← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 59

Sashe 25

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" kai ummah tanada damuwa wallahi, menene kuma na ambatar mutuwa? "cewar Fawaz, daga nan yatashi yashige toilet yayi wanka, tsaf ya shirya cikin qananun kaya, yafuto falon, ganin dakin Dida arufe yasa bai shigaba, yasan tana bacci itama

Kai tsaye Mota yashiga yakira wayar Ilham din tafada masa a asbitin dasuke, sannan ya kashe wayar yaci gaba da driving

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Zaune take agefen gadon akan kujera dede setin Inda kansa yake, Dan qaramin handkerchief ne a hanunta data jiqashi da ruwa tana goge masa kansa dashi, saboda taji kan nasa akwai zafi

Fawaz ne yashigo dakin shida wata nus datayi masa jagora, yana ganin halin da Aslam yake ciki jikinsa yayi sanyi, wannan hannu duk an nad'e masa shi, ga qananun ciwuka, tashi Ilham tayi tabashi kujerar Yazauna, anan yake tambayarta yamai jiki

Shiru sukayi na wani lokaci, Fawaz de jiki yayi sanyi, cikin ransa yake magana tabbas dan'adam ba abakin komai yakeba, kaduba kaga de halinsa Aslam yake ciki rai ahannun Allah shida bayama shan ko wacce irin qwaya, Allah ya jarabceshi da wannan qaddarar, to idan shine dayake aikata wannan mugun halin yaya nasa abin zai kasance kenan? 🤔
Tabbas dole ne yayiwa kansa fada ya shiryu Kamar sauran yan'uwansa, insha Allah yayi alqawarin daga yau yaraba hanya da kayan maye.
Jiki a sanyaye yayi mata sallama yatafi gida

Shiru Ilham tayi tana kallan Aslam, ita sai yanzu ne take ganin mugun kyansa, ya Aslam ya hadu ba qarya, amma da qiyaiya tahanata gani,Allah sarki, ko yaushe zai farka?.
Ahankali yafara bude idonsa, yasaukesu akanta, rufe idonsa yayi yana tunani nan take hatsarin dayayi yadawo masa cikin qwaqwalwar sa, bude idon yayi yaga tabbas Ilham yake gani a gefensa, meyasa tazo Inda yake? Ai yayi tunanin zatafi kowa murna
Farinciki ya rufe Ilham, cikin murna tace "Alhamdulillah, ya Aslam katashi? Sannu ya Aslam bari nakira Doc."

Cikin sauri tafice daga dakin yabi bayanta da kallo, menene ya sauya yarinyar nan haka lokaci daya?

Doc. ne yashigo dakin ya duddubashi tareda yimasa yan tambayoyi sannan yace yaci gaba da shan magunguna zuwa jibi za'a warware masa hannun nasa, sannan yafita

Ilham kuwa sai murna take bakinta Yaqi rufuwa, kujerar datake kai takoma ta zauna, ta dora hannunta akan goshinsa tace "ya Aslam sannu, ahadama Tea kasha ko?"

Dayan hannunsa da Babu ciwo yasa yakawar hannunta dake kansa yace "kidena tabani banaso, ai shikkenan tunda hankalinki ya kwanta, ba haka kike so kiganni ba"

Wani irin kuka ne yazo mata maicin rai, batasan lokacin data fada kansa ta rungumeshi ba, tana kuka, hawayenta yana d'isa agefen wuyansa, cikin kukan tace "ya Aslam Dan Allah kayi hakuri Allah nadena"

Aslam kuwa baisan lokacin daya lumshe idonsa ba jin nashanunta masu laushi akan qirjinsa, dama gwadat yake yaga tadena rashin kunyar kokuma de tarkonsa yakama shima tafara sonsa🤪

Adede lokacin Adam yashigo dakin, hannunsa dauke da ledojin fruits, murna yafara ganin idon dan'uwansa biyu yaude yafarka, adaya bangaren kuma kunya ce ta kamashi ganin yanda Ilham ta rungumeshi tana wani kuka qasa-qasa 🤣

Aslam yace "Adam sannu da zuwa"
Ya kalli Ilham dako niyyar tashi batayi yayi qasa da murya yace "qanina fa yashigo, zakisa ya renani" 🤣

Ahankali tatashi tana goge hawayen idonta tace" ya Adam sannu da zuwa, ina wunin "

Adam yayi ajiyar zuciya yace" lafiya Ilham, ashe maigida ya miqe "

