← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 59

Sashe 19

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaja littafin ta yana gani, itama da taga yanada kokari saita fara Tambayar sa abinda bata saniba

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Yau Tun safe take shiri zataje wajan biki, wanka ta dauka taci kwalliya Kamar me, sannan ta shirya tsaf tafice batare data kalli ko Inda dakinsa yakeba, shima daya shirya yafuto zai tafi makaranta bai gantaba, kuma beyi tunanin neman Inda tatafiba, Yarufe gidan yayi tafiyar sa

Tun azahar yagama abinda yake amma saiya zauna baidawoba sai yamma, daya dawo gidanma abin mamaki bata nan, yayi shiru yana tunani, yarinyar nan tunda akai aurensu gaisuwa ma bata Hadashi da ita, ga mu'amula datake da samari awaje duk yana sane da ita, me zaiyi mata ne yaja hankalin ta ta daina abinda take?
Dariyar dayaji ne yasa yadago kansa da sauri ya kalleta, wani shegen mayafi tayafa ga kayan datasa dinkin irin dede da itan nanne, ta kalleshi taci gaba da wayarta tana cewa "ashe pictures sunyi kyau, kaima kagani ashe,"
Ta saki dariya tashige dakinta

Adam yabita da kallo, yanzu idan Diyana zata fita bekai tafada masa Inda zataje ba? Anya yarinyar nan kuwa tasan me ake nufi da aure? 🤔

Binta yayi cikin dakin tana zaune tana cire Dan kunnanta, yace" daga ina kike? "

Hankali kwance tace "daga gidan bikin wata qawata"

"ke ba'a isa da keba kenan, kindauki qyale qyalen duniya kinsa aranki, maza suna kawo miki ziyara, kinada aure akanki kina waya da wasu qartin banza, to Karki Manta de da aure na akanki, kuma duk abinda kika aikata zunubi kike kwasa akanki"

Kallansa tayi tace "zunubi?"

Takaici yakama Adam, tabbas idan yaci gaba da kula yarinyar nan, zai iya yimata dukan tsiya, kuma yasan hakan a addinance Babu kyau, cikin bacin rai yafice yayi dakinsa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Kalau yadawo gidan yau yana cikin nutsuwarsa,yana sanye da qananun kaya sunyi masa kyau sosai, kayan kallo take gogewa tadago taganshi taci gaba da abinda take, beyi mata sallama ba yaqaraso falon Yazauna yana ganin yanda take komai cikin nutsuwa, itama ko kallan Inda yake batayiba, harta gama tashige kitchen

Bayanta yabi da kallo kenan shi yarinyar nan saboda bata daukeshi a mijiba ko gaida shi ba zatayi ba bare sannu da zuwa
Ajiyar zuciya yasaki yatashi ya shige d'akinsa, Dan qaramin fridge din dakin nasa yabude yadauko magungunan maye ya ajiyesu a gefensa, Yazauna agefen gadon yabude kowanne yasha, sannan ya koma gadon ya kwanta yana lumshe idonsa

Acan kitchen kuwa Dida lemon Kankana tahada Mai dadi tahada da Abincin datayi tazuba masa sannan tafuto zata kawo masa, tana zuwa falon taga baya nan, Dan haka kai tsaye tashige dakin da Abincin

Tana zuwa gabanta yafadi ganin uban kwalaben dake gabansa shikuma gashinan Akwance yana bacci ko takalma bai cire ba

Girgiza kai tayi ta ajiye Abincin agefe ta tsugunna tadauke kwalaben, karantawa tayi, afili ta furta "Benalyn, Codein,Emzolynn, 🙆🏻‍♀️tabdi harda su Emzolynn acikin kayan mayen?"

Karaf maganar ta shiga kunnansa, a lokacin bacci yafara fizgarsa

Dida kuwa kwashe shu tayi, ta ajiye masa agefe,kafarsa takama tafara kokarin cire masa takalmin, tana cirewa ta zubawa kafarsa ido tana gani, kafar me kyau kuwa, saide Mai kafar bashida kyan hali, ahankali tatashi zatabar wajan yasa kafarsa yabigeta, lokaci daya ta'iyo kansa tafada Kirjinsa, sai jin mutum yayi akan Kirjinsa, Dasauri yabude idonsa yazuba mata ido yana Kallanta

Dida kuwa idonta yana kan bakinsa, meyasa yana shan kayan maye amma lips dinsa beyi baqi ba?

