← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 59

Sashe 41

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusif sai Kallanta yake, kwalliyar tata tayi bala'in tafiya da imaninsa, ahankali suke ta kowa gwanin sha'awa har suka qaraso part din Momy, Nihla sai Fara'ah take, a falon suka zauna Momy tafuto suka gaisa, tayaba da Yusif din Babu laifi, cikin sakin fuska tace "yaka baro mutanan Abuja" yace "Alhamdulillah, suna lafiya wallahi"

"aaa masha Allah, ai kullum muna jin labarinka awajan Nihla"

Yusif yayi Murmushi cikin ransa yana yabon matar

Tashi tayi tace "bari akawo maka Dan ruwa, Alhaji yafita aida kun gaisa dashi "

tatafi tasa Adala takawo masa kayan motsa baki dakuma Abincin da aka shirya masa

Kallanta yayi yace "wannan ce Momy ko?"

"itace ya Yusif"

"tanada kirki gaskiya, idan naje gida saina fadawa baba cewa kina nan kalau wani kyau ma kike qarawa"

Murmushi tayi masa, tatashi tazuba masa Abincin, yafaraci, Dan kadan yaci yace ya'isa

Yakalleta yace "Nihla gaskiya bazan boye miki ba ina qaunar ki, kuma naji dadin yanda naganki hankalin ki kwance, fatana mu kasance inuwa daya amatsayin Ma'aurata nanda Dan wani lokaci qanqani"

Kallansa tayi "ina fatan hakan ya Yusif"

Fira sukaci gaba dayi har yamma tayi, yatashi yayi sallah suka dawo falon suka zauna, wayarta ce tayi ringing, cikin zolaya tace "bakada kirki yaron nan"

Daga daya bangaren akace "ninema yaron, gaskiya kin cuceni, koke aka kawomin yanzu tsaf Zan riqeki"

Dariya tayi "lalle ma Abdallah, aikuwa baza'a kawo makaba, yakake yagida, ya service"

"gida lafiya Nihla, dama nashigo kano ne shine zanzo mugaisa saina wuce"

"Ok to shikkenan abdallah saikazo, zan turoma adress din gidan yanzu"

Wayar ta katse ta kalli Yusif "ya Yusif abdallah ne yakirani, wai zaizo mugaisa"

Yace "Ok Abdallah qanin Nadiya qawarki"

"eh shi"

Yace "to saiyazo, ina pictures din birthday din naki baki turomin ba, nunamin nagani" 🙆🏻‍♀️

Hankalinta kwance tabashi wayarta tace "gashinan suna cika duba kagani"

Bude wayar yayi yashiga gallery anan yaga pictures din, lokaci daya yanayin fuskarsa ya sauya yace "ashe bake kadai kikai ba"

Jikinta ne yayi sanyi "eh nida ya Abba ne"

Tabe baki yayi yabata wayarta, sannan yatashi yace "toni Zan tafi"

Shagwaba tafara masa "haba ya Yusif, ya za'ai katafi Tun yanzu, karfe hudu nefa"

Jiyayi ta birgeshi, yace "karfe hudu nakeso nabi jirgi nakoma, bakina tareda wani masoyin nakiba, menene zaki damu?"

"saboda ina sonka, kuma kai zuciyata ta'aminda dashi shiyasa nabaka dama ka gabatar da soyaiyar mu awajan mahaifina"

Yaji dadin maganar ta, kuma ya gamsu sosai, danhaka shima ya lallabata yace bayason yayi missing flight ne, daqyar ta yarda, takira masa Momy sukai sallama sannan suka futo harabar gidan tare domin tayi masa rakiya

Awajan motarsa suka tsaya suka jingina da motar, sai kallan soyaiya suke sakarwa junansu, yabude bayan motar yabata wata leda cikeda coculate, ta karba tayi masa godia, yace "to Zan tafi, mezaki fadamin Wanda Zan dinga tunawa ina jin dadi"

Murmushi tasakar masa har dimple dinta suka futowa sosai, adede lokacin maigadi yabude wa Abba get yashigo ciki

Dasu yafara tozali, lokaci daya gabansa yayi mugun faduwa, jikinsa har rawa yake yana neman yakasa driving din, hakan yasa yafaka motar tasa a'inda bai kamata ba, waye wannan yake tareda Nihla? Wanne dan'iskanne yazo yasakata agaba ita kuma sai wani murmushi take masa?

Cikin sauri yabude motar yafuto, fuskarsa adaure, Dafarko yayi niyyar zuwa wajansu, amma saiyayi hakuri yarabu dasu yazo yawuce su ko kallan Yusif din baiyi ba

Yusif ya kalleta da mamaki "waye wannan?"

