← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 59

Sashe 49

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saura kadan tasaka shi dariya, amma saiyayi Dan murmushi yakawar da fuskar sa, yadafa bangon dakin harya shige cikin toilet din Ahankali

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya tasauke sannan takoma kan gadon ta zauna tareda dafe kanta🤦🏻‍♀️
Inda yariqe mata dinnan wani iri takeji

"Zoki gani"

Ta tsinci muryar ya Abba yana kiranta

Dak.. Dak.. Gabanta yafara faduwa, Innalillahi.... mekuma zataje tagani? 🤔

Abba dake toilet yaji shiru, yasaki yar qaramar dariya yasake cewa "Kizo kigani"

Nihla kuwa mayafin ta tayafa, tana jiran likita yashigo tagudu gida, sarai tana jinsa tayi shiru, da yasan zai iyayin wankan amma shine zaisata wahalar goge jiki

Masu cewa naqara yawan typing suma su qara yawan Comments, dama nafada more Comments more typing 👌🏻

Amnah El Yaqoub ✍🏻
[7/15, 12:34 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

55&56

Jin bata amsa masa ba yasa yayi Murmushi yafara wankan sa, yasan cewa sarai tana jinsa

Bai dauki lokaci Mai tsawo ba yafuto, yana sanye da kayan jikinsa, Nihla tana jinsa yafuto amma bata daga kai ta kalleshi ba, idonta aqasa, ya kalleta yayi Murmushi yasaka hannu yadauki sallaya sannan Yazauna abakin gadon yayi qasa da muryar sa Kamar Wanda yake rada yace "please yaushe mukazo asbiti?"

Yatsun hannun ta take wasa dasu batare data dago ta kalleshi ba tace "Shekaran jiya"

"kwana biyu kenan?" yasake yimata Tambayar

Kanta tadaga masa alamun hakane

Kansa ya Jinjina alamun gamsuwa sannan yatashi yatada kabbarar sallah

Yasha addu'ah sosai acikin sallar tasa, yana qara yiwa Allah godia, bayan ya idar ya ajiye abin sallar sannan yafara kokarin hawa gadon

Cikin sauri tatashi takoma kujera tazauna, Sam taqi yarda suhada ido dashi

Shikuma kwanciyar ta isheshi, haka Yazauna yasata agaba yana Kallanta, tanaji a jikinta ana Kallanta Dan haka koda wasa taqi yarda suhada ido dashi

Wayarta tadauka takira Momy, Momy na dagawa cikin shagwaba tace "Momy yaushe zakizo"

Momy tace "Nihla me zaisa nazo asbiti bayan gaki nan? Menene yake faruwa?"

"Momy Babu komai"

"A a ki sanar Dani idan akwai abinda yake faruwa"

"Babu komai Momy, dama ya farka ne"

Momy tace "to Alhamdulillah, Allah mungode ma, yana ina Abban?"

Satar kallan Abba tayi daya zubawa lips dinta ido yana kallo tace "gashinan"

"to bashi wayar"

Ahankali ta miqa masa wayar, memakon ya karbi wayar kadai sai da yahada da hannunta yariqe sannan yazare wayar yayi qasa da murya yace "Momy...."

"Abba na ashe jiki yayi sauqi, to Alhamdulillah bari mu shirya muzo"

"A a Momy, kiyi zaman ki, banajin ciwon sosai, sonake ma yasallame mu"

"to shikkenan idan kana buqatar wani abu de karka yi shiru ga Nihla nan"

Murmushi yayi yace "to Momy"

Wayar ya ajiye gefensa, a lokacin likitan dayake aiki da safe yadawo yadubashi,shima yayi mamakin yanda Abban ya warke

Abba yace "Doc. Ai ina ganin ma dazaka temaka daka sallamemu, saboda banajin komai yanzu, inajin karfi ajikina banajin ciwon komai"

Likitan yace "ka tabbatar?"

"da gaske nake Doc."

