← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 59

Sashe 17

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk kuci gaba da bibiyata, nagode 🙏🏻

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/22, 1:47 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

19&20

Murmushi Nihla tayi "Allah sarki Anty Nadiya, nagode, bari inje an akenine"

Gidan tawuce zata shiga Nadiya tace "to ai gidanmu ne, Dan haka tare zamu shiga"

Daria sukayi gaba dayansu, sannan suka shige gidan

Nadiya ta lura yarinyar akwai abinda yake damunta, tabbas akwai damuwa a atattare da ita, amma zata jata a jikinta har taji damuwarta, Dan ita kam haka kawai taji yarinyar ta kwanta mata, Kamar qanwarta kasancewar batada qanwa mace sai namiji

Nihla tabawa maman su Nadiya takardun, cikin murmushi takarba tace idan yadawo zata bashi, daga nan Nihla tayi musu sallama tafuto, amma fafur Nadiya tahanata tafiya, qarshe ma dakinta tajata suna fira kadan kadan, Nihla ta lura Nadiya Babu ruwanta, gata da son mutane, Tun tana dari-dari da ita harta sake sukayi ta fira Kamar sun saba

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Zaune suke su uku Sunayin break fast, mamy tadubi Alhaji Isma'iel tace "Alhaji Nihla fa batada kayan sakawa sosai, sannan Babu waya ahannun ta irinta 'yanmata,kuma ace wannan kyakykyawar yartawa Babu waya Alhaji, yanzu idan tafita ta samomin siriki wacce number zata bashi?"

Yusif yana jinta, ahankali ya kalleta, yamaida hankalinsa kan Abincin dayake ci

Alhaji Isma'iel yayi Murmushi, yaga alama hajiya tanaso ta maida yarinyar tata Babbar yarinya yace"to hajiya ai ga yayanta nan, suje su siyo duk abinda takeso, idan sun kawo kinga akwai abinda babu saikiyimin magana asiyo mata "

Dadi yakama Nihla ta kalleshi tace"Nagode Dad"

"Babu godia a tsakanin mu Nihla, sannan ga albishir ki shirya zuwa next week zaki fara zuwa makaranta, saide kuma zaki bar mamynki da kewa"
Daria sukayi gaba dayansu

Suna gama cin Abincin suka tafi shopping ita dashi, suna tafiya ahanya Babu Wanda yakewa dan'uwansa magana, shi har yanzu maganar mamy ce take masa yawo a zuciya, wai saboda tabawa samari number Hmm

Ita kuma Nihla ganin Yaqi bata fuska akan maganar yasa itama tayi shiru

Har sukaje super market din ataqaice yace mata "Futo"

Babu musu kuwa tafuto, sukayi ciki

Dogayen riguna suka diba, masu shegen kyau, saida suka duba Wanda sukayi mata dai dai sannan suka dauka, inde yaga kalar riga zata karbi fatar jikinta saiya dauka yaqara musu, har mamaki yake bata
Da sukaje wajan kayan kwalliya komai Set yake dauka
Kallansa tayi "yaya Yusif sunyi yawa fa"

Yace "zaki dade kina amfani dasu"

Daga haka bata qara magana ba, suka koma wajan perfume dakuma inner wears, Kallanta yayi, yanzu kam bashida damar dazai zaba mata, yace "dauki mutafi"

Kunya ce ta kamata, haka ta matsa taba zaba, da yaga tana kunyar sa saiya kauce yabar wajan

Atamfofi kuwa sun kwashe su sosai, sannan suka tafi shagon saida wayoyi

Anan ma Kallanta yayi yace "wacce iri kikeso?"

Tace "irin tawa tada, iphone ce"

Haka nan yaji zuciyarsa tana zargin cewa mijinda zata aura ada ne yasiyamata wayar, cikin kishi yace "dole sai irinta?"

