← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 59

Sashe 28

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi tayi batare da tace masa komai ba tashige dakinta, shikuma yabi bayanta da kallo yana ganin yanda surar jikinta tafuto acikin kayan sakamakon jiqewa dasukai, haqiqa ya yarda cewa a yanxu kam yanason Dida, tunda haryakejin yanayin jikinsa yana sauya wa akanta

Washe gari dasafe dakansa yadauki Dida suka tafi asbiti wajan wani doctor yayi masa bayanin matsalar sa

Likitan yabashi shawarwari akan yanda zaiyi Yaqi da shan miyagun qwayoyi, Sannan kuma ya dorashi akan wasu magungunan, Wanda zai dinga sha koda shaye-shayen dayayi abaya sunyi masa wata illar batare daya saniba

Haka suka dawo gida cikeda farin ciki, babu wanda yakai Dida murna, yau ya Fawaz yadena shaye-shaye, haka al'amarin yaci gaba da kasancewa, Inda kwanaki suka qara ja, lokaci yana qara wucewa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Takardu ne a gabanta na handout, banda books manya manya dake jere a gabanta

Karatu take sosai, hankalinta kwance, dinkin doguwar riga ne a jikinta na atamfa, kanta Babu dankwali, hakan yasa dogon gashinta kwanciya agaban qirjinta kasancewar gaba tawatso shi

Turo dakin nata akayi a kashigo, amma bata daga kai ta kalli kofar ba, saboda tasan cewa Babu me shigo mata daki inba mamy ba

Saide kuka qamshin turaren dataji ne yasa tadago kanta Dasauri, Idanunsu ne suka hadu, lokaci daya murna ta baiyana a fuskarta

Tace "ya Yusif!, Dan Allah kaine? Yaushe kadawo?"

Murmushi yayi Yazauna agefen gadon, daga wajan qafafunta, yace "zanyi miki Surprice ne shiyasa nace kada afada miki yau zanzo qasar, but Dafarko dai ki sanar Dani me kikeci kika koma haka?, Nihla idan na ganki ahanya fa daqyar Zan iya gane ki, anya kece kuwa?"

Murmushi tayi tace "Allah ya Yusif kaganka ko? Nide bari na kawo ma ruwa"

Tana fadar haka tatashi daga kan gadon ta nufi fridge din dakin domin kawo masa ruwa, Yusif yabi bayanta da kallo yaga yanda hips dinta yake rawa acikin kayan, gaba daya Nihla ta sauya masa, acikin wannan 'yan shekarun takoma haka, kokuma danya dade baiganta bane? 🤔
Komai yaqaru ajikin yarinyar Kamar ba itaba, lalle dole yadinga kaffa-kaffa da'ita Tun kafin wani gayen yayi masa qafa 🤣

Yana wannan tunanin takawo masa ruwa da lemo ta ajiye masa, shide sai binta yake da kallo harta farajin kunyar kanta, zama tayi tace "ya Yusif ya hanya, Yaya kabaro china?"

"china tanacan Nihla, na kawo miki tsaraba Mai yawa harda kaya, but nasan may be suyi miki kadan, dannaga yanzu masha Allah, kinzama Babbar yarinya"

Murmushi tayi tace "a a fa ya Yusif, bawata Babbar yarinya nide"

Yace "kina zaune adaki ke kadai, ko tunani nama bakyayi ko"

Tace "ya Yusif kenan, tayaya Zan kasa tunaninka, kawai de karatu ne yamin yawa shiyasa, kaga munata shirye-shiryen rubuta exam din qarshe, yakamata na maida hankali akan karatu kozan samu sakamako Mai kyau, shiyasa duk nashiga damuwa ina zama adaki ina karatu"

Kallanta qaramin bakinta yake yanda take juyashi tana magana, baiso tadena yin maganar ba, gaba daya Nihla tabashi mamaki, nema take ta susutashi, wani irin kallan luv yayi mata tace "no kada kisake kirawa kanki damuwa inde kina tare dani, bakisan cewa ita kanta damuwar bata isa tazo wajan kyakykyawar mace Kamar kiba? Tana zuwa zanyi ball da'ita namaye miki gurbinta da tsananin farin-ciki"

