← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 59

Sashe 14

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"subhanallah, subhnllh, banida labari hajiya, Allah yakiyaye gaba,"

Tace "amin Ibrahim to sai anjima"

Shima yace mata "to hajiya Farida nagode sosai"

Wayarta takashe tana tunani aranta, anya kuwa Mai hakuri Babu abinda yake damunsa? Afada maka wannan maganar amma kace Allah yakiyaye gaba,? lalle kuwa in hakane ya tabbata Mai hakuri 🤣

Shiru yayi yariqe wayar a hannunsa, me Alhaji Abubakar yakeji da shine? Za'ayi bikin yarsa ta cikin sa amma bashida ikon da za'a kirashi Afada masa amatsayin sa na ubanta? 🤔 Wannan wanne irin iko ne?

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Zaune suke a part dinsu, shida Momy, yasaka qananun kaya, farin wandon jeans, sai riga marar hannu, yana zaune afalon suna kallo shida Momy, gaba daya tamanta dashi awajan, harkar gabanta kawai takeyi, Dan wani irin haushi takeji aqasan ranta, yana Kallanta Tun dazu take ta hada wani abu da madara, daga gani zai yi dadi sosai 🤣
Nihla ce tafuto, jikinta sanye da kayan bacci amma ta dora Babban hijabi akai,dogo ne sosai Tsawon sa har qasa, daqyar kake gano qarshan wandon jikinta saboda tsayin hijabin 🤣
Tana ganinsa afalo tayi turus, nan da nan gabanta yafara faduwa, ahankali ta qaraso cikin falon itama tazauna, tunda akai meeting dinnan sai yau taganshi

Tunda tafuto yake Kallanta, cikin ransa yake cewa kullum tana cikin hijabi, yarasa metake boye wa, yarinya qarama ta d'orawa kanta wahala 😂, kullum ka takura kanka acikin hijabi kome zata boye masa bayan yagama yimata wanka? 🤔 🤣

Ahankali ta dago kanta, karaf suka hada ido, cikin sauri yakawar da kansa gefe, Kamar ba shiba
Ajiyar zuciya tayi tace "Ya Abba ina kwana?"

Ataiqaice yace "lafiya"

Haushi yakama Momy, taso ace Nihla tayi banza dashi wallahi, domin kawar da bacin ranta yasa tadau cup din maganin tsumin data hada mata tace "Nihla ungo wannan kisha"

Dasauri ya kallesu, yayi tunanin shi zata bawa yasha ashe wannan yarinyar take hadawa? Kona menene oho musu

Dauka tayi tafara sha, abin yanada dadi Dan haka Babu musu ta shanye shi tsaf

Yana ganin ta shanye cikin ransa yace gaskiya ne, yanzu Momy bata sonsa 🤣, kowa dakowa Nihla Nihla Kamar abin sihiri 🤦🏻‍♂️

Kallanta yayi Babu ko d'ar yace mata "Am Zan'iya samun coffee?"

Ba Nihla kadai ba, hatta Momy saida tayi mamakin qarfin halin Abba
Batare da tace komai ba tatashi taje kitchen tahado takawo masa, daga nan tawuce daki, bata qara dawowa falon ba, Dan ganinsa ma zai iya qara mata wata soyaiyar tasa acikin zuciyarta

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

"umma Tun safe gashi har yamma tayi amma yaya Fawaz yana dakinsa yana bacci, saikace me baccin mutuwa"

Hajiya Abida tace "Ilham kenan, zai wuce qwaya yasha ne? Jiya idona biyu har karfe biyu Fawaz bai dawo gidaba, sai wajan biyu da kwata yadawo shima ina Tambayar sa daga ina yake yafara min magana cikin maye alamun wajan abokansa yaje suka sha tare, nasan shine yasa har yanzu bai tashi ba"

"to amma ummah meyasa yaya Fawaz bazai daina halinsa ba? Kayi ta bankawa cikinka kayan maye baka tsoro suma illa? Gashi ko sallah baiyi ba"

"Hmm Ilham ni kaina al'amarin Fawaz yana bani mamaki, kinga babanku yayi masa maganar aiki yafara zuwa office amma Fawaz yayi biris, inajin haushin yanda ake kiran dana Mashayi, Allah ya shirya minshi kawai"

"Ilham tace" amin ummah, gabana yana faduwa idan natuna da ranar bikin nan ummah "