Yace "to shikkenan, zaku iya hada kayan ku, zanje nadawo yanzu"

Yana ganin Fitar likitan ya kalleta yace "madam kira min Abokina mana"

Kallansa tayi, taga wayar tana gefensa, tace "gata nan awajan ka"

"eh nasani, kinsan wayar yanmata, saisu"

Ahankali tamiqo hannunta zata dauki wayar yabi hannunta da kallo gwanin sha'awa dogaye dasu
Tadauki wayar tadannawa ya Aslam kira

Ringing din farko kuwa yadauka, batayi magana ba tabashi wayar

Cikin aji yace "Abokina"

Cikin murna Aslam yace "kaga Ango, Ango kasha qamshi, kace kanajin qamshin amaryar taka kamiqe"

Murmushi yayi kawai yace "naga saqon ka ai"

"Hmm ai addu'ah nayi tayi kada Nihla tagani, amma yanzu de jikin da sauqi ko"

"babu komai, na warke"

Aslam yasaka dariya yace "toganinan zuwa"
Daga nan sukai sallama, doc. Yazo yabasu takardar sallama, sannan Nihla tafara hada musu kayansu, ko minti goma ba'aiba Aslam yazo, suka tafi, sun shiga cikin Mota su agaba ita kadai abaya, wayarta tafara qara, tana dubawa taga baban tane, cikin ladabi tadauka "Baba ina kwana"

"lafiya Nihlan Diddi, Yaya su hajiya"

"suna nan kalau baba, inasu mamy"

"mamy tana nan lafiya, bakya wani abune yanzu ko"

"eh baba"

Gyaran murya yayi yace "to abinda nakeso dake shine ki saurari abinda Zan fada miki,jiya su Alhaji Abubakar sunzo andaura miki aure da Dansa Abubakar"

Gabanta yafadi, cikin sauri tadafa qirjinta tace "Aure kuma baba"

Abba da Aslam dake gaban Mota suna jinta, Aslam aransa yace to fada mata ake kenan
Abba kuwa shiru yayi yana jinta

Daga daya bangaren baba yace "eh aure, Yusuf da kansa shiya fara yiwa mahaifin sa magana akan ya hakura, saide bai yarda ba, saida sukazo jiya muka sake tabbatar wa, ga sadakinki ahannu na dubu dari cif,kiyiwa mijinki biyaiya sannan kiyiwa Yusufa addu'ah Allah yabashi mace tagari, mahaifin sane ya tsaya akai komai aka gama, sannan Alhaji Abubakar yanemi yafiyata da kansa, Dan haka banason wani tone tone, kiyi hakuri Allah yabaku zaman lafiya "

Hawaye suka silalo daga idonta, muryarta ta sauya tace" to baba "

" yawwa Allah yayi miki albarka "

"amin baba"

Daga nan sukai sallama, tayi shiru tana goge hawayen idonta, yanzu ashe dama shiyasa Momy ta barta awajan ya Abba, wani hawayen yasake zubo mata, Allah sarki ya Yusuf, haqiqa tayi rashin masoyi, yasha wahala akanta, tasa hannu tashare hawayen

Ahankali Abba yadubi Aslam yace "dan tsaya Aslam"

Babu musu kuwa ya tsaya, yabude gaban motar yafuto yadawo baya wajan ta Yazauna, Aslam yayi Murmushi yadauke kansa yaci gaba da driving

Sake matsawa yayi jikinta, tanajin yanda jikinta yake gogar nasa, yasaka hannunsa ta bayanta ya rungumota jikinsa, batada zabin daya wuce ta dora kanta akan faffadan qirjinsa

Bayanta yafara bubbugawa Ahankali, yasunkuyo da kansa dede kunnanta cikin rada yace "kiyi hakuri kidena kuka kinji, kukan ki yana tabamin zuciyata, kiyi shiru, kinji?"

Ahankali tadaga masa kanta, wani irin dadi Abba yaji, yanda yaga lokaci daya taji maganarsa

Cikin kunnanta yadora bakinsa yace "kin hakura?"

Wani irin abu taji yana yawo a jikinta, kode ya Abba ya Manta da ya Aslam ne, ahankali ta janye jikinta daga nasa

Shima sai murmushi dayayi, yamatso kusa da Aslam yace "Abokina ina Abba nah"

Aslam yayi Murmushin waskewa yace "kaiko, Hmm"

Dahaka suka qarasa cikin gida, suna zuwa tabude motar tafuto jikinta asanyaye, tayi part dinsu

Momy da Daddy na zaune afalo, Adala tana gefen Momy tanayi mata lissafin abubuwan dazata siyo mata, haka Nihla tazo ta samesu, cikin ladabi ta gaishe su tareda zama aqasa

Momy tace "a a, yana ganki yanzu, yanxun nanfa nake cewa Alhaji yatashi mutafi"

"Momy ai an sallamemu, yace yawarke"

Daddy yayi Murmushi, a lokacin suka shigo falon shida Aslam, suma gaida su sukai suka zauna aqasa

