← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 59

Sashe 10

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama Nihla tana gama hadawa tadauka adan qaramin tire, tazo tawuce tagaban Momy tashige dakin nasa, saura kadan tasaki farantin dake hannunta, saboda yanda taganshi dagashi sai gajeren wando 😳, babu riga ajikinsa,gashi kwance a qirjinsa, yana kwance yana waya qasa qasa, batasan dawa yake wayar ba

Qamewa tayi a tsaye, takasa qaraso wa ciki, tayi dana sanin shigowa dakin nan nasa batare da nocking ba

shi kansa baiyi tunanin shigowar taba, futowarsa kenan daga wanka yasaka Dan gajeren wandon, ko shirya wa baiyi ba aka kira wayarsa shine yad'an kishingid'a yana wayar

cikin ransa ya furta "yasalam! Yarinyar nan kada ta raina shi fa" ahankali yatashi zaune tareda zubo qafafunsa zuwa qasa

Ya tsareta da ido Bece mata komai ba, hannunta ne yafara rawa, duk ta rikice, wanne irin qirji ne dashi haka me fadi? Duk Ta diririce tarasa me zatayi

Shima ya lura da yanayin data shiga, ko menene ya tsoratata take karkarwa haka? 🤔 🤣
Ya tambayi kansa.

Cikin in-ina tafara magana "Am dama... dama coffee..."

"zoki ajiye"
Abinda yace da ita kenan

Ahankali ta taka ta qarasa wajansa, sai kawar dakai take, takasa kallansa, ta tsugunna ta ajiye masa agabansa tafuto da sauri

Binta yayi da kallo, to menene abin tsoro ajikinsa ? To kodan ta ganshi haka ne dukta tsorata? Tabe bakinsa yayi, sannan ya kalli wayar tasa yaga anma kashe, shima bai sake kiraba yayi wulli da wayar yadauki coffee din data kawo masa

Tana futowa daga dakin tazauna afalo kusa da Momy suna kallo, amma gaba daya hankalinta bayakan kallan, 🤣

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tsawon satin su biyu da zuwansu , koda yaushe da irin kulawar da Nihla takewa Abba, zuwan yanzu kam, kowa yasan cewa Nihla nason Abba, Shidinne de suka rasa gane Inda yadosa

Alhaji ne yashigo falon nasu dawowar sa kenan daga wata tafiya dayayi, Momy tanayi masa sannu da zuwa, ya amsa mata, yana zama akan kujera, "ina ya rannan ne?"

"Nihla bata nan taje wajan Ilham, Abba kuma ni Tun safe ma banganshi ba "

Wayarsa yadauka ya kira Abban
" kazo kaida Aslam ku sameni agida yanzu, kokuma ka turomin shi "
Yana fada masa haka ya kashe wayar

Basuda dauki lokaci ba sai gasu sun shigo shida Aslam din, cikin ladabi suka tsugunna agabansa bayan sun gaida shi,Alhaji ya dubesu " Aslam inaso ka shirya kaje India ka dauko Aisha daga makaranta, munyi magana da abokina cewa harma tarafa university, to Zan turoma adress din gidan, saika shirya kaje kutaho tare "

Momy ta kalleshi tace " Amma Alhaji lafiya kuwa? "

" lafiya kalau Alhamdulillah, kawai de lokacin karanta wasiyyar hajiya ne yayi, tunda Allah yayi mana Tsawon rai, gara intara kan kowa na family a karanta wasiyyar agabansa "

Momy ta Jinjina kai, tace" hakane, Allah Mai iko, kwanci tashi kenan "

Beyi mata magana ba, yadubi Aslam din yace " shine kiran dama, ka shirya katafi, ka tabbatar kun dawo akan lokaci "

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

" gaskiya Ilham akwai matsala "

" matsala kuma Nihla? Allah yarabamu da matsala, 🤣
Meyake faruwa? "

" Ilham ina tunanin son yaya Abba nake wallahi, shikuma naga Kamar hankalinsa baya kaina, ina yawan tunanin sa, sannan ni Tun ina qarama nakasa mantashi a raina, Ilham ina tsoro kar yaya Abba Yaqi saurara ta "

" soyaiya Nihla? Kuma ma da yaya Abba? Anya baki debo da zafi ba Nihla? "

" nima abinda nake tsoro kenan Ilham, bansan ya zanyi ba wallahi "

