Sashe 15
Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tabbas hakane, laifin wani baya shafar wani, amma kuma Babu dadi kayi rubutu a karanta ma bayan ansan kanason Comments a share ka, danku nake wannan rubutun, be kamata agani ayi shiru ba, masu kirana, masu min private text, masuyi min magana ta group, da Wanda suka min ta page d'ina, duk naji maganganunku, nagode da soyaiyar dakuke nunamin, insha Allah zanci gaba da typing, daga qarshe wannan page din na sadaukar dashi ga dukkanin masoyan Amnah El Yaqoub 💋
'yan labe ina kuke? 🤔 To Allah yasa ku d'ore dayin Comments ehe😚😚
17&18
Liman ya kalli Alhaji Abubakar kozaice wani abu tunda shi ne babba, amma tashin hankalin da Alhaji Baqir ya hango a fuskar Daddy ne yasa shi yayi magana dasu yace "ala gafarta Malam mungode, mungode sosai,"
Yadauko kudi a aljihunsa masu yawa ya ajiye musu, Sannan yakama hannun Daddy suka futo daga masallacin, Alhaji Kabeer kuma shine yake sanarwa da mutane ansoke daya daurin auren, daga nan yaci gaba da godia ga jama'ar dasuka gayyata
Uban gayya kuwa fuskarsa Babu yabo Babu fallasa Wato Abba
Angwaye dukda dama can suna cikin bacin rai, sai abin yasake qaruwa
Usman yadafe kansa, meyasa baba Ibrahim zai musu haka? Amma aida yayi hakuri anbi komai Ahankali ko, amma abu acikin taron mutanen da sukazo daurin aure
Dan haka yayiwa su Aliyu alama da ido, nan danan suka futo gaba dayansu sukabi bayan Daddy
Su Daddy kuwa saida sukaje bakin get sannan Alhaji Baqir yasaki hannunsa yace "Alhaji kayi hakuri, nasan yanda kake ji acikin ranka, kayi hakuri" ya qarasa maganar yana bubbuga kafadarsa
Su Usman ne suka qaraso, Aliyu yajashi hannun Daddy yace "Daddy Muje ciki"
Alhaji Baqir yawuce part dinsa jiki a sanyaye
Suma sukaja hannun Daddy suka tafi, mutane baqi anata hidima, dasuka shigo kowa sai gaida su yake amma su Usman ne masu amsawa, suna shiga dakin Daddy gaba dayansu suka zauna Babu me magana acikinsu, farouq yafuto daga dakin yayi wajan Momy
Yana zuwa yakama hannun yace "Momy zokiji"
Kallansa tayi tace "jarababbe, farouq Dan Allah kabarni nahuta yau ana bikinma bazaka rabu Dani kaima kaje wajan mutanan ku ba"
Yace "Momy kitaho please"
Fuskarsa ta kalla taga Babu wani wasa ko Fara'ah, mamaki ya kamata, Dan haka kai tsaye tabishi zuwa dakin Daddy
Kujera ta nema tazauna, tace "yanaganku haka jiki a sanyaye? Meyake faruwa ne?"
Daddy yayi shiru har lokacin Bece komai ba, Aliyu ne yafara magana "Momy Wallahi fa ansamu matsala, anfasa auren Nihla da Abba"
Cikin mamaki tace "me kace Aliyu?"
