← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 59

Sashe 40

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayi tunanin dazu da farouq yace pictures dinta suna wayarsa zatace yatura mata, amma sai yaji tayi shiru, yarasa me zaiyi mata tadinga sakewa dashi suna magana Kamar da

Zuwansu wajan ne yakatse masa tunanin dayake, Nihla ta kalleshi yana sanye da jallabiya fara qal wadda ta karbi jikinsa, sumar kansa ta kwanta luf tana sheqi gwanin sha'awa, hankalin sa yanakan waya

Zama sukai, Momy tace "Nihla zuba mana Abincin"

Tashi tayi tafara zuba musu, ahankali ya ajiye wayarsa yazuba mata ido yana Kallanta, rigar jikinnata tayi mata kyau,wadda ta kasance marar hannu,kyakykyawar fatarta ya kalla tayi luwai luwai da'alama zatayi laushi

Momy ta kalleshi taga ya zubawa Nihla ido, duk abinda take akan idonsa, tunani tafara to kode Abba ya Manta tana wajan ne yakebin 'yarta da wannan mayen kallon? 🤔
ahankali ta dauke kanta

Nihla tazuba wa kowa sannan tazauna kowa yafara cin Abincin
Suna tsaka dacin Abincin yadubeta yace "please inason Tea"

Dago daradaran idanunta tayi ta kalleshi batare da tace komai ba tatashi ta janyo flaks din dake gabansa tadauki cup tazuba suger kadan sannan tasaka madara

Momy ta kalleta, gaskiya ne Nihla ta karanci Abba tas, Inda wanine zai hada masa Tea dinnan da tuni yayi magana yace kar asaka suger dayawa, amma ita ko magana baiyi mata ba saboda yasan tasani

Ruwan zafin tafara tsiyayowa by mistek hannunta yazame Ruwan zafin yazubo ahannunta

Flask din ta ajiye dasauri tace "auch..." tafara yarfe hannunta tana runtse idonta

Spoon din hannunsa yasaki yatashi dasauri ya nufeta, yanda take girgiza hannun ne yasa qirjinta suke rawa Wanda batasaka musu ko 'yar breziya ba, numfashin sane yafara kokarin daukewa, badan tana cikin jin azabar zafi ba da Babu abinda zai hanata ganoshi, jiyake Kamar ya fuzgota jikinsa
Ahankali yadora hannunsa akan nata yariqe hannun data qone din, gaba daya damuwa ta baiyana a fuskarsa, hannun yakai bakinsa yafara hura mata iska awajan,runtse idonta tayi yace "wayyo Momy hannu na"

Kallanta yayi yaga idonta yacika da qwallah, yace "Sannu, kidena kuka"

Hannun yakalla dogayen yatsunta masu kyau sunyi jajir, yasake hura mata iska awajan

Cikin shagwaba tace "wash!"

Dago kansa yayi yazuba mata manyan idonsa, rakinta yana birgeshi, haka yatsira mata ido yana Kallanta ga hannunta yariqe cikin nasa

Momy tadena cin Abincin ta tsaya tana kallan ikon Allah 😱, kode sun Manta tana wajan ne? Lalle wannan Inda ace Nihla tana sonsa Kamar yanda yake sonta a yanzu, Toda Babu abinda zai hana su hanata zaman gidan mijinta, irin wannan rashin kunya a gabanta har ina!🤦🏻‍♀️Ita Nihla yanda take shagwabar saika rantse da Allah da niyya takeyi, shikuma gaba daya ya susuce akanta yasakata agaba Kamar zai maida ta cikin jikinsa

Gyaran murya tayi, Abba yajuyo ya kalleta batare daya cika hannun Nihlan ba, itama sai a lokacin tabude idonta ta kalli Momy

Momy tace "jeki saka qanqara akan hannun, zakiji yadena zafi, Allah yasawaqe"

Cikin sauri yace "bari a dauko"

Yasake kallan Nihla yace "Sannu" sannan yasaki hannun nata yawuce kitchen batare daya jira ta amsa masaba
Tausayinsa yad'an kama Momy yanda taga gaba daya ya rikice, to idan yaji akwai wanda Nihla take tare dashi yaya zaiyi kenan?