" kinga ki kwantar da hankalin ki, shima nasan Babu yanda za'ai yaganki amma baiji aransa cewa yana sonki ba,Nihla Allah yamiki kyau, sannan kuma ke dashi duka DANGI 'DAYA ne, bazai qikiba, dan'uwanki ne, tunda duk cikin mu Babu Wanda yake sakewa da'ita Kamar ke, amma idan zaki iya to kiyi masa maganar mana "

Kai tsaye tace" bazan iyaba Ilham, yanamin mugun kwarjini wallahi, kullum naganshi agabana ma gabana tsananta faduwa yake, sannan yana cikamin ido, koba wannan bama bazan iya tunkarar namiji da wannan maganar ba "

Ilham tayi ajiyar zuciya," hakane kam,gaskiya gara shiya fara furta miki, amma mezai hana cikin siyasa kifara nuna masa? "

" to ta wacce hanya kenan Ilham? "

" kulawa, kidinga bashi kulawa yanda yadace "

" Ilham duk Wanda Yazauna a part dinmu zaisan cewa ina bawa ya Abba kulawa ta gaske, saboda haka kicire kulawa a lissafi"

Girgiza kanta tayi tace "gaskiya ne wannan, nima shedace, ke kinga mudena bata lokacinmu akan wannan tunanin, duk miskilancinsa qarya yake ya juyawa mace Kamar ki baya Nihla"

tace" da gaske kike Ilham? "

Girgizakai Ilham tayi," da gaske nake "

Cikin farin ciki ta rungume Ilham

(to ko yaya zata kasance?ko yaya bayanin wasiyya? Fatana kuci gaba da kasancewa Dani)

Kada amanta da sharhi da Comments 🙏🏻

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/19, 12:52 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️

{Romance & Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook 👇

https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

13&14

Bayan kwana biyu Aslam ya shirya yatafi India domin tahowa da Aisha, yaso sutafi tareda Abba amma sai Abban Yaqi
Yana sauka a Airport yakira number da Daddy ne yaturo masa amma wayar taqi shiga, haka yadinga tsaki shi kadai
Daga qarshe saiya kira Daddy yafada masa, a lokacin Daddy yasa Alhaji Basiru yatura masa number Aisha

Aslam na ganin number nan take yakirata, amma yakira yakai sau hudu bata daga wayar ba, haka yasake kiran Daddy ya sanar masa, daga qarshe de sai Daddy ne yayi masa kwatancen gidan da kansa, shikuma yahau taxi suka tafi, daqyar ma me taxi din yagane abinda Aslam din yake nufi, saboda shi Babu turanci, shikuma Aslam Babu yaran hindi 🤣

Sunyi tafiya Mai nisa sannan yasauke Aslam ya nuna masa bus din dazai shiga, zata kaishi har kofar gida

Dole saida dala yayi amfani wajan sallamar me taxi din, sannan yafara jiran zuwan bus
Yanayin garin yake kalla da dan hadari kadan, Kamar wasa kuwa aka fara yayyafi, mutane dasukasan kan garinsu kowa sai yake baza lema, Aslam kuwa sai kare ruwa yake da hannu amma abin ba riba🤣

Ruwan yafara jiqa masa kayansa saiga bus din tazo ta tsaya awajan, gani yayi mutane suna shiga, shima yace ai ko ba ita bace wallahi shiga zaiyi, sukaishi koma ina ne 🤣

Duk kujerun motar ma sun cika, sai wata yarinya datake zaune gefenta akwai kujera daya, kallo daya yayi mata yagane cewa Babbar arniyace, shigar ta kadai zaka kalla kagane hakan

Riga da wando ne a jikinta kayan ya kamata sosai, sannan gashinta awaje sai Dan qaramin mayafi data dora akai Wanda dashi da Babu duk daya
Itama kallansa tayi, taganshi a tsaye yariqe karfen Mota, kayan jikinsa sunyi masa kyau sosai, da yaren India tace masa yazo yazauna, taga ko Kallanta ma baiyiba alamun baima san dashi takeba
Dan haka tace "hi"

Sai lokacin ya juyo

Tace "please come and sit"

Kallanta yasakeyi ya yatsina fuska, "no, thank you" yafada mata haka yana yatsina fuska
Hankalinta ta maida kan window bata qarabi ta kansa ba

Wayarsa yaciro yaciro daga Aljihun jeans d'insa yakira Abba, Abba yana dauka Aslam yafara zuba "Abokina kasan me? Wallahi gara da Allah yasa baka biyoni ba, gani nan muna tafe awata bus tana tafiya yanda kasan hawainiya, ni a tsaye ma nake narasa wajan zama"

Abba yace "Kamar ya?"