Usman yace "hakane Momy, baba Ibrahim yazo yadauketa, suntafi"
Adede lokacin Abba yashigo dakin, yanemi waje Yazauna, duk Babu Wanda ya kulashi
Momy ta kalli Daddy tace "to Alhaji meyasa zakayi shiru? Yanzu de ka kirashi kafada masa Dan Allah ni yadawo min da yarinya" 🤣
Ajiyar zuciya Daddy yayi, sai a lokacin yayi magana "Ibrahim ya nunamin yafini iko akan Nihla ne, yanda na nuna masa iko da farko, shine yazo har gida ya nunamin yafini iko akanta"
Tace "mekake nufi Alhaji, bangane maganganun ka ba"
Yace "Rahma bayan rasuwar Aisha nashiga tashin hankalin da ban taba fuskantaba, Nihla kadai Zan gani naji dadi, ita kadai Zan gani yarinyar inji Kamar Aisha tace akusa Dani, hakan yasa lokacin dazamu dawo gida kai tsaye nace ku fito mutafi, saboda ina tsoron inyiwa Mai hakuri magana yace bazai ban itaba, nasan shima yaji mutuwar Aysha, Awannan lokacin bazai taba yarda yarabu da 'yarsa ba, nikuma Rahma bazan iya tahowa nabar jinin Aisha Awannan wajan ba, shiyasa nadauko ta muka Taho batare da iznin mahaifin ta ba "
Momy tace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un,"
Dukda taji gaskiyar magana a bakinsu, wani bangaren na zuciyarta bai yardaba, wayarta tadauka takira layin Nihla, Adayan bangaren wayar tana hannun Dida tana ganin sunan Anty tasan cewa Momy ce, saboda ita kadai Nihla take cewa Anty
Ta daga wayar tace "Momy Nihla tafita bakin get, wai babanta yazo"
Kashe wayar Momy tayi tace "Innalillah... Yanzu Alhaji shikkenan Nihla tatafi? Inaji ina gani anrabani da 'yata..." Sai kuka
Su farouq suka dawo gefenta suna bata hakuri, takalli Abba tace "duk abinda yafaru, laifin ka ne, Inda ace baka nunawa yarsa qiyayya ba, babu abinda zaisa Ibrahim yazo yatafi da ita, idan ma akan antaho da ita batare da sanin sabane to danaka laifin, na tabbatar labari yaj...j...ji" numfashi tane yafara sama
Anan maganar ta tsaya, numfashinta yana qara yin sama, cikin tashin hankali Abba yataso yacire Babbar rigar jikinsa yayi wulli da ita 🤣
Ya cacimeta yana kiran "Momy! Momy!!,"
Amma inaaaa, numfashinta ne kawai yake sama, qirjinta sai Dagowa yake, lokaci daya kuma, jikinta yasaki
Cak Abba yadauketa yadawo da ita kan gadon Daddy, farouq yadauko ruwa a fridge ya shafa mata, Usman kuma yafara kiran number family doctor nasu yace gashinan zuwa
Saida tadauki lokaci kafin ta farfado, tana bude idonta tafara kuka, Daddy yanaga yashiga tashin hankali ashe duk abinda yakeji Rahma tafi shi 🤣
Mamaki yagama kashe Abba, yanzu duk saboda Nihla suke wannan abun? Lalle ba qaramin so suke mataba
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Sai yamma liss suka sauka, saboda Alhaji Isma'iel bayasan gudu, futowa sukai daga ciki motar, Yusif yasaki miqa yana fadin "wash Allah" idonsa akan Nihla
Mami tace "Yusif banasan wannan san jikin fa, to yanmata de basason rago, oya bude boot ka dauki kaya mushiga"
Yace "yanzu ni dinne rago?"
Murmushi tayi, ta kalli Nihla data shagala wajan kallan hadadden gidan, yanzu itace zatayi rayuwa acikin wannan gidan? Duniya kenan
Mami tace "Muje ciki Nihla"
Fuskarta Babu yabo ba fallasa tace "bari nadauki wata jakar mami"
Kusadashi taje ta tsaya, shi beyi mata magana ba itama haka, haushi yaqara kama Yusif, duk murnar dayake zaizo yaganta yaga yanda takoma amma shine tashareshi, 🤣
Cikin fishi yadauki jaka guda daya yamiqe zaiyi ciki
Dasauri ta tareshi tareda miqa hannu zata karbi jakar tace masa "kawo jakar"
Lokaci daya hannunsu yahadu dana juna, kallan hannunta yayi zanen qunshin da akayi mata yayi kyau sosai, Dasauri ya fizge jakar yace "no Barshi kawai"
Daga haka yayi ciki, sai wata tadauka acikin boot din tabiyosu ciki
Dakinda zata zauna mami ta nuna mata, sannan tashige ciki, anan taga babanta yana ciki, yana futo mata da kayaiyakinta na sakawa daga cikin jakarsa, cikin ranta tace dama de baba yagama shirya komai
Jakar yadauka yatafi Inda akayi masa masauqi daga can baya
Yana fita taga wayarsa ya mantata, Dasauri tadauka tasaka number Momy tafara kira
Acan kano kuwa gida duk ya hargitse yanmata duk sun shiga damuwa saboda labarin tafiyar Nihla, Ilham tafi kowa Baqin ciki saboda Babu abokiyar shawara antafi, Dan dole ake saka su abu su yi, yanzu ma wanka akasa ko wacce tayi domin anjima kadan za'akai kowa dakin mijinta
Apart din Momy kuwa kowa sai neman ta yake yarasa, tunda tashiga dakin Daddy bayan doctor yazo yagama dubata bata sake futowa ba, wayartace data Nihla a gefenta, adede lokacin wayarta tafara qara, Dasauri ta dauka tace "Ibrahim Dan Allah kayi hakuri, munsan munyi maka laifi amma kayi hakuri kadawo min da yarinyar nan" hawaye yazubo mata tasa hannu tashare
Kuka Nihla tafara tace "Anty kidena kuka nice"
Dasauri tace "Nihla kece? Kina ina, gida kuka koma?"
