← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 59

Sashe 33

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau bataje makaranta ba Inda take service, ta dade tana bacci dasafe sai wajan goma da rabi tatashi, doguwar riga ce a jikinta ta bacci amma me kauri, rigar batada hannu, sai hula datasa akanta, tana hamma tafuto falon anan taga Momy itada wani da alama likitane sun futo daga dakin ya Abba, yanayin Momy ta kalla kawai tasan Babu lafiya saboda yanda jikinta yayi sanyi,kuma hakan baya rasa nasaba da abinda likitan yafada mata, sallama sukai da Doc din sannan tajuya zata koma dakin nasa, Nihla tace "Momy lafiya?"

"wallahi Abba ne baida lafiya Nihla"

Tace "subhanallah, Allah yabashi lafiya Momy" tafadi haka tana kokarin juyawa dakinta

Momy ta kalleta da mamaki tace "yayanki baida lafiya, amma kina kokarin juyawa daki? Ba zakizo ki ganshi ba?"

Turo baki tayi gaba alamar shagwaba, Sannan tabiyo bayan Momy suka shiga dakin nasa, yau ne karo na farko data shigo dakin Tun bayan barin ta gidan, gaba daya dakin saiya koma mata sabo saboda ansauya komai nasa

Yana kwance yana bacci, dagashi sai wando three quater, da vest fara qal ajikinsa, kallonsa Nihla tayi, faffadan qirjinsa gashine kwance, sai Dan qaramin bakinsa daya fara bushewa, ko menene yake damunsa oho?

Kallan Momy tayi tace "Momy ai bacci ma yake, bari naje nayi wanka kafin yatashi" tafadi hakanne kawai danta gudu, saboda bata fatan ace yafarka yaganta a dakinsa

Abinda bata saniba kuwa shine idonsa biyu, kawai yana kunyar hada ido da Momy ne, tayaya zai iya Kallanta bayan fama dayayi da ciwon ciki Tun cikin dare kuma yau doc yazo yace yakamata ayi masa aure saboda sha'awa datake damunsa, tayaya zai iya hada ido da Momy?

Momy tace "a a, ai hakuri zakiyi da wannan wankan, nasa Adala tahada masa Tea, zanje na karbo, ki zauna karya farka shi kadai kozai nemi wani abu" 🤣

Wannan karan kam, ran Nihla baci yayi, harta kasa boye hakan akan fuskarta, Momy ma taga yanda yanayin ta ya sauya amma haka tayi shiru tafice daga dakin, taga alama Nihla har yanzu yarinya ce, yanda takejin ta aranta Kamar su Usman Babu yanda za'ai tadinga Hadata Da Abba Dan wata manufa, itace ta haifi Abba amma dole zata nuna masa kuskurensa akan abinda yayiwa Nihla abaya, amma hakan ba zaisa tazuba musu ido tana kallansu suna zaman doya da manja ba, koba komai dukansu yaranta ne, babu wanda zata nunawa banbanci acikinsu, tana wannan tunanin ta qarasa cikin kitchen din

Shiru Nihla tayi tana tana zaune akan bedside drower, ko Inda yakema bata kallo, shima yana jinta a gefensa amma bai bude idoba, asali ma jiyayi bugun zuciyarsa yana qara sauya wa, kuma yarasa dalilin hakan, yasan cewa a dole take zaune dashi, saboda yanda yake ganin tsanarsa qarara acikin idonta, yasan kozai mutu bazata kulashi ba

Ahankali wata dabara tafado masa, bari ya gwada, yasan idan yayi hakan dole zata ambaci sunansa, sannan tabashi kulawa

Ahankali yafara motsi tareda yatsina fuskarsa, cikin alamun ciwo yace "wayyo Allah nah.... Momy... Momy Zan mutu..."

Cikin sauri Nihla ta kalleshi, amma abin mamaki ko sunansa bata kamaba tace "subhanallahi, sannu" 🤣

Haushi yakama Abba, waime yarinyar nan take nufi ne? Murqususu yaci gaba dayi Kamar gaske, duk ya rikice Kamar bashi ba, handle din dakin da aka kama za'a bude yasa Nihla tayi tunanin Momy ce zata shigo, kuma tasan fada zata mata tace tana ganinsa ta qyaleshi, hakan yasa cikin sauri tatashi tadawo gefensa tazauna tana cewa "Sannu, sannu"

Jinta akusa dashi yasa yatashi Ahankali Yazauna, sannan yazuro qafafunsa qasan tiles din dakin yamiqe tsaye zai shige toilet, yana Miqewa kuwa mararsa ta murda agaske, cikin azaba yadawo Yazauna, baisan lokacin da yadora kansa akan kafadarta ba, hannunsa kuwa yana kan cinyarta, gaban Nihla yahau luguden faduwa, itafa tarasa gane Inda ya Abba yadosa, meyake nufi hakane?