Murmushi tayi masa kawai, takama hannun Aslam din tariqe Kamar wani zai qwace mata shi.
Hajiya Na'ila ce tashigo dakin Diyana tana gefenta da abinci a hannunta

Da Adam tafara tozali acikin dakin, yana sanye da qananun kaya, saiyayi mata mugun kyau, ahankali tasauke idonta kasa, shikuwa Kallanta yake yana magana cikin ransa, Wato maryam dayace taje gida saiya nemeta wajansa mahaifiyarsa tatafi kenan 🤣, dama ai matsalar ka auri wadda kuke DANGI 'DAYA da'ita kenan, yanzu Inda bare ya aura ko hanyar gidansu bazata nemaba, Dan Allah kalli wannan shegen kayan data saka duk ya kamata hips dinta awaje, kuma mama tana gani shine suka futo ahaka

Cikin nutsuwa Diyana tace "ya Aslam ya jiki?"

Yace "jiki Dasauqi Diyana"

Ta kalli Adam dinma tace "ya Adam ina wuni ya aiki" 🤣

Shiru Adam yayi be amsa mata ba, haushi yakamata, Hmm zata rama ne

Hajiya Na'ila tace "kema de dabata yawun bakinki kike, kina gaidashi yana wani hura hanci, ajiye musu Abincin mutafi gida" 🤣

Diyana ta ajiye Abincin tafice daga dakin, hajiya ta kalli Adam tace "kasan abinda ka aikata ai, shiyasa idan na nemeka baka dagaba, to kazo gida ka sameni ina nemanka" tana fadar haka tafice daga dakin

Aslam yace "Adam kayi hakuri, kasan sha'anin mata sai Ahankali, dole sai kakai zuciyarka nesa, da niyya ma zasu dinga qin yiwa mutum biyaiya kasan... Su"

Maganar sace ta katse saboda mintsininsa da Ilham tayi ahannu🤣

Adam yayi Murmushi, shikam sun birgeshi, inama maryam zatazo ta koyi yanda ake kula da miji anan, yace "to insha Allah, nizan tafi, sai gobe idan Allah yakaimu"

Aslam yace "to shikkenan kakira Abba kafada masa natashi please"

Yace "okey"

Daga nan yaja musu kofar, Ilham tayi masa hararar wasa cikin shagwaba tace "shine zakake fada masa laifi na ko?"

Murmushi yayi yana Kallanta Kamar ba'itaba, Kamar an sauya masa qanwar budurwarsa🤣
Yace "ya jikinki? Yanzu de Babu kuka kin warke sosai ko?"

Kunya takama Ilham, tasa hannu ta rufe idonta tace "dan Allah ya Aslam katashi Muje kayi wanka" 🙈

Murmushi yayi, sannan yafara kokarin tashi, yana jin dayan hannun yana masa ciwon kadan-kadan

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Jikinsa a sanyaye yadawo gida yana tunanin mutuwa, kai tsaye dakinsa yawuce yabude kayansa duk wata qwaya datake ciki saida ya dauko ta, nacikin fridge ma yadauko su yazuba acikin wani kwali yanufi dakin Dida dasu, yanaso ya tabbatar mata cewa yau yadena shan komai, yanaso yafara tabbatar wa matar sa cewa daga yau Babu me sake kiransa da Mashayi
Amma me, yana bude dakin yaga bata nan, qarasa shiga yayi yaga kofar toilet dinta abude, afili yace "a a, to ina yarinyar nan tatafi ne? Nasan duk Inda zataje tana tambayata ai"

Cikin sauri yafuto yadawo kitchen bata nan, yaduba compound bata nan, kwalin dake hannunsa yasaki yafadi qasa, yasake komawa cikin gidan da gudu, karon farko daya fara ambatar sunanta "Dida! Dida!! Dida!!!, ina kike ne?"

Wasa-wasa saida Fawaz yagama duba gidan tas yaga bata nan, Kamar mahaukaci haka ya koma dakinta ya kalli Inda akwatunanta suke yaga sunragu, anya kuwa Dida ba guduwa tayi tabarshi ba? Kode taganshi ne dazu bayan yasha maganin mayen nan? Tabbas yarinyar nan taganshi, awajan ya sulale yazube akan gwiwar sa tareda dafe kansa 🤦🏻‍♂️, ya zata masa haka?