Itama kallansa tayi tanajin dadin yanda yake sakata nishadi idan tana tare dashi, ko awaya yakirata bataso yace mata saida safe, bare kuma yanzu datake ganinsa azahiri

Masu buqatar DANGI DAYA daga farko su nemi wannan number 09039066577,kokuma kai tsaye suje suyi like na page dina zasu sameshi acan

Amnah El Yaqoub ✍️[7/2, 12:57 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

🤒Mutane dayawa suna cewa a posting din danayi na shekaran jiya basu gane gyadar miya ba
ba gyadar da'ake miyar taushe dasu amaro nake nufi ba, ita wannan gyadar miyar idan ki kaje wajan masu saida kayan qamshi na girki, ana hadawa da'ita, wasu suna sakata acikin miyar ja, tanada qamshi sosai, sannan jikinta baqi ne saikun fasa zakuga cikin ta da Jan duhu haka, amma wasu suna kiranta da Diyar miya, Wanda basu gane taba kuma suje wajan masu saida kayan qamshi irinsu citta da kanumfari suce abasu gyadar miya kokuma Diyar miya, insha Allah zasu samu , Allah yasa kun gane 🙏🏻

31&32

Tace "ya Yusif ga lemo nan baka shaba"

"baki zubamin ba ai"

Murmushi tayi tayi, tadauka ta tsiyaya masa lemon sannan tabashi, ya karba yasha Dan kadan ya ajiye "to bari nabarki, kici Gaba da karatun ki nima zanje nahuta, anjima sai musha fira ko"

Cikin kunya tace "to ya Yusif Allah yahuci gajia" bayan yafita kasa cigaba da karatun tayi, gaskiya ya Yusif yayi arayuwa, yana kokarin ganin yasakata nishadi akoda yaushe
Ahankali tatashi tafuto falon zuwa kitchen, mamy ma tashigo kitchen din tace "ai tunda naga yashiga dakinki nasan cewa saiya hanaki karatun sannan zai futo, gashi yanzu yataso ki"

Dariya tayi tace " a a mamy, nice nataso da kaina, inaso nahada masa abinci"

Mamy tayi Murmushi tanajin dadi aranta, tace "um to Allah ya temaka ni bari na fice" daga nan tafita daga kitchen din tsabar Nihla tana kokarin hadawa Yusif abinci

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Ahankali komai ke gudana, rayuwa natafiya yanda ya kamata awani wajan.
Tun Aslam da Ilham basu gane Dan qaramin cikin dake jikinta har suka dawo suka gane, sukaci gaba da bawa cikin ta kulawa, Wanda yatasa sosai yanzu

Zaune suke afalo shida ita ta dubeshi tace "ya Aslam yau ba zakaje wajan aiki bane?"

"Ok koratama kike ko?"

Tace "a a, inaso mu kasance tare ne, bansan kanayin nesa dani, shiyasa na tambayeka"

"yau banda aiki me yawa ne, zanyi agida kawai, wai in tambayeki mana Ilham"

Tace "inajin ka"

"idan kika haihu wanne suna kikeso a sakawa babyn?"

Ajiyar zuciya tayi tace "gaskiya idan mace ce Anty Aysha zamusa, idan kuma namiji ne... Muga, sunan wa yakamata musa masa.. Ina ganin sunan Babanku ko?"

Cikin farin ciki yace "Nikaina abinda nasa a raina kenan, inde na haifi mace, sunan tsohuwar budurwata zansa 🤣
But idan namiji ne, kidena ma tunanin Wanda zamu saka, Dan already abokina Zan yiwa takwara"

Kallansa tayi tace "wai ya Abba?"

Yace "yes, Abba zansa, because shine yabani shawarar yanda Zan shawo hankalin matata, kuma shawara tayi amfani ta kaini zuwa wata jihar, wadda bantaba tunanin akwai wata jiha Mai dadi kamarta ba"

Hannu tasa ta rufe fuskarta, wallahi maza kunyar su kadance, yanzu shi ya Abba dama shine yazuga ya Aslam ayi mata wannan abun kenan, kana ganinsa shiru-shiru Kamar bazai aikata ba🤣

Kallanta Aslam yayi yace "har yanzu de kunyar ce?haba qanwar budurwa ta, yakamata adena wannan kunyar haka"

Jikinsa ta fada tana murmushi, shikuma yadora hannunsa akan cikin ta yana shafa wa, tabbas yanzu ne yasan yayi aure.