Ahankali yaji maransa tadena ciwo yabude idonsa, amma me? Saiya kasa dauke kansa daga kan kafadarta, yanda ya kwantar da kan nasa hakan yabawa idonsa damar hango cikakkun nashanunta farare tas, cikin ransa yace wallahi natane Babu qari, but ya'akayi yarinyar nan takoma hakane cikin shekara hudu?

Turo dakin Momy tayi tashigo hannunta dauke da cup din Tea, ganinsu ahaka yasa ita kanta gabanta yafadi, anya Abba kuwa bason yarinyar nan yakeba? Me Abba yake shirin janyo musu? 🙆🏻‍♀️

Haka de takawar da tunanin aranta, takawo masa Tea din tace "gashi Abba, tashi kasha Tea"

Ahankali yadago kansa daga kafadarta, cikin dabara ta matsa can gefe dashi tana hamdala aranta, Tea din ya karba yafara shan ahankali, cikeda shawaga yace"Momy zafi "

Tace" nifa Abba dama ba rashin lafiyarka ba kadinga langabewa mutum kenan, kaiba qaramin yaro ba amma kadinga shagwaba, kuma wannan gashin na qirjinka ka zauna ka askeshi Dan Allah"🤣

Dukda yana jin jiki, saida ya danyi murmushi kadan, yasaci kallan Nihla, sai yaga kanta a sunkunye batama kallansu

Saida Momy tabashi magani yasha sai runtse ido yake alamun bayaso, sannan suka futo daga dakin itada Nihla

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Yau Tun safe tatashi da matsananciyar naquda, daqyar ta'iya kiran Aslam dayake wajan aiki, yana jin yanayin muryarta yasan ba kalau ba, haka yadawo gida suka tafi asbiti
Tayi doguwar naquda sai cikin dare ta haihu lafiya, tahaifi danta namiji Mai kamada ita sak
Tun asuba labari ya'isa family house cewa Ilham ta haihu, dasassafe kuwa asbitin yacika sosai da yan'uwa, Nihla kam tafi kowa murna, gata da ihlam haka suke zaune a dakin, sai wajan la'asar sannan suka dawo gida, amma Nihla sai dare tadawo agajiye, hajiya Na'ila bataga ta zamaba, tunda akai haihuwar tayi kane-kane akan komai, ko kara bata yiwa hajiya Abida ba, Wato Maman Ilham 😃

Ita kuwa hajiya Abida abin ma bai wani dameta ba tunda ana kula da yarinyar ai shikkenan, ita dadi ma taji, tasan cewa hakan alama ce ta Ilham din tana zaune da sirikarta lafiya

Bayan kwana bakwai aka radawa yaro suna Abubakar Wato Abba, suna kiransa da lil Abba

Da yamma ta shirya tsaf cikin riga da siket na leshi, Mai launin dark blue da sirkin fari, qananun kalba ne akanta, da kanta ta tsara kwalliya taci daurin dankwali Mai kyau, ta tattare kalbar tata tadaureta abaya, wayarta ce take qara taqi dauka, su Dida ne suke kiranta Tun dazu, tasan kuma bazai wuce suce basu ganta ba

Saida ta shirya tsaf sannan tayafa mayafin ta Dan ma dedeci tafuto falo, hayaniyar su ya Usman take juyowa a dakin ya Abba, tace to wannan yaushe sukazo, gefenta ta kalla taga wata waya qirar iphone tayi Murmushi tadauka tace may be ta ya farouq ce, tana daukar wayar kai tsaye tatafi camera tadinga yin Selfie masu shegen kyau, sai Style take qarawa tana yin pictures din, saida tagama sannan ta ajiye wayar ta qwalawa Momy kira

Sai gata tafuto daga dakin ya Abba ita dasu ya Usman ashe ma tare suke, suna futowa farouq yace "kai kai kai, ina zakije haka Kamar Wanda zakije wajan gasar sarauniyar kyau?"