Tabe baki tayi sannan tace "ya Abba"

Nan take shima bacin rai ya wanzu a fuskarsa 🙆🏻‍♀️

Falon yashigo anan yaga kayaiyakin da'aka ajiye da alama wannan gayen aka sauka dasu, zama yayi akan kujera yadafe kansa🤦🏻‍♂️, lokaci daya idonsa yayi jajir, to zaman mema zaiyi anan? Meyasa zai zauna yanacin Baqin ciki ita kuma tanacan tareda wani? Lokaci daya wani irin kishi ya rufe masa ido, glass cup din da'aka kawowa Yusif domin shan lemo yasa qafa yayi ball dashi, lokaci daya cup din yahadu da bangon falon ya tarwatse awajan, cikin bacin rai yafuto daga falon yanufi wajan Nihla da Yusif

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Cikin kuka tace "mum wallahi Tun safe nakejin qaiqayin, Tun yanayi Dan kadan yadawo yanayi dayawa, idan nasosa ma sakeji nake"

Hajiya Farida tace "Dida, to kiyi shiru kidena kuka mana, ba komai gane sanyi ne yake damunki, kuma muddin kina dashi to shima Fawaz din zai iya samu, kina amfani da Ruwan zanyi ne?"

Tace "eh mum inayi"

Hajiya Farida tace"to ai kinji, Dida Tun kuna gida nake muku magana akan Ruwan sanyin nan, kidena tsarki da Ruwan sanyi, sannan idan kina period kwata kwata kidena shan Ruwan sanyin ma bare kiyi tsarki dashi ko wanka, kiyi shiru zansa akawo miki magani yanzu, shima Fawaz din saiki bashi yadinga sha "

Tashare hawayen ta tace" to mum, mungode "

Yana zaune agefenta yayi tagumi, yace" to yanzu kinsa itama hankalinta zai tashi, bayan nace Karki fada mata kinqi ji, tunda safe fa nakira ummah nima nafada mata, kuma tacemin zata kawo miki magani da kanta "

Zaro ido Dida tayi," nashiga uku ya Fawaz meyasa zaka fada mata, aida kunya "

Yace" keni bawata kunya, meyasa Dan muna cikin damuwa zamu kasa sanar da iyayen mu, sunefa suka haifemu Dida "

Shiru tayi masa tafara matse cinyoyinta, ya kalleta yace" qaiqayin kikeji ne? "

Ta daga masa kanta, ahankali yatashi yadawo gabanta ya tsugunna sannan yasaka hannu yadaga yar qaramar rigar dake jikinta bejira komai ba yatura hannunsa ciki 🙈

Cikin nutsuwa yafara sosa nata wajan yana Kallanta, yanayin sa ne yafara sauyawa cikin shaqaqqiyar murya yace "yana raguwa qaiqayin?"

Idanunta a lumshe tadaga masa kai, yasaka hannu yasake bude kafarta yaci gaba da sosa mata,daga susa sai aka zarce abinda yafi yafi susa, gaba dayansu sunyi shiru kowa da abinda yakeji

Sallamar da sukaji ana doka wa ne yasa suka dawo hayyacinsu, ahankali yatashi duk hankalinsa yatashi, yace "ga ummah nan," sannan yashige cikin daki

Hajiya Abida Maman Fawaz tashigo falon tace "Sannu Dida, ke kadai ce agidan ne?"

Cikin kunya tace "a a umma ya Fawaz din yana daki"

Zama tayi akan kujera ta cire mayafin ta tashiga kitchen din didan da kanta, tafuto da wani itace daga leda ta wanke shi sannan tasaka tafarnuwa aciki tazuba a tukunya tadafa mata shi

Saida ya dahu ta debo a cup takawo mata tace "karbi wannan kisha"

Adede lokacin Fawaz yafuto daga daki bayan yagama dedeta kansa 🤣

Hajiya Abida tace "Sassaqen Zogale ne wannan, shi zaku dinga sha dagake har shi, ga sauran can a kitchen nabar muku, kudinga sha kuna tsarki dashi, ina tabbatar miki koda sanyi Hajiya Farida ta haifeki to insha Allah saiya barki" 🤣

Dida da Fawaz sukai murmushi gaba dayansu, sannan hajiya Abida tayi musu sallama tatafi