Tana tsaye sai turo baki take gaba yadauko qanqarar yadora mata ahannun sannan ta danji dama dama

Suka zauna kowa yayi shiru, Momy tadubeshi, taga ko kallan Tea din beyiba, magana tafara aranta, yasa yarinya tahada masa abu, a dalilin haka ta qone amma baima kula Tea dinba, tace "Abba kasha Tea din mana"

Bece da'ita komai ba, kawai de ya girgiza kansa 🤣

Ajiyar zuciya tayi tace "nikam na qoshi, saida safen ku,"

Ta kalli Nihla tace "idan hannun be daina zafi ba koda cikin dare ne kizo ki fadamin saina tasoshi yakaiki asibiti"

Abba yayi Dan qaramin murmushi saboda yasan sarai dashi take

Wajan yarage saisu biyu kawai,kowa yayi shiru Babu me magana, ta dago ta kalleshi ta kawar da kanta, shikam, zuba mata idanu yayi, wani irin dadi yakeji cikin ransa, besan cewa ya takura taba, dazai matsa da tafi cin Abincin yanda ya kamata, tunda shi baci zaiyi ba

Bata tsammata ba taji yace "kek yayi dadi"

Ahankali batare data kalleshi ba tace "thank you"

Daga nan tayi shiru, tana tunanin maganar Momy da tace idan yadawo tayi masa godia akan motar daya bata, tarasa tayaya zata gode masa, kwata kwata ma batasan tuno da maganar motar, saboda wannan takardar daya hado mata da'ita tarasa gane Inda yadosa, shi ya Yusif dasuke soyaiya tayi masa godia yanda ya kamata amma shifa ya Abba?

Ahankali tadago kanta ta kalleshi, karaf idonsu yahadu, tayi saurin janye nata idon tace "nima... Nagode sosai"

Murmushin yayi, zaiso ace taci gaba da magana saboda yana jin dadin yanda Dan qaramin lips dinta suke motsawa dan haka yace "for what?"

Kai tsaye tace "motar daka turomin"

Memakon yayi mata maganar motar saiya jefo mata tambaya "Can you drive?"

Tace " i can't, but yaya farouq saiya koyamin"

Shiru yayi na Tsawon mintuna, farouq, farouq, karfa tasa yafara kishi da yan'uwansa, ya kalleta yace"dole sai shi?"

Amnah El Yaqoub ✍️
[7/7, 11:07 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

43&44

Kanta tsaye tace "ehmana"

Fuskarsa ta nuna alamun damuwa yace "no, kibarshi, zan koya miki"

Kallansa tayi, lalle ya Abba yasakko, ahankali tace "nagode, amma kabarshi"

Tsam ta miqe daga wajan, Dan taga alamun zancen yakeso, kawai yazo yasa ta agaba, hanyar dakinta tanufa batare data qara masa magana ba, shima binta yayi da kallo, saida yaga tashige dakinta sannan yasaki ajiyar zuciya

Shima dakinsa yatafi ya kwanta, tunani yafara akan tayaya zai shawo kanta? Har tausayin kansa yakeji wani lokacin, tana bashi irin wannan amsar tayaya zaiji qwarin gwiwar fada mata abinda yake ransa?

Har qarfe biyu da rabi yakasa bacci yana tunanin ta, yaji haushin kansa yafi a qirga, Inda ya amince da'ita Tun farko daduk haka bata faruba, ganin tunanin Babu Inda zai kaishi yasa yatashi yanufi toilet yadauro alwala yazo yafara fadawa Allah kukansa

Bayan ya idar ya kashe wutar dakin ya kwanta, bai taba barin wayarsa akunne ba idan zaiyi bacci, koda yaushe kashe ta yake idan zai kwanta, amma yau akunne yabarta, rigar jikinsa yazare dagashi sai boxer yaja fillo ya rungume a qirjinsa sannan yadau wayarsa yana kallan pictures dinta, ahaka bacci ya daukeshi.