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Kasancewar yasan Babu me shigo masa daki yasa daya futo daga wanka yana daure da towel iya qugunsa yanufi cikin kayansa yadauko manyan kaya, saboda baqi dazasu gani shida Abba akan shirye shiryen bude campany nsu.
Kayan yadauko ya ajiye sannan yagama shafe shafensa yadawo zai saka kayan, gajeren wando yadauko, ya cire towel din ya wulllashi kan gado, zai saka kenan sai gata taturo kofar dakin tashigo 🙆🏻‍♀️
Tana ganinsa haka tasaki qara tafuto aguje, gabanta sai faduwa yake, Innalillahi..😳,meyakaita dakin yaya Aslam?

Shikuwa Aslam yana jin qaranta ya tabbatar yarinyar taganshi, qarasa saka wandon yayi Yazauna agefen gadon yadafe kansa 🤦🏻‍♂️, shikkenan girmansa yazube a'idon qanwar budurwarsa, zance yaqare taga komai

Haka yatashi ransa abace yagama shirya wa yafuto, tana ganinsa futowarsa takwasa aguje tayi dakinta, shikuwa Aslam ko Kallanta beyiba yawuce zai fice daga falon, ta kalli bayansa tasaka dariya, tashige dakinta

Sarai yana jinta yayi fuska ya shareta, toba dole tayi masa dariya ba, duk yanda yake kare mutuncinsa saida yarinyar nan taga komai, wallahi yanda yakeji aransa idan ta kuskura yadawo tayi masa dariya wallahi sai jikinta yayi tsami 😃

Bayan sun gama ganawa da baqin harma suntafi, sun tsaida ranar dazasu shirya bude campany, Aslam yayi shiru yana tunani, Abba ya kalleshi yace "meke damunka"

Ajiyar zuciya yayi yace "wallahi Abba akwai damuwa"

"wacce irin damuwa?"

"Abba kaga tunda akai auren nan, yarinyar nan ko abinci bata min, kullum ina wajan cin abinci, idan na yi mata magana tafadamin ba dadi"

"Aslam wannan ne dalilin dayasa nake fada muku kudena kula qananun yara, amma bakwa ganewa,"

Ajiyar zuciya yayi yace "yanzu de abinda nake fadama yarinyar nan fa taga komai, koda nayi mata fada bama lalle taji ni ba"

Abba yace "Kamar ya, mekake nufi"

Cikin haushi Aslam yace "kagane mana, saina futo fili nama bayani ne"

Dariya takama Abba, sosai yake dariya yana kallan Aslam

Aslam yace "tomiye kuma abin dariya, miye hakan, wallahi Zan huce akanka"

Abba yace "maida wuqar abokina, kaima saika rama abinda tama, kaga shikkenan kunyi 50 50, babu wanda zaiyi wa wani dariya"

Kallan Abba yayi yace "Kamar ya Abba? Ma kake nufi?"

Abba yakama Kunnan Aslam yayi masa rada
Lokaci daya sukasa dariya, Aslam yace "kai Abba wallahi bakada dama, natafi, yanzu yanzu zanje nasiyo, sai munyi waya"

Daga nan kowa yayi gida

Aslam bai zarce ko'inaba sai wani super market da ake saida kayaiyakin wasan yara, daga nan yayi gida, lokacin yamma liss, yana shiga falon yaji qamshin abinci yadaki hancinsa, ahankali yaleqa kitchen yaganta tana girki tana waqa hankali kwance, cikin sand'a yadawo da baya yashige cikin dakinta, yabude toilet dinta yadauko lizard cikin aljihunsa yasaka mata shi dede Inda yaga tana shanya panties dinta, cikin sauri yafuto Yarufe dakin Ahankali ya koma falon Yazauna yadora kafa daya kan daya yana jijjigata

Agabansa tafuto daga kitchen din, ta kalleshi tayi Murmushi, tazauna tazuba Abincin ta ita kadai tanaci tana murmushi
Kallanta yayi yasan sarai dashi take, sotake yamata magana tafada masa marar dadi, Dan haka yayi shiru yaqyaleta, suna zaune ana kallan kallo har dare yayi, bega tatashi ta shiga dakiba, shikuwa sallah yake zuwa yadawo falon Yazauna, daga qarshe ma bayan sallar ishsha'i wanka yayi yadawo falon Yazauna yana kallo, abin harya fara bata mamaki, yatsina fuska tayi tashige daki, zuciyarta daya tazage ta shiga wanka, cikin nishadi tasha wankan ta tas, ta janyo towel zata daura kenan tayi ido biyu da qadangare, tsaro ido tayi😳