"Anty gida baba yadawo Dani, amma yanzu muna Abuja, mun tafi Abuja gaba daya da zama Anty"
Momy tace "Innalillah...Nihla banji dadi ba, banji dadin tafiyarki ba yata, kiyafemana kinji?"
Tace "Anty kidena neman yafiyata ba kiyimin komaiba, kedin Kamar mahaifiyata ce"
Momy tace "to ai kinji Nihla, kema kikace kama, ba kama nakeso nayi da mahaifiyar ki ba Nihla, sonake ki daukeni amatsayin mahaifiyar ki, ki kirani da Momy Kamar yanda 'ya'yan cikina suke fadamin, ke dasu bakuda banbanci a wajena"
Jikin Nihla yayi sanyi sosai, bata taba sanin cewa Momy batasan Antyn datake fada mataba sai yau, ashe haka Momy take kaunarta? Wannan wacce irin soyaiya ce? Kasa magana tayi sai kuka datake sosai abaiyane
Alokacin baba yashigo yadawo daga masallaci kenan, tana ganinsa takwashe wayar, idonta jajir, tana share hawaye
Zama yayi agefenta ransa abace yafara magana "ke saboda rashin hankali, da hauka dayake damunki zaki zauna kinawa mutumin dabai damu dake ba kuka,? idan akayi muku auren waye zai wahala bayan ke?
Anayi wa mace auren dole kuma tayi hakuri tazauna din, amma namiji karkiyi tunanin lokaci daya zai hakura Yazauna dake amatsayin matar sa, yaron yafuto yace bayasonki to kema ki cireshi aranki, sannan daga yau ko awaya ne ban yarda ki nemesuba, "
Yana fadin haka yafice yabar mata dakin
Innalillahi... Baba bai taba fishi irin wannan ba, dama ance ka kiyayi fishin mutum Mai hakuri
Wai ita ta d'orawa kanta soyaiyar yaya Abba ne? Yaya zatayi da Rayuwar ta? Yanzu yaya Yusif yadawo amma ta gagara yimasa magana, ba kuma komai ne yasa hakanba sai tunanin datayi akan Abba, yadawo daga wata qasa tabi ta shishshige masa, daga qarshe ya Wulaqantata, tana tsoron shima tayi masa magana daga qarshe yayi mata Wulaqanci, itada shigewa maza har abada, ya Abba ya koya mata Hankali 🤣
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Shadaya da rabi kowa ya watse daga gidan amare anbarsu su kadai, mayafin da'aka lullube mata kai dashi ta cire tayi wulli dashi tafara fada "ina dalili Zan takura kaina akan wannan malamin, kun wani rufeni da mayafi ai zafi sai yamin illa" 🤣
Saukowa tayi daga gadon, tafara cire kayan ta, daga ita sai under wear a jikinta, tadauki towel tashige wanka, da ruwa Mai Dan dumi tayi wankan saboda gajiyar biki
Tana futowa daga wanka tadawo gaban mirrow tafara shafe jikinta da turare, ko kayan bacci bata nemaba ta kashe wutar dakin ta kwanta bacci
🤣
Shikuwa Ango Adam sai wajan sha biyu yashigo gidan, hakanan gabansa yake faduwa saboda baisan mezai tarar ba
Falon yashigo da sallama, yaga Babu kowa, wucewa yayi zai shige dakinsa amma wata zuciyar tace yakamata kaje kaduba yarinyar nan, haqqinta yana kanka