" kiyi hakuri, insha Allah komai zaizo da sauqi, kitashi kije gidan safara'u sister na, tamin maganar gyaran jiki "

Haushi yakama Ilham, wai gyaran jiki, tarasa wa zata gyara wa jiki sai saurayin yayarta🤦🏻‍♀️

Suma su Dida haka hajiya Farida tasasu agaba tahada musu kaza kowa dai-dai,
Diyana kuwa tafi bata maganin matsi, saboda ita kanta batasan adadin mazanda yarta takula ba🙆🏻‍♀️🤣

Haka akaci gaba da hidimar biki kowanne bangaren Babu maiso, har Allah yakawo satin biki

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Rana bata qarya, ayaune aketa hada-hadar daura aure, iyaye maza kowa ka kalli fuskarsa zaka ganshi yana farin ciki, amma iyaye mata kowa da abinda ya isheta
Tun karfe goma mutane suke ta tururuwar zuwa wajan daurin auren, saboda iyayen maza sun sanar, su kuwa yaran a tsakanin su ko walima Babu Wanda yahada

Angwaye kowa yayi kyau da fararen shaddodin da Alhaji Basiru ya dinka musu, Kamar ka sacesu ka gudu

Kowa ya hallara acikin Babban masallacin unguwar domin daurin auren, liman ya gyara zama da nad'in rawanin kansa, yace "to Alhamdulillah , wanne za'a fara daurawa?"

Alhaji Baqir yabashi sunayen yaran a rubuce kowa da matar sa agaban sunansa

Adam -maryam(Diyana)
Fawaz-Khadija (Dida)
Aslam - Ilham
Abubakar - Fatima (Nihla)

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tun safe yafuto daga gida yanaso yaqaraso gidan amma matsalar go slow tasa ya makara, mutanan daya gani a masallacin unguwar ya tabbatar masa da cewa anan ake daurin auren, kai tsaye yatafi masallacin shima,
Kutsawa yake cikin dandazon jama'ar wajan har ya qarasa cikin masallacin

Adede lokacin liman yake cewa "yawwa Alhamdulillah saura na mutum daya kenan,"🤣

Ladan yace "eh saura na Abubakar da Nihla"

Qarewa mutanan wajan kallo yayi, Alhaji Baqir, Daddy, Alhaji Basiru, da Alhaji habib mijin hajiya Farida, dakuma mazan family din baki dayansu su Usman dasu Aslam Wato Angwaye

Dasauri yadaga hannu yace "A dakata!!"

Gaba daya idanu suka dawo kansa, Daddy cikin ransa yace "Mai hakuri"

Amma afili baice dashi komai ba, yazuba masa ido yana kallansa

Baba ya kalli liman yace "ala gafarta Malam, nine mahaifin Nihla, amatsayina na ubanta ban yarda adaura wannan aure ba, yarinya ta kawai nazo dauka, ita nake buqata"

Ko kallan Inda su Daddy suke baiyi ba, bare gaisuwa ta hada su, yajuyo yafice daga cikon masallacin, yanaji ta cikin Speaker anata salati 🤣🤣

Daga nan baba ya koma gidan,ya tsaya abakin get, yasa maigadi yashiga gidan yakira masa Nihla, ace inji babanta tazo

Maigadi kai tsaye yatafi part din Momy, jama'a sun taru anata hidimar biki, gaba dayansu yanmatan suna zaune a dakin Nihla, Mai kwalliya tana tsantsara mata

Diyana ce tafuto falo tana amsa wayar wani saurayinta 🤣
Maigadi yana ganinta yace "yawwa Diyana, kicewa Nihla babanta yana kiranta, yana can abakin get"

Ta amsa masa sannan ta amsa wayarta tajuya dakin tace "Nihla babanki yana bakin get, yace kije"

Yanda ta dade tana kiran wayarsa Yaqi ya amsa, tana tura masa saqo Yaqi yayi reply, hakanne yasa ta naji ance babanta tatashi tace "Baba nah!!!"

Sannan ta kalli maiyin kwalliyar tace "ina zuwa, bari naje nashigo da babana ciki"

Futowa tayi, Momy bata lura da ita ba tanata baqi
Kai tsaye Nihla tafuto bakin get din ko mayafi Babu🤣

Tana zuwa taganshi fuska Babu Rahma tace "Baba!!!"