Itama da taga fuska ad'aure Babu alamun wasa sai tace "A a, ko wacce ma asiya inaso" 🤣

Babu musu yasiya mata Babbar waya Qirar Huawei

Sannan suka dawo gida da kaya niqi-niqi

Mamy suka samu afalo tana ganin su tare taji dadi, harga Allah tanason Yusif da Nihla, anan Nihla tabata kayan itama tana gani

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Cikin satin mahaifin Nadiya yanema mata admission a wata private university, Base university, yayan manya ne acikin makarantar kowa tanajin kanta ita watace, gayu kuwa ba'a magana, ko wacce mace tanaji da tata wayewar
Direban gidan zai kaita yadawo da ita, saide kawai zuwa take, amma bata gane komai, damuwar datake ciki ma ta isheta, gashi babu wanda zatai sharing damuwarta dashi bare ta cire maganar datake ranta abata shawara ko zataji dadi baba yahanata kiran kowa na kano
Ahankali sabon su da Nadiya yake qaruwa harta kai kowa yana ziyartar kowa acikinsu

Yauma bayan tadawo daga makaranta tana daki tana duba hand out, Nadiya ta kirata awaya suka gaisa sannan sukai sallama, dena karatun tayi tafuto falo, anan taga mamy tana zuba danbun nama dayawa acikin wata roba, tace "mamy wannan ina za'a kai?"

"Na yayanki ne, zai tafi dashi yanzu"

"mamy ina yaya yusif din zaije?"

Murmushi tayi, ganin yanda Nihla tayi mata Tambayar cikin sauri haka, tace "china zai tafi, akwai aikin dayake son yayi"

Jikinta ne yayi sanyi, ahankali ta karba tace "to mamy kawo nazuba masa"

Bar mata tayi, tazuba masa sannan tace "mamy bari nakai masa"
Bata jira amsar mamynba tayi hanyar dakinsa, akaro na farko Tun zuwan su gidan

Turawa tayi ta shiga dakin nasa da sallama, yana zaune yana hada kayansa acikin truly
Ya amsa mata batare daya kalli Inda takeba, zama tayi akusa dashi tace "ya Yusif gashi inji mamy"

"ajiye anan" abinda yace mata kenan

Ta ajiye masa, zuciyarta tana karyewa Kamar zatayi kuka, duk sai shamata kunu yake tunda yadawo, wai ita ya sukeso tayi ne?

Dauka yayi yasaka acikin jakar tasa sannan yatashi tsaye yace "idan kinsamu time kuje keda Nadiya abude miki account idan kina buqatar kudi saiki kirani ki fadamin, zan tafi yanzu, may be nadawo dawuri"

Yana fada mata haka bakowa ne yafado mata araiba sai ya Abba, duk alamomi sai yanzu suke nuna mata cewa dama ya Abba baya santa, itace takasa gane hakan soyaiyar sa ta rufe mata ido, duk su ya Usman Babu abinda basuyi mata lokacin data dawo kano, kowa yana nan nan da ita, amma shi ya Abba itace take nan nan dashi, 😃
Gashi shima ya Yusif yadawo amma bata bashi kulawar komai ba sai shine yake hidimta mata, batasan lokacin da hawaye yazubo mataba, ahankali ta miqe tsaye tafada jikinsa tana sakin wani irin kuka abaiyane

Qam Yusif yaqame a tsaye, shibe tureta ajikinsa ba, shikuma bai saka hannu ya rungumeta ba 🤔
Kuka take sosai har hawaye yana d'isa agaban rigarsa

Wata irin ajiyar zuciya yasaki, sannan yasaka hannu ya rungumeta gaba daya, yana bubbuga bayanta, wani irin yanayi ya tsinci kansa aciki, Wanda bai tabajin irinsa ba, cikin kasalalliyar murya yace"kiyi hakuri mana kiyi shiru, menene na kukan? Me aka miki?kokuma Wanda zaki aura kika tuna? "

Girgiza kanta tayi, tace" dan Allah kayi hakuri, kadena fishi "

Yaga alama idan akaci gaba da tsaiwa ahaka to yarinyar nan zatasa yayi mata ba daidai ba, Dan haka ya janye tadaga jikinsa, yace" ya'isa to, ni bana fishi dake, kuma kece yakamata nabawa hakuri, tunda kina ganina kika share ni, saboda kin samu wani"

Wasa tafara da yatsun hannunta tace "kayi hakuri, kuma ba kullum saina kiraka ba, amma wayar taqi shiga"
Tafadi haka cikin shagwaba

Murmushi yayi "to naji, komai yawuce, yanzu Muje ki raka yaya Yusif zai tafi kada yayi missing flight, but banda bawa samari number, kinji ko?"