(Yar'uwa kisamu Sassaqen Zogale, ina nufin jijiyar Zogale, za'a saro miki shi daga jikin bishiyar Zogalen, saiki qara daddatsa shi yayi Dan dede misali kisa shi a tukunya kidafa da tafarnuwa, kokuma kidafa da jar kanwa, idan ya dahu saiki dinga sha safe, rana, dare, daga lokacin zakiyi hannun riga keda cutar sanyi, Allah yasa anfahimta 🙏🏻)

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Hannunsa zube cikin aljihun wandonsa jeans Mai launin fari yaqaraso wajansu fuska daure, kana kallansa zaka hango tsananin kishi afuskar sa
Kallan Yusif yayi yace "Sannu ko"

Ya Yusif shima da kishi Yarufe masa ido yace "Sannu fa"

Kallan Nihla yayi "ina jiranki kizo Muje ki hada min abinci"

Kallan mamaki tabishi dashi, da'ita ce take hada masa abinci? Tace "abinci kuma?"

"eh abinci, kokuma da kaina zanje nahada? Bayan kinsan ban'iyaba?"

Tace "Abincin...." cikin sauri ya Yusif ya tare ta, ta hanyar daga mata hannu
Ya kalleshi yace "Abba ko?"

Fuskarsa Babu alamun wasa yace "Yeah"

Ya Yusif yace "kanata kishi kana bacin rai saboda kawai muna tare, to bakaga tana tareda mijin da zata aura bane?"

Haushi yaqara kama Abba, baice masa komai ba yakalli Nihla yace "banda lokacin batawa anan, zaki wuce mutafi kokuma saina daukeki nashiga dake?" 🙆🏻‍♀️

Cikin fishi Yusif yace "karka kuskura kafara tabamin mata, idan tana yarinya ka tureta narabu dakai to yanzu ko Dan yatsanta ka taba ranmu ne zai baci gaba daya"

(Lol dama kunsa ba 🤪)

Abba ya kalleshi, sai yanzu yagane komai, sai yanzu yagane shine meyi masa shishshigi akan qanwarsa Tun tana qarama, kuma shine silar dayasa yayi fishi da'ita kafin subaro qauyen na jigawa, meyasa har zuwa yanzu yake masa katsalandan acikin rayuwarsa ne? 🤦🏻‍♂️

Cikin fishi yakai Hannu zai fuzgota shima Yusif cikin sauri yasa hannu zai tareta, Nihla tana ganin ikon Allah tace "nashiga uku, ya Yusif Dan Allah kayi hakuri karabu dashi banaso kokadan ranka yabaci akansa, Muje kada kayi missing fligh"

Yusif yace "shikkenan my dear, idan nasauka Zan gaida su baba"

Abba jin tace Yusif yasake kallan gayen, ashe shi nede yake kiranta awaya, kuma shine Wanda ya aiko mata da gift daga Abuja, damuwa tataru tayi masa yawa

Adede wannan lokacin shima yaqaraso wajansu, Tun daga nesa ya gansu a tsaye cirko cirko da alama ba kalau ba, yana zuwa kuwa yayi musu sallama, Nihla da Yusif suka saki ransu, shikuwa Abba mamaki yake meya kawo Abdallah gidansu? "

Fuskantarsa yayi yace" kai meya kawoka gidannan? Mekazoyi? Mayaudaran banza Mayaudaran wofi, kafice kabar gidannan yanzu yanzu "

Nihla tarasa yanda zatayi, tace" Abdallah Dan Allah kayi hakuri "

Abdallah yace " Babu komai Nihla, sai munyi waya "

Yayiwa Yusif sallama ya juya yatafi ransa fal da tunani me yakawo Nihla gidansu ya Abba saurayin Anty Nadiya? Dama Ta sanshi ne?

Shima Yusif yayi mata sallama yatafi, Abba kuwa Be qara cemasa komai ba saima hanya daya nuna masa

Nihla ta kalleshi," haba ya Abba, meyasa kake min hakane? Sainayi baqi zakazo ka tozartani agabansu, me kake nufi danine? "

bata jira amsarsa ba tawuce tayi part dinsu cikin fishi

Wato duk abinda yake Tsawon wannan lokacin batasan ma meyake nufi ba, tunda gashi tana tambaya meyake nufi da'ita, bin bayanta yayi yace "dakata"

Tayi banza ta qyaleshi taci gaba da tafiya

"ki dakata nace"

Nanma tayi shiru ta qyaleshi harta qarasa cikin falon, sannan Tajuyo ta kalleshi cikin fishi, bacin raine yasa batasan lokacin data daga muryarta ba, takalleshi tace " inajin ka"
Chapter 41 · 0% Book details