"wuce mutafi gida" abinda yace da ita kenan

Mamaki yakamata, bata taba ganin baba cikin fishi irin wannan ba, tace "Amma baba Anty...."

"Kiwuce mutafi gida nace!!!"

Yadaka mata tsawa

Tace "To baba Babu ban dauko hijabi..."
Kafin ta qarasa yaja hannunta, suka fara tafiya, sai dankwalin da aka nad'a mata akanta ta ware tayafa a jikinta 🤣

Suna zuwa bakin titi yatare musu adedeta suka shiga, gaba daya tarasa gane kan baban nata, tashar Mota sukaje, daga nan suka wuce jigawa

Awa biyu ce ta kaisu gida, kuma har lokacin Bece da'ita uffan ba, suna zuwa kofar gida sukaci karo da motar Alhaji Isma'eeil qirar Range rover

Alhaji Isma'eeil yace "Mai hakuri ina ka shiga Tun dazu angama zuba kaya amota kai muke jira?"

Baba yace "Alhaji wallahi kano naje Tun safe, yarinya ta za'ayi wa aure batare da iznina ba, shine naje nadauko ta"

Adede lokacin yafuto daga gidansu shida mami, karaf maganar tasauka acikin kunnansa, Dasauri yakai kallansa kan yarinyar da ake magana akai
"Nihla my friend" yafadi sunan cikin ransa, fuskarta ya qarewa kallo har yanzu kyanta yana nan saima qaruwa dayayi

Cikin mamaki yakalli baba yace "Baba wai wannan yarinyar za'ayi wa aure?"

Ko a mafarki taji wannan muryar bazata taba mantawa da ita ba, kallansa tayi tafara magana cikin ranta "yaya Yusif! Innalillah.. Yaushe yadawo? 🤔

Alhaji isma'iel yayi Murmushi yace" Mai hakuri, hakuri yaqare kenan "🤣

Mami da baba sukai daria, Nihla tayi shiru, ga tashin hankalin rabuwarta da yan kano ga kuma mamakin ganin yaya Yusif

Handbag din mami ce a hannunsa, ahankali ya matsa ya wullawa Nihla jakar yace "ke riqe wannan "

Dasauri ta cafe jakar, saboda karta fadi qasa

Alhaji isma'eeil yakalli Yusif yace "nasa Mai gadi yadauko kayan Mai hakuri ansaka amota, bani key naja motar da kaina, ban yarda da driving dinka ba na ganganci, idan kuka samu titi kuna gudu Kamar bakwa son ranku" 🤣

Sumar kansa ya sosa,sannan yabashi car key din

Sai a lokacin Nihla tagaidasu, mami da Alhaji Isma'eeil suka amsa mata cikeda kulawa

Alhaji ne yabude motar yashiga, shima baba yashiga gaba, mamy da Nihla suka shiga baya, sannan shima Yusif yashiga bayan daga daya bangaren, Yazauna agefen mamy

Mamy ta kalli Nihla cikin kulawa tace "Nihla kinsha hanya sosai ko 'yata, nasan kin gaji, zoki kwanta kihuta" 🤣

Taja Nihla jikinta sannan ta dora kanta akan cinyarta tana bubbuga bayanta Kamar wata qaramar yarinya

Shikuwa Kallanta yake, Wato bazatayi masa magana bako? It means batayi missing dinsa ba,koda yake yaushe zatayi masa magana tunda ta Manta dashi harta samu wani zata Aura (tofa🤔)

Ahankali Alhaji isma'eeil yatada motar, suka dauki hanyar Abuja.

To Alhamdulillah anan na kawo qarshen labarin DANGI DAYA, zan Dakatar da typing dinsa badan komai ba saidon Comments din readers da ban gamsu dashi ba, sharhi yayi qaranci, idan akwai wadda na batawa rai Sanadin wannan labari to tayi Hakuri 🙏🏻

WhatsApp readers banida bakin dazan gode muku, kunyi min komai akan wannan littafi
masu yimin sharhi daga cikinku nayi saving number dinsu insha Allah zansakaku asabon group dina, mudinga gaisawa

Yaya labarin Mazawaje family?

Wanne hali Momy zata shiga dangane da tafiyar Nihla?

Yaya Rayuwar Nihla zata kasance a Abuja?

Ina labarin amare masu shirin shiga daka ciki?🤣

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/21, 1:40 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️

{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Chapter 14 · 0% Book details