Cikin faduwar gaba tace " Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, nashiga uku me yakawomin masifa cikin toilet" dagudu tafuto towel ahannu

Shikuwa yana zaune yana kallo yana shan lemo, yana jin salati yace "lokaci yayi kenan" 🤣 Ahankali yatashi yayi hanyar dakin, yana zuwa bakin qofa sukai karo, jikinta yana karkarwa ta kamashi ta riqe, cikin tsoro tace "yaya Aslam qadangare a toilet dina, wallahi yana ciki, Muje ka ganshi"

Aslam kuwa gunki yazama a tsaye, magana take masa amma yadade da shagala yana kallan surar jikinta, ashe haka yarinyar nan take?

Jijjigashi tayi tace "yaya Aslam!!!"

Firgigit yadawo cikin duniyar mu 🤪
Yanayin sa yadan sauya kadan, ya kwashe da dariya yace "to daura towel din"

Sai a lokacin talura da towel din dayake hannunta, kunya ta kamata, cikin sauri taja tarufe jikinta, amma takasa kallan idonsa 🙈

Futowa yayi yabarmata dakin, tabiyo bayansa, yana dauke kafa tana maidawa, yajuyo ya kalleta yace "wai menene?"

Cikin shagwaba tace "to Muje kacire min shi mana, haka kawai saika tafi kabarni"

Banza yayi da ita ya kashe kayan kallo yadauki wayarsa yayi hanyar dakinsa, itama ta doru abayansa 🤣

Dakinsa yashiga, yafara cire kayansa,cikin sauri tajuya masa baya, Kallanta yayi yanda tajuya bata kalleshi ba, ya zubawa cinyarta ido daga baya, yadauki jallabiya yasaka, yahau gadon ya kwanta

Tanajin ya kwanta tataho kansa ta tsaya tana share hawaye, yanajinta ya qyaleta, ita kuwa daga ta haka saita qara gunjin kuka, tsaki yayi yatashi yafuto yabar mata dakin, itama tasake futowa, cikin ransa yace yau naga ta kaina 🤣
Hanyar fita daga falon yanufa tabiyoshi, yajuyo ya kalleta "ina zakije ahaka?"

Cikin kuka tace "Allah bazaka fita kabarni ba"

Yace "abinci nakeso naje nasiyo, banaso dare yamin"

Tace "to baga abinci can a kitchen ba, basai kaje kaciba"

Cikin sauri yace "ni? A a riqe abinki, Abincin da ba'abanishi Dan dadi ba saidon wuya?"

Yana fadin haka ya juya zai fice, tasa hannu ta riqe gefen jallabiyarsa
Yuyowa yayi ya kalleta ya girgiza kai sannan yadawo falon Yazauna, itama tadawo tazauna akusa da qafafunsa 🤣

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Computer datake gabansa Yarufe ya ajiye ta agefe, sannan yadauki coffee din da Adala Sabuwar Mai aikin Momy takawo masa
Yana kai coffee din bakinsa ya runtse idonsa, zaqi yayi yawa, shikuma bayason zaqi, ga shi kansa coffee din har wani d'aci-d'aci yakeyi

Tsaki yaja, yadauko cup din yafuto falo yana kwalawa Momy kira "Momy! Momy!!"

Momy dake kallo afalo tadago idonta ta kalleshi, tace "Abba nah menene?"

Cikin damuwa yace "Momy waye yahada wannan coffee din?"

Tace "waye zai hadama coffee Abba bayan Adalaiye? "

Tamkar qaramin yaro haka yafara yimata shagwaba "Momy wallahi Babu dadi, zaqi yayi yawa, kuma ni kwata kwata ma bayamin dadi abakina Kamar yanda yarinyar nan take min, duk Babu teste"

Momy tayi shiru tana kallansa, Wato Nihla ce bazai fad'aba saide yarinyar nan,ai already Nihla tagama bata Abba da wannan shegen coffee Kamar qa'ida, Tun bayan barinta gidan komai yaci yadinga mita kenan shi Babu dadi 🤔

ajiyar zuciya tayi afili tace "Abba Tun yanzu?"

Ko'ina masu lizard zasu kwana yau? 🤔

Oga me coffee ko yaya abin zaici gaba da kasancewa🤣?

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/23, 11:31 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️

{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
Chapter 19 · 0% Book details