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Yauma suna zaune shida ita afalo, gaba dayansu suna kan doguwar kujera, yau kuma littafin akdari ne a hannunsa yanayi mata bayanin sallah, da yanda zata gyara idan tayi rafkanuwa 🤣

Abin tun yana damun Diyana harya dena damunta, ace kullum karatu, karatu Yaqi ci Yaqi cinyewa Kamar cin qwan makauniya 🤣
Ganin idan tayi masa shiga ta daukan hankali ma saide yagani ya lumshe ido baya iya yimata komai yasa taci gaba yin shigar ta son ranta, tunda saide agani alumshe ido, batada damuwar komai, ita irin tsoron nanma da'ake tunanin ji a first night Diyana bata nuna komai, kanta tsaye take shigewa jikin mijinta ko'ajinta, kodan tasaba hulda da maza ne oho 🤔, kokuma Dan tasaba shiga cikin su suyi fira da Komai ne yasa hakan oho 🤔

Amma batasan cewa tana bala'in kunna ustazun nataba, kawai daure wa yake

Karatun yake mata amma tana kwance ajikinsa ta dora kanta agefen kafadarsa, tana ganin littafin, shikuma Adam yanayi mata bayani, shi yanaso maryam duk tasan wad'annan littattafan saboda yasan bata sansu ba abaya, shiyasa yadage yana koya mata, yanzu idan sun gama da littattafan ma, baqi zai fara koya mata na arabic, yanda zataji iya bude qur'ani da kanta ta karanta,🤣
Aishi yaji dadi sosai yanda maryam zata zauna tanaji ana karanta mata littafin addini tana koya, yaji dadin hakan sosai, kuma ansamu cigaba acikin Rayuwar ta

Littafin yana hannunsa na dama, ita kuma tana daga gefen hannunsa na hagu, ahankali takai hannunta ta sanya acikin masa hannun na hagu Wanda Babu littafin, idonta yana kan littafin amma tana wasa da tafin hannunsa acikin nata, wani irin abu yaji yana masa yawo ajinin jikinsa 😱
Hannun maryam yanada laushi sosai, yaso ya qwace hannun amma yakasa, haka yaci gaba yana karatun murya ashaqe, agefe guda kuma yana jin dadin yanda take wasa da hannun nasa, shiru yayi yadena karatun kawai yana saurarenta, Diyana taji yayi shiru tadago kanta ta kalleshi, sai ganinsa tayi idonsa a lumshe 🤣

Dariya yabata sosai, cikin ranta tace ya Adam kenan, sarkin lumshe idanuwa, taci gaba da abinda take

Ahankali yabude idonsa, duk sun qanqance, yadora su akan qirjinta, meyasa yake dagawa maryam qafa ne? Har yaushe zai tausaya mata bayan yasan cewa itama tasan komai,? Ai yayi hakuri, Tun ana jin tausayi kar adawo daukan haqqi kuma, ahankali Kamar me tsoron wani abu yadaga hannunsa ya dorashi akan qirjinta, Diyana da batasan abinda yakeba kanta na qasa kawai sai jin hannun ya Adam tayi akan qirjinta, wannan ne karon farko tunda take dashi dataji faduwar gaba, gabanta yafadi, cak ta tsaya da wasan datake da hannunsa

Kallanta yayi, yayi wurgi da littafin dake hannunsa akan daya kujerar, Diyana tabi littafin da kallo 🤣

Ahankali yafara shafa qirjinta yana jin wani irin dadi aransa, yau kam bazai iya hakuri ba, gara yafuto fili yafadawa matar sa yanda yake tsananin kaunarta, cikin sigar rada yanda ita kadai ce zata iya jin abinda yace, yace mata "Diyanaaaa!, please inaso nasha"
Chapter 28 · 0% Book details