Daddy yace "Abba ashe jiki yayi sauqi"

Lallausar sumar kansa ya shafa yace "eh Daddy"

Yace "to Alhamdulillah, Dafarko de kayiwa Allah godia, sannan ka godewa Aslam,idan da hali ma kayi masa Babbar kyauta 😃sannan kaida Aslam din Idan jikinka yagama warware wa kushirya kuje can Abuja kuyiwa yaron nan Yusuf godia, yayi mutuqar kokari kuma yayi maka halacci, sannan dazu mahaifiyarka tayi waya da Ibrahim ta sanar dasu ka farka, sunce asaka musu lokacin da za'ayi biki yan'uwan mahaifin ta zasuzo daga jigawa ahadu anan, na Abuja ma zasu so gaba dayansu duk ayi komai anan, nikuma nafada musu nasaka sati daya, saboda haka sai kayi kokari zuwa next week din kagama shirya komai, saiku tare a gidanku "

Cikin farin-ciki yadan sosai qeyarsa yace" to Daddy insha Allah"

Sannan yakalli Nihla yace "kinji abinda yafaru ko?"

Tace "naji Daddy"

"to kiyi hakuri, ki qara akan Wanda kikai abaya, Allah yabaku zaman lafiya"

Tace "amin Daddy"

Momy ta miqe tace "Nihla taso Muje kitchen"

Bayan Momy tabi abaya, suna zuwa kitchen Momy tabata wani magani tace "kisha wannan yanzu, sai kici abinci kishirya kitafi gidan gyaran jikin"

Cikin ladabi tace "to Momy" tadauka tafara sha tana tunani aranta, Ilham tabata, Momy tana qara mata wani itakam yaya zatayi?
Momy ta kalleta tanajin tausayin yarinyar, gani take Kamar ba'a kyauta mata ba, Allah yasa de taso Abban nata, koda yake tasan Abban ma da naci, zai rarrasheta

Bayan tagama sha tawuce dakinta tazauna agefen gadon tana tunani, yanzu haka aure ne akanta fa, ashe yaya Abba yasani shiyasa yake min wasu irin abubuwa a asbiti, tatuno lokacin da ya Aslam yake cemata yaya marar lafiyarta, Hmm ashe duk sun sani, wayarta tadauka takira Anty Nadiya tabata labarin komai, nan take Nadiya tace zatazo bikin itama domin ta nemi yafiyar sadeek, tayi musu ala sanya alkhaairi, bayan sun kashe tatashi tashiga wanka, tafuto ta shirya tsaf taci abinci, sannan tayiwa Momy sallama tatafi driver yakai ta gidan

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Sai bayan sallar ishsha'i tadawo gida, zaune suke afalo su biyu shida Momy, Momy tana bashi coffee abaki, sallama tayi tashigo cikin falon idonsa yasauka akanta, doguwar riga ce a jikinta Mai godon hannu amma rigar abaje take sosai, ya dinta yanada santsi Kamar na abaya, da mayafin rigar tayi amfani tayafa akanta sauran kuma ta zuba shi baya, dukda fadin rigar hakan bai hana ka hango bajajjan hips dinta, yayinda cikakken qirjinta yadago ,hakan yasa cikinta shafewa, da yar qaramar jakar ta a hannunta

Cikin ransa yafara magana

ya'ilahi! Yanzu haka duk anganta ahaka, amma yaya zaiyi? Bazai iyamata magana ba tunda shine yake neman sulhu

Zama tayi akujera kusa da Momy, tace "wash Allah Momy nadawo"

Zaman datayi awajan kawai wani irin qamshi na daban yake tashi, ahankali ya lumshe idonsa sannan yabudesu

Momy tace "Sannu Nihla, ai gara da Allah yakawo ki, zanje in dubawa Alhaji wasu takardu, karbi wannan coffee din kibashi"

Baki taturo gaba alamar bataso, ita Momy batasan halin ya Abba ba, kawai shagwaba ce take damunsa, amma aiya warke
Haka tasa hannu ta karba Momy tashige dakin Daddy tabarsu anan

Gyara zaman sa yayi akan kujerar ya dauki fillo din kan kujera yadora a cinyarsa yazuba mata ido yana murmushi
Gaskiya yaji dadin abinda Momy tayi, wani irin nishadi yakeji aduk lokacin dasuka kasance su biyu shida ita

Kallanta yayi yace "zeyi sanyi fa"
Chapter 49 · 0% Book details