← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 59

Sashe 35

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri tafuto daga dakinta tana saka wayarta acikin jaka, sanye take da riga da wando na kayan bautar qasa, kayan anyi masa shape sosai, wandon nan tacika abinta Dam, rigar ma tabi jikinta, sai jacket din kayan data dora asama, tasaka Dan qaramin hijabi daya tsaya mata iya qirji, idonta sanye da glass

Qamshin turaren dasukaji ya bigesu ne yasa dukansu suka daga kansu suka kalleta
Itama kallansu tayi tace "ya Aslam ina kwana"

Murmushi yayi yace "lafiya Nihla, ya service"

Tace "Alhamdulillah" sannan takama hanya zata fice

"ke koma kicire wannan kayan"
Ta tsinci muryar Abba yana mata magana

Cak ta tsaya awajan, Sanna Tajuyo ta kalleshi fuskarta Babu yabo Babu fallasa "makaranta fa zanje, kuma kowa da uniform dinsa yake zuwa"

"nace kikoma kicire wannan kayan bazaki fita dasu ki janyo mana magana ba"

Aslam daya ga za'ayi drama agabansa saiyayi gyaran murya yace "haba Abba"

Sannan yadubi Nihla yace "Nihla jeki"

Babu musu kuwa tajuya tafice daga falon

Aslam ya kalleshi yaga fuskar nan ahade tace "meyasa zakayi mata magana Abba? Bayan kasan waje dayawa doka ne coppers suje batare da uniform ba"

"kalli shigar ta mana Aslam, tayaya yarinya 'yar musulmai zata fita da wannan kayan ana ganin komai nata"

Murmushi Aslam yayi yadubi abokin nasa "Abba kana kishin Nihla, kode sonta kakeyi ne?"

Cikin sauri yace "Babu wani so"

Aslam yace "Abba banason rainin wayo, baka sonta tayaya zaka dinga wannan masifar akan zata fita da wannan kayan? Ni nayi mata magana ne? Malam ko kanaso ko bakaso, ina tabbatar ma kakamu dason Nihla"

Hannunsa yadaga masa "dakata Aslam, Dan Allah kadena min wannan maganar, meyasa bazaka fahimce niba ne?"

Haushi yakama Aslam yace "Ok fahimta ko? Nafahimceka"

Daga nan ya tattara takardun gabansa yafice daga part din, aikin da ba'a qarasaba kenan 🤣

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Cikin farin-ciki ya kalleta, yana goge jikinsa da dan qaramin towel, "Baby Dida Tun dazu kike wannan kukan, bayan kuma kece kikace nayi, cemin kikai kinajin dadi nayi"

Hawayen idonta ta goge tace "to aiba wannan nace kayi ba, kuma saida nacema kabari amma tsabar mugun ta ka qyaleni"

Murmushi yayi, yau Babu Wanda yakai shi murna ya angonce, gaskiya masu aure sunji dadinsu, yasan hakane ai da tuni an wuce wajan yace "toki hakuri, ai daga yau nadena, wajan yadena ciwo?"

Jan zuciya tayi tace "akwai zafi sosai, rad'ad'i nakeji sosai, kuma zazzabi ma nakeji"

Yace "subhanallah, bari nagani"

Batayi masa musu ba, haka tabarshi yabude kafarta yaga wajan, yasa bakinsa yahura mata iska kadan aciki, jiyayi Kamar ya qara, amma dole hakura zaiyi Tun kafin ya ballowa kansa ruwa, tasa shi agaba tana kuka

Rufewa yayi yace "shikkenan to kiyi hakuri, zai daina insha Allah"

Ahankali ta daga masa kanta, yasaka hannu yana shafa kanta

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Washe gari da yamma yana kwance a dakinsa, tunanin maganar Aslam yakeyi, yanzu idan maganar Aslam ta tabbata gaskiya yaya zaiyi? Gabansa yafara faduwa, idan hakane kuwa ai yashiga ukunsa, tayaya zai iya fuskantar yarinyar dayace bayaso cikin bainar jama'ah yace yana sonta yanzu? Anya kuwa su Momy zasu bashi goyon baya akan hakan? Innalillah...

