babu wata damuwa aranta take nuna masa kulawa, sai tarairayarsa take Kamar Dan qaramin Baby

Tsawon lokaci suka dauka kafin su Gama, falo suka dawo suna kallo, su Usman sai tsokanarta suke suna janta da fira, ahankali yatashi ya kalli Momy "Momy zanje nayi wanka nahuta"

"to Abba nah,"

Wani irin kallo yayiwa Nihla Wanda ni kaina nakasa fassara shi, amma tabbas za'a sami matsala idan aka yiwa mutumin daya dade yana cikin soyaiyar ka "ina Diddi? Why bakizo da itaba?"

Gaba daya falon shiru sukayi, kowa yakasa bashi amsa
Shikuma ya tsareta da Idanunsa, dago kanta tayi ta kalle shi takasa magana, karkata kansa yayi alamun yana jiran amsa yace "uhm inajin ki"

Idanunta ne suka cika da qwallah, Ahankali ta dago kanta ta dubeshi "Diddi tarasu ya Abba"

"what?"

Dasauri ya kalli Momy yace "Momy, me yarinyar nan take fada haka?"

Jijjiga kai Momy tayi, alamun da gaske ne, Lokaci daya mutuwar Diddi ta dawowa Nihla sabuwa, da gudu tatafi daki tana kuka 😭

Lokaci daya jikinsa yayi sanyi "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Diddi tarasu, Momy meyasa baku fadamin ba? Haba Momy, meyasa? Innalillah..."
Yadafe kansa da hannunsa🤦🏻‍♂️ya koma kan kujera Yazauna jagwab

Dafashi Momy tayi "kayi hakuri Abba, Aisha ta rasu Sanadin zazzabi na kwana daya, Daddynku ne yace kada afada muku, hankalin ka zai tashi, addu'ah take buqata idan kuka dawo sai kuyi mata"

"Momy yanzu Diddi tarasu?ashe ganin qarshe nayi mata?"

Su Aliyu dake zaune jiki a sanyaye, sune suka fara bashi hakuri, sannan ita kuma Momy tabi bayan Nihla daki

Zuwa dare ta ware, tadan kwantar da hankalin ta tadena kuka a dalilin nasihar Momy, tana kwance agadon dakinta tana daddana wayarta, yauma takira ya yusif yafi sau biyar amma wayar taqi shiga, ko a wanne hali yake?
ta duba Agogon dakin karfe tara da arba'in da bakwai, Dasauri ta furta "kaiiii goma saura"

Dasauri taduro daga gadon tafuto falo, kitchen tashige tafara hada coffee Mai Dan karan dadi
Momy ce taji motsinta, ta furta alhmdlh aranta, tunda tasaki ranta harta futo falo

Kitchen din ta shiga taganta tana aiki "Nihla me kike hada mana ne da wannan daren?"

"Anty bafa mu nake hadawa ba, Ya Abba nake hadawa coffee, nasan zaiji dadinsa"

ha'ba Momy ta riqe, "to Allah ya temaka, nima kallo zanyi shine naji motsinki na futo"
Tana fadar haka tajuya zuwa falo
Chapter 9 · 0% Book details