Murmushi tayi, tace "ya farouq gidan suna Zan tafi"

Ya Usman yace "gaskiya wannan wankan nawa ne"

Murmushi tayi batace komai ba, Aliyu kuwa baiyi mata magana ce kawai de yana murmushi cikin ransa yana yaba kyawun surar yarinyar

Shikuwa Gogan abakin kofar dakin nasa ya tsaya hannunsa zube cikin aljihun wandonsa, yana qare mata kallo Bece dasu komaiba, yatsani yaga tanayiwa mutane murmushi saboda yanda take yin mugun kyau, musanman ma yanda dimple dinta suke futowa
Fuskarsa adaure Babu alamun wasa yake kallanta, amma yakasa cewa uffan

Momy ta kalleta tace "masha Allah, yanmatan Momy kinyi kyau sosai, bari na gyara miki daurin dankwalin naki"

Nihla ta tsaya Momy kuwa ta qara gyara mata daurin, sannan tayi mata sallama tatafi

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Gidan suna yayi albarka sosai, Mazawaje family duk sunje, iyayenne mata kawai basujeba, saikuma 'yan'uwan mahaifiyar ta suma duk sunje sosai, maijego tana shiga cikin kayaiyaki na alfarma itada Baby

Har dare yayi anata hidima sannan mutane suka Dan rarragu, duk wannan abun da ake jikin Dida asanyaye yake, sai bayan mutane sun watse ne da daddare Nihla take cewa "Dida meyake damunki ne Tun yamma kinyi shiru"

Tace "tunanin ya Fawaz nake, ina tsoron karyaqi shan ma ganinsa"

Diyana tace "Dida kina shagwaba ya Fawaz wallahi, koda yake soyaiya ce, rannan ma munyi waya da mum take cemin tabawa driver yakawo miki jakar ki tunda kintafi Babu sallama" 🤣

Murmushi tayi kawai

Ilham tace "kice anaji da yayan nawa, toki sakarwa dan'uwana jiki de yamore ehe"

Diyana tace "um, nikam danba qara, Tunna farko bansake yarda ba"

Nihla tace "waiku Dan Allah miye hakan, kawai saiku dinga yin wannan firar agabana, salon ku lalatani"

Dida tace "kwana nawane kema Nihla, ai Kamar yaune"

Diyana tace "ke gwauruwa waye zaizo yadauke ki ne? Kingani ya Adam zaizo, kuma Dida ma nasan ya Fawaz zaizo"

Tace "nikam driver, dama shiya kawoni"

Itama Diyanan tace "wai kina nufin ya Abba ba zaizo yadauke ki ba?"

"ya Abba fa kikace, ashe kuwa saide na kwana anan, keni fa ko magana bamayi, kowa harkarsa yake agidan nan infada miki"

Ilham tace "haba Nihla, ya Abban kine fa, kudena Dan Allah"

Itade Nihla shiru tayi tanajin su suna zancen su ta qyalesu, taga alama Ilham ta Manta cin mutuncin dayayi mata

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Fira suke sunata kwasar daria amma shi yana zaune akujera shi kadai ya zubawa wayarsa ido, farouq Tun dazu ya lura kwata-kwata hankalin Abba yanakan wayarsa, ko kallansu Babu kawai ya qurawa waya ido

Ahankali yatashi yayi kitchen Kamar gaske 🤣
Soyake yaga menene yadauke hankalinsa haka, daya dauko Ruwan da niyya yazo wucewa ta bayan Abba,karaf idonsa yasauka akan screen din wayar Abba, pictures din Nihla ne, kuma da kayan data fita dashi dazu da yamma ne, toya akai Abba yasamu pictures din? Yaushe yayi mata? Dama sun fara shiri shida itane harya fara yimata photo awaya?
Ganin Babu me bashi amsa yasa ya tsaya yana kallan Abba dayake kallan pictures din daya baya daya, idan yashiga cikin guda daya saiya dade yana kalla sannan zai sake zubawa nagaba ido

Momy data lura shurun nasa yayi yawa tace "Abba na lafiya de ko?"

Kafin Abba yayi magana farouq dayake bayansa a tsaye yace "lafiya Momy, yana ganin abinda yake rayuwa tare dashi ne acikin gidan"
Chapter 33 · 0% Book details