Daga masa kai tayi, tace "to"

Sannan ta janyo masa jakar suka futo daga dakin, mamy bata falon, kai tsaye dakinta suka nufa domin yayi mata sallama

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Dawowar sa kenan daga makaranta duk yagaji, ga yunwa dayakeji yaji Kamar ana buga get din gidan
Tsaki yaja sannan yatashi yafita, yana budewa yaga samari su uku dukansu yarane bazasu wuce 27 ba, gaba dayansu sun tsuke cikin qananun kaya, kallansu yayi dakyau yace "samari lafiya kuwa? Ko wani gida kuke nema?"

Daya daga cikin su yace "dama munzo wajan qawarmu ne, munyi waya da ita, so tace mana tadawo nan gidan dazama"

Cikin mamaki yace "qawarku kuma? Inaga kunyi batan hanya ne, ba nan bane"

Na biyun yace "bawan Allah ya zakace mana ba nan bane, bayan nan gidan tayi mana kwatance?"

Yace "Wacece qawar taku?"

Na ukun yace "Diyana"

Tsayuwarsa ya gyara yace "Ok ai sai yanzu nagane ku, ashe wajan aminiyarku kukazo, to bismillah, kushigo mana"

Wanda yace wajan Diyana sukazo yakalli Adam dakyau, anya kuwa zai shiga? Da alama fa wannan yayan tane, karfa su shiga yamusu shegen duka 🤔

Saiya girgizakai yace "no, Barshi kawai,"

Ya kalli sauran yace "Baba kuzo mu ware kawai" 🤣

Sukuma biyun suka dage sai sun shigo, Adam yana tsaye cikin zuciyarsa yana addu'ah su shigo gidan, ysce"ku qaraso mana, tana ciki fa maryam din "

Sunfara shigowa gidan kenan sai daya yalura da yanda Adam yake tattare hannun rigarsa aboye 🤣, sai yaja dan'uwansa ya tsaya

Adam yajuyo ya gansu sun tsaya yace" me kuka tsaya yine? Rakaku zanyi "

Adede lokacin tafuto daga cikin dakinta zuwa compound din gidan, tunda aka kawota gidan yaune kawai Adam yaganta da atamfa a jikinta dinkin riga da Zani, kuma sai kayan yayi mata kyau sosai

Tana ganin mazan tasaki murmushi tace" guy's, ya garin? Yakuka tsaya daga nan? "

Murmushi sukayi, atare sukace" zamu dawo, Karki damu zamu dawo next time "daga nan suka fice da sauri

Itama tajuya cikin gidan ko kallan Adam batayi ba, shikuwa binta yayi da kallo yace" Allah ya shirye ki "

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Da yamma suna zaune afalo shida ita, kanta ko dankwali Babu dana daddana wayarta, shikuma yana can kujerar qarshe yana cike wasu takardu daya karbo awajan Abba
Tun safe rabonsa da abinci, Dan haka yana gama cike takardun yadago kansa ya kalleta
Besan meyasa yarinyar nan take san zama kai Babu dankwali ba, amatsayinsa na saurayin yayarta ai yadace ace tana shiga ta kamala, amma kullum kai Babu dankwali, wani lokacin ma shigar da zatayi idan yaganta daqyar zai dauke idonsa akanta 🙈
Badan yana ganinta amatsayin qanwar budurwar sa ba ai zata iya saka shi awani hali

Ajiyar zuciya yayi yadaga murya yanda zata jiyoshi, saboda basa zama waje daya yace "ke tashi kikawomin abinci"

Hankalinta yana kan waya tace "banajin yunwa banyi abinci ba"

Yace "Wato Ilham na lura kanki yana rawa acikin gidannan, rashin kunyar ki tafara kaini bango, Karki qureni kuma"

"to yanzu yaya Aslam girki akace nazo nayi kome? Ni wallahi bazan iyaba, saikace wata jaka"

Yace "okey Wato nida nake nemowa na kawo gidan na ajiye nine jaki, 🤣
To bari kiji Dan Allah ki yarda nasake yimiki maganar abinci acikin gidannan"

Yana fada mata haka yatashi yafice ransa abace, wannan qaddararran auren yafara isarsa, haba!

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

"A'a, yanmatan Yusif, kece atafe kenan"
Chapter 17 · 0% Book details