Dasauri yatashi yafuto daga dakin yashige motarsa bai zarce ko'inaba sai gida

Kai tsaye part dinsu yatafi, hajiya Abida tana zaune tana kallo sai ganinsa tayi yashigo Kamar mahaukaci

Tace "subhanallah Fawaz lafiya?"

Yana daga tsaye yace "umma Dida batazo nan ba?"

Tace "Dida kuma? Aini rabona da Dida Tun bikinku Fawaz, kai baka taba hankalin dauko ta ka kawomin ita ko wuni ne muyi ba, itama batazo ba"

Gabansa ne yafadi, Yazauna aqasa kafet din falon jagwab, Idanunsa suka kada sukai jajir yace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un , Umma Dida tagudu tabarni" sai kuka 😭

Gaban hajiya Abida yafadi tace "kaini banason sakarci, yanzu Inda qannanka suna nanma haka zaka zauna kanamin kuka, kayi min bayani dalla-dalla meyake faruwa?"

Cikin kuka yace "umma...gani...ganina..tayi nasha wani magani shine... Shine...tagudu"

Tace "ahaf, ni nasan da walakin goro amiya, haba Fawaz, yarinyar nanfa tana kokari, aure kusan shekara biyu amma bata taba kawomin kararka ba, lokacin da akace anhadaka da'ita yarinyar nan ko uhm batace ba, duk family dinnan kowa yasan anfi qwararta akan sauran 'yan'uwanta, ai kai kamata yayi ma ace kayiwa yarinyar nan gata samada kowa acikin gidannan, kayi mata abinda takeso ka fifitata saboda ta rufama Asiri ta zauna dakai, yanzu ma dakace akan kasha wani magani tagudu bawani magani dazaka sha Fawaz bayan na maye "

Cikin kuka Fawaz yace" to umma kuma saita gudu tabarni "

Tace" a a, bamu bincikaba ba zamuce tagudu ba, tashi Muje wajan maigadi muji ko yaga shigowar ta gidan "

Tashi yayi yana goge hawaye yabi bayanta, suna zuwa wajan maigadi ya tabbatar musu da cewa tabbas yaga Dida Tun rana tashigo gidan, shine ma yabude mata get

Hajiya Abida tayi masa godia takoma part dinta, ta nemi kujera zata zauna kenan Fawaz yasa hannu yariqe rigarta yace "Ummah matata" 😭

Qwace rigarta tayi tazauna tace "tome Zan maka Fawaz? Bakaji da bakinka ance tazo gidaba? Ai kasan hanyar part dinsu"

Zama yayi agefen qafafunta yana kuka Kamar mace yace "Ummah Allah nide adawomin da matata, ya za'ai naje part dinsu bayan nasan mamanta bata sona" 🤣

Hajiya Abida tace "kaga Fawaz karufe min baki, ya zakazo kasani agaba kanamin kuka? Lokacin daka mata laifin kayi shawara Dani? To bari kaji, tunda akai auren ku har yau Babu Wanda yace uffan akan zaman aurenku, Dan haka ba zanje part din hajiya Farida tafadamin magana inqyale taba, wallahi saide kaje"

Bece da'ita komai ba, yatashi yafice daga part din, yayi nasu Dida, hankalin sa kwance yatura kofar falon, a lokacin kuwa Dida tana zaune itada Hajiya Farida suna kallo, kallo daya tayi masa tadauke kanta, cikin ransa yace tana nan kenan

Hajiya Farida tace "a a Fawaz kaine atafe, sannu da zuwa, shigo ka zauna"

Fawaz yanemi waje Yazauna yana mamakin yanda ta karbe shi hannu biyu, sai sunkuyarda kansa yake qasa dan karsu gano yasha kuka 🤣

Hajiya Farida ta miqe tsaye tace "Dida kawo masa ruwa mana" daga nan tayi cikin dakinta tabarsu su biyu, cikin ranta tace tasan bazai wuce biko Fawaz yazo ba, ita kuwa bada itaba, yaje su qarata atsakaninsu, tunda taga Dida tadawo gida tasan cewa qarshe yakai yarinyar shiyasa tayi fishi tataho gida, to ba zatayi mata dole akan takoma gidansa ba, Dan daga nanma zata iyayin wani gidan su nemeta su rasa, gara yanda tazo da qafarta, takoma da qafarta, amma bazata bakinta a sabgar yara ba

Daga kan kujerar yasauko yadawo kusa da ita har tanajin yanda numfashinshi yake sauka akan fuskarta yace "Dida"
Chapter 25 · 0% Book details