Dadewar dayayi beyi bacci bane yasa daya koma bacci bayan sallar asuba, yajima yanayi, bai tashi ba sai wajan shadaya

Wanka yayi yafuto domin ya gaida Momy,ganin su yayi gaba dayansu zaune afalo,ga Daddy ga Momy ga kuma Nihla agefen Daddy tana sanye da Jan leshi Wanda akayi mata dinkin riga da siket amma wuyan rigar irin budaddan nan ne da'ake yi yanzu

Cikin murna ya qaraso Yazauna ya gaida Daddy da Momy

Itama Nihla fuskarta Babu yabo Babu fallasa ta gaida shi ya amsa cikeda kulawa

Daddy yace "Tun karfe takwas nadawo momyn ku tace baka tashiba"

"eh Daddy, ban kwanta da wuri bane shiyasa"

"to Alhmdlh, kuma bana nan sai qanwar ka tazo service harma kasiya mata Mota"

Shiru yayi Bece komai ba
Daddy yace "to Allah yasaka da alkhaairi, Allah yabar zumunci" 🤣

Ahankali yace "Amin"

Tashi Daddy yayi yakalli Momy yace "idan yagama break fast ki turomin shi"

Momy tace "to Alhaji"

Bayan yagama cin Abincin kuwa Momy ta turashi dakin Daddy, sannan itama tabi bayansa, Nihla kuwa kwanciya tayi tana daukan remote

Zaune yake agabansu kansa aqasa, yarasa dalilin wannan kira, Daddy yadubeshi yace "Abubakar Momynka ta sanar Dani rashin lafiyar dakayi kwanaki harma da abinda likita yace"

Abba najin haka cikin ransa yace Innalillah.., yayi shiru Kamar ruwa ya cinye shi

Daddy yaci gaba da fadin "nadade inama kallan marar lafiya ashe ba haka bane kalau kake tunda gashi har kana rashin lafiya akan haka, ina ita yarinyar dakace kanaso din take, inane gidansu sai Muje ayi magana guda daya, ka dade da sanar damu cewa kana sonta, amma maganar aure kayi shiru"

Shiru Abba yayi, idonsa yayi jajir, ga kunyar iyayen nasa dayakeji Ahankali yace "Daddy tayi aure"

Cikin sauri iyayen suka kalleshi, Daddy "to shikkenan Allah yakiyaye gaba, sai kayi kokari kasamo wata ka aura, bazai iyu kaci gaba da zama da rashin lafiya ba"

Jinjina kansa yayi yace "insha Allah Daddy"

"zaka iya tafiya"

Ahankali yatashi yafuto daga dakin, ta gabanta yazo yawuce yashige dakinsa, itade Nihla taga shigar sa daki Kamar yana cikin damuwa, tabe baki tayi taci gaba da kallonta

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Bayan sati daya tana kwance tana bacci da weekend kasancewar bazata ko'inaba
Wayarta ce tahau ruri cikin magagin bacci takai hannu tadauki wayar cikin sexy voice tace "Hello"

"Baby na kina bacci kenan"

Tace "Um"

Murmushi yayi "to albishirinki"

"goro ya Yusif"

"yau ina kan hanyar zuwa naganki, aide adress din dakika taba turomin kina nan ko?"

Bude idonta tayi "ya Yusif da gaske kake zakazo?"

"Yes, yau zanzo insha Allah, yanzu hakama wanka zanyi nabiyo jirgin dazai tashi 12"

"wayyo ya yusif, mekakeso na shirya ma?"

"Karki wahalar min da kanki, kiyi zaman ki kawai"

Murmushi tayi, amma Babu yanda za'ai zaizo takasa shirya masa wani abu

Daga nasa bangaren yace "me kikeso nataho miki dashi?"

"mamy ya Yusif, ita nakeso, nayi missing dinta"

Murmushi yayi yace "tunda zaki ganni ai Kamar zaki ganta ne"

"to shikkenan ya Yusif sai kazo"

Tashi tayi taje ta sanar da Momy, nan da nan kuwa Momy ta aiki Adala kasuwa tasiyo musu abubuwan buqata, Adala tana dawowa suka hau aiki itada Nihla,ko sau daya bataga Abba yafuto ba, may be baya gidan ne, aikin sukaci gaba dayi lokaci daya gida yadauki qamshin hadadden girki

Saida Nihla taga komai yayi normal sannan taje tashiga wanka

Karfe biyu saura yakirata yace yana bakin get
Kwalliyar datayi ta doguwar riga ta atamfa ya karbi jikinta, tayi mutuqar kyau sosai
Da kanta tafuto taje ta taryoshi daga bakin get,ta karbi key din motarsa tabawa Direban gidan tace yashigo masa da ita
Chapter 40 · 0% Book details