"to gashinan de kowa yana zaune, babu kujera sai guda daya, ita kuma wata qatuwar arniyace azaune nake fadama 🙊, inani ina zama kusa da manyan arna😳
Shegiya harda cewa wai in zauna, d'an iska neni, ina zama zata liqemin daga nan kuma ta addabi rayuwata"

Murmushi Abba yayi, yasan halin Aslam sarai, "to kayi hakuri mana, insha Allah zakuje lafiya"

Wani uban birki aka taka, hakan yasa Aslam yayi gaba yasake dawowa baya, nan take yakashe wayar yasake riqe karfen 🤣

Mutum uku ne suka fita, kujerar datake gaban yarinyar Babu kowa, nan yakoma Yazauna, yarinyar tanata kallansa

Kafin su qarasa Inda zaije motar ta lalace, kowa yafuto, wasu suka fara tare Mota, wasu kuma suka tsaya, kiran sallah yaji anayi awani masallaci, Dan haka yaje wani dan case agefen su yasiyo ruwa, yadawo wajan motar ya tsugunna yafara daura alwala

Yarinyar tana tsaye a gefensa, duk tana kallansa, ajiyar zuciya tayi, tataka Ahankali ta qaraso wajansa cikin yaren hausa tace masa "bawan Allah Dan Allah idan kayi sauran ruwan inaso nima zanyi sallah, kudin hannuna baida yawa bazai isheniba"🤣

Shiruuu Aslam yayi Kamar an kwada masa sanda🙆🏻‍♀️
Kasa Dagowa yayi, bare yahada ido da ita 🤣

Tasake cemasa "dan Allah, kaji"

Sai a lokacin yadago kansa, cikin kuskurin kunya yace "yanzu ke, dama kinsan kina jin hausa kika barni inata zuba?"

Murmushi tayi batare datayi magana ba, Ruwan ya miqa mata yace "gashi inde ruwa ne, ai ruwa baya had'a fad'a, shi musulmi ai dan'uwan musulmi ne" 🤣

Hannunta ta meqo zata karbi gorar Ruwan idonsa yasauka akan wani abun hannunta irin Wanda yan gayu suke daurawa maza da mata, amma nata anrubuta mata MAZAWAJE da manyan harufa 😃

Fasa bata Ruwan yayi, ya tsaya yakalli fuskarta dakyau, aishi sai yanzu nema yaga yarinyar tanayi masa kama da Nihla sosai, saide tafi Nihla cika dakuma 'yar qiba, yayi ajiyar zuciya yace "ke fadamin, Yaya sunanki?"

Murmushi tayi tace "Aysha Basiru Abubakar Mazawaje" 🙆🏻‍♀️
Cikin ransa yace tabd'i, dara tasake cin gida kenan, yatsunsa biyar ya nuna mata yace "uwaki" 🤣

Yaci gaba da cewa "to a qasar nan qafata qafarki dake Zan koma Nigeria, Aslam ne Dan gidan Alhaji Baqir yayan babanki"

Cikin sauri tace "yaya Aslam, Innalillah..., ya akai nakasa ganeka?"

"aikokin ganeni, ko baki ganeniba, daga nan, babu Inda zan barki kije,wuce Muje muhau wata motar kikaini gidan"

"toka bari muyi sallah mana, bani Ruwan nayi alwala ni"

"da wannan shigar zakiyi sallah? Haba, haba, wannan kam baki isaba, ina wayarki ina kira baki dagaba?"

Jakar hannunta ta duba tace "kaganta acikin jaka, niban saniba"

Yace "yayi kyau, to wuce Muje gidan" 🤣

Daga nan tajuya sukayi bakin titi domin tare wata motar

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Kallanta yayi idonsa akan manyan qirjinta yace "gaskiya naji dadin rawar nan, gashi gayu sunzo dayawa, club din yacika sosai, Ina alfahri dake Diyana kin iya rawa ba qarya"
Chapter 10 · 0% Book details