Sumar kansa ya hargitsa, yana tuno lokacin da Momy take ce masa tana gujemasa ranar dazaiyi DANA SANI (my first novel)

Kai, bazai iyu bama, tayaya zai fara son Nihla? To amma meyasa yakejin kishinta aransa? Meyasa ranar sunan takwaransa yakasa kwantar da hankalin sa akan dadewa datayi bata dawo gida ba? Meyasa yakejin haushi idon yaga tana wa yan'uwansa Fara'ah bashi ba? Meyasa? Meyasa duk yakejin hakan?

Wannan alamomin duk sun nuna cewa tabbas yanason Nihla, Innalillahi wa inna ilaihir raju'un..., Idanunsa ne suka cika da qwallah, yasan cewa Babu me fuskantarsa

To amma yasan Nihla, yasan cewa Nihla tana sonsa, yasan cewa koda kowa zai juya masa baya banda ita, amma yanda yake ganin tsanarsa a'idonta yasan cewa abinda wahala, amma tayaya zai gane cewa tana sonsa? Ta wacce hanya?

Wata dabara ce tafado masa, lokaci daya yadanji sanyi aransa, haka yatashi yashiga toilet yayi wanka, wata shadda yadauko yasaka Mai launin Ash, yasaka hula tareda Agogon sa qirar gucci, yayi masifar yin kyau, idan ka kalleshi Babu qarya saiya birgeka

Falon yafuto yanata zuba qamshi, Nihla tana kwance da waya a hannunta tana chatting, Momy tana zaune agefe, gaba dayansu kallansa sukayi, yayi mutuqar kyau Kamar bashi ba

Momy takasa yin shiru tace "Masha Allah, Abba wannan wankan sai ina?"

Murmushi yayi Wanda yaqara wa fuskarsa kyau, yasaci kallan Nihla, Sanna yace "Momy zanje wajan zance"

Momy tayi dariya tace "Alhamdulillah, gara da kayiwa kanka fada ai"

Haushi yakama Nihla, tayi shiru batace komai ba, Abba kuwa ya juya zai fita daga falon

yaje dede kofar falon ya tsinci maganarta tace "ya Abba"

Cak yaja ya tsaya awajan, shi yasan cewa Nihla tana sonsa, wani farin-ciki ya kamashi, finally yau de takira sunansa, cikin murmushin da yaqara masa kyau ya juya yana Kallanta yace "na'am"

Budar bakinta saitace "idan kaje ka gaishe ta" 🤣

Be'iya cemata komai ba saide Jinjina kansa dayayi kawai tareda ficewa daga falon

Yana fita itama tatashi tashige cikin dakinta, Momy tabita da kallo amma bataga komai akan fuskarta ba
Tana zuwa dakin tafada kan gadon ta tasaki wani irin kuka Mai cin rai, ita kanta tarasa dalilin yin kukan, haushin ta daya, yanda tadage ta gyara kanta, take Jan ajinta, duk Dan yaso ta tayi amfani da wannan damar wajan nuna masa kuskuren daya aikata abaya, yanzu komai yatashi abanza kenan, ashe duk wannan dauke kan datake abanza, ashe hankalinsa yanacan kan wata daban, Wato harda yimata Fara'ah yana amsawa Dan zaije wajan wata, to tunda hankalinsa yana kan wata, tayaya zata iya rama abinda yamata?

Haka tasha kukanta sannan tashige toilet ta wanke fuskarta tadawo falon tazauna

Yana futowa daga falon nasu yake ganin duhu-duhu a'idonsa, duk hasken dayake wajan Abba baya gani, duhu kawai yake gani, baisan Inda yake saka qafarsa ba,lokaci daya Idanunsa Yarufe ruf yadena ganin komai sai jinsa yayi yafada jikin mutum Wanda baisan ko waye ba

Daqyar Aslam da Allah yakawo shi gidan yanzu, yakawo Abba cikin falon

Momy da Nihla cikin tashin hankali sukai kansu, Momy tana cewa "subhanallah, Aslam lafiya? Menene ya sameshi? Yanzu yanzu fa yafita"

"Momy wallahi shigowa ta kenan nima naci karo dashi"

Momy ta kamashi suka qarasa cikin dakin Abban, akan gado suka kwantar dashi, Nihla tabude fridge din dakin tabawa Momy ruwa tace "Momy ga ruwa" jikinta sai rawa yake

Momy ta kalleta taga yanda duk ta rude, ta karbi Ruwan aka shafa masa a fuska, Allah ya temakesu yafarka, yana bude idonsa yasauke su akanta, kallo daya tayi masa tace "Sannu"

Yadaga mata kai, daga nan tafice daga dakin

Momy tace "meyake damun kane Abba na, naga lafiya kafita"

Ahankali yace "Momy kaina ke ciwo"

Tace "to Allah yasawaqe, bari ajima idan bakaji sauqi ba sai akira Doc"
Bece da ita komai, domin kuwa abinda yakeji yafi ciwon kan yawa, Inda ace ciwon kai ne Toda sauqi 🤣

Momy na fita Aslam yace "Abokina meyake faruwa ne? Meke damunka?"

Cikin damuwa yace "Aslam kayi Gaskiya, kafini gaskiya Aslam, ina sonta, Nikaina yanzu na tabbatar ina sonta" ya qarasa maganar tareda fashewa da kuka

Gaban Aslam yafadi, bade maganar datake ransa hakace take shirin kasancewa ba, kallan Abba yayi yace "Wacece?"

Kai tsaye yace "Nihla"

Aslam yayi shiru Tsawon second talatin,zaka dade kafin kaga Abba yana kuka Kamar haka, yasan cewa tabbas tunda haka ta faru toba qaramin so yakewa yarinyar ba, haka yasa hannu yayi tagumi hannu bibbiyu,
gaskiya Abba yadauko musu Babban aiki, kallansa yayi yace

"Gaskiya Abba akwai damuwa,ka janyo mana Babban aiki a gabanmu, maganar gaskiya itace kana ruwa tsundum kusada kada"

Cikin masifa Kamar bame kukaba yace "Dan Allah Aslam idan bazaka bani goyon bayaba to kamin shiru kawai, meyasa bazaka fahimci abinda nakeji bane?"

Cikin damuwa shima Aslam din yace "Abba aini nafi kowa fahimtar ka" 🤣

"dan Allah Aslam tashi kafita kabarni da abinda nakeji" yasa hannu ya goge hawayen idonsa

Sharhi please

Amnah El Yaqoub ✍️
[7/5, 10:18 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

39&40

Aslam yatashi yafuto daga dakin jikinsa a sanyaye, domin kuwa yasan abokin nasa yana cikin damuwa yanzu, maganar aikin data kawoshi ma baiyi ba.

Fitar Aslam keda wuya Abba ya danna kansa cikin fillo yana hawaye, to Aslam ma dayake makusancin abokinsa yakasa fahimtarsa inaga sauran jama'ar gida? 🤔

Har dare yayi sosai Abba bai sake futowa daga dakinsa ba, saide Momy tana zuwa tana dubashi akai akai

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Karfe goma na safe ma agida tayi mata, babu part din da batajeba cikin family house din nasu, tana zuwa part dinsu Nihla taji shiru Kamar Babu kowa, kai tsaye dakin Nihla tashiga taganta kwance tana bacci fillo rungume a qirjinta

Batare data tasheta ba, ta'ajiye mata lil Abba agefenta, yaron kuwa idonsa akan fan din dakin dake juyawa Ahankali

Fita tayi daga dakin tashiga kitchen din tanaso ta hadawa kanta Tea Dan taga Momy da Nihla harkar gayu suke ji ita kuwa tana goyon yaro bazata iya wannan zaman ba

Cikin baccinta taji yaron yana wasa, bude idonta tayi ta kalleshi, shi kadai, sai tsotsar hannu yake, murmushi tayi tatashi zaune tareda daukar sa tace "Wato mamanka tazo shine ta ajiye min kai tagudu danka tashen a bacci"

Kissing dinsa tayi, suka futo falo, anan taga taga Ilham zaune tana shan Tea da uban Bread a gabanta, Momy tana zaune da alama itama yanzu tatashi

Qarasowa tayi ta ajiye yaron tace "ashe kinzo, yau kece agida kenan"

Kafin Ilham tace wani abu momy tace "nima yanzu na futo naganta"

Ilham tace "Momy Tun dazu ya Aslam ya kawomu yawuce wajan aiki, ina zuwa wajan umma nace ko Abincin ta ba zanci ba wajan Nihla Zan tafi, shine na tarar da ita tana bacci, nabar mata Yayanta a dakin na futo"

Momy tace "Ah kin kyauta wallahi, gashinan ya warware,"

Daukansa Momy tayi tace "Abba nah, mekakeci ne?"

Daga nan tayi cikin dakinta dashi tabarsu anan suna fira
Chapter 35 · 0% Book details