Sashe 12
Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga baya yan gidan gaba dayansu suka qaraso asbitin, Aslam yafi kowa shiga tashin hankali, Daddy ya kalli Alhaji Basiru yace "wai dama batada lafiya ne?"
"wallahi yaya Abubakar kwana mukai bamuyi bacci ba, cikin ta yana ciwo, bayan wani dan lokaci saiya lafa, shine muka Taho Asbiti yanzu"
Alhaji Baqir yace "subhanallah, Allah yabata lafiya"
Gaba dayansu sukace amin, haka suka zauna jugum jugum, babu wanda yankewa dan'uwansa magana, har likitocin suka futo
Gaba dayansu sukai kansu da tambaya, Likitan ya goge gumin fuskarsa yace "Alhaji saide kuyi hakuri, Allah yayi mata cikawa, munyi iya kokarin mu ganin mun ceto Rayuwar ta, amma hakan ya gagara sakamakon ciwon Hanta datake dauke dashi, hantarta tariga ta lalace, kuyi hakuri"
Ilham najin haka ta yanke jiki tafadi, yaran kuwa kowa kuka yake, Aslam ya sulale Yazauna aqasa yana maimaita kalmar Innalillahi wa inna ilaihir raju'un acikin ransa
Gaba daya waje ya kaure da koke koke, babu me lallashin wani, haka suka dauki gawar Aysha suka tafi gida, akai mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya, Aslam kuka Kamar mace, duk yafita a hayyacinsa, saide muce Allah yaji qanta, idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tunda akai wannan mutuwa gidan yadawo shiru, Diyana kuwa kullum tana cikin hijabi🤣
tunda taga aysha qiri-qiri tamutu da quruciyarta, sosai mutuwar tataba matasan gidan, saboda basu taba kawowa kowa mutuwa acikinsu ba
Ranar ukunta yayi daidai da ranar da Daddy ya sanar za'ai meeting, amma ganin anyi musu rashi yasa aka sanarwa kowa sai bayan sati biyu akwai gagarumin family meeting.
Hakan ce kuwa ta kasance,ranarda sati biyu tacika kowa yatafi Babban dakin taro nacikin gidan mata da maza manya da yara, Usman shida matar sa da yaransa biyu, sai Aliyu shima yazo da matar sa da dansa daya namiji, farouq kuwa matar sa ko haihuwa batayi ba
kowa yazo yanaso yaji abinda wannan wasiyya ta qunsa
Samarin ne awaje kawai basu shiga ciki ba suna jira saisu Daddy sun qaraso
Sunata fira kadan kadan amma Aslam baya magana, Adam kuwa gabansa ne yake ta faduwa harya kasa boyewa yace "nifa gaskiya meeting dinnan danya zama dole ne amma gaskiya da bazan zoba, yau inada lacture, sannan gabana faduwa yake narasa dalili"
Fawaz kallansa yayi bai tankaba, Abba ma shiru yayi, Aslam kuwa daja tunda aysha tarasu suka kasa gane kansa
Kallansu yayi yace"wai badaku nake bane duk kunmin shiru?" 🤔
Ajiyar zuciya Fawaz yasauke yace" kai sai yanzu kakeji,? ni Tun jiya gabana yake faduwa, Kamar akwai abinda yake san faruwa Dani, amma koma menene Allah yasa ya sameni ni kadai banda Nihla "🤣
Kallansa Aslam yayi cikin mamaki, to kode Fawaz nason Nihla ne? 🤔
Kafin wani yace wani abu su Daddy suka qaraso wajan, shida Alhaji Baqir da Alhaji Basiru
Dakin taron suka shiga, sannan suma samarin suka bisu abaya
Wajan meeting din yayi kyau an qawata shi da lemuka da ruwa domin baqi 😃
Nihla tana kusada Momy, yayinda Ilham ma take gaban ummanta hajiya abida, suma su Dida itada Diyana suna gaban maman su hajiya Farida
Su daddy suna zama hall din yayi shiru, Kamar ruwa ya cinyesu, megadin gidanne yaqaraso dauke da akwatin da aka rufe takardar wasiyya aciki ya ajiye yajuya yafita 🤣
Daddy dakansa yatashi yabude, kowa yazuba masa na mujiya, yadauko takardar Yazauna sannan ya'ajiyeta agabansa
Yakai dubansa wajan samarin sun zauna waje daya gaba dayansu, Adam ya kalla yace "Adam taso kabude mana taro da Addu'ah"
Babu musu yatashi yadinga kwararo musu addu'ah, sannan aka shafa
Daddy yayi gyaran murya, yafara magana "Alhamdulillah, muna qara yiwa Allah godia akan Tsawon rai dayayi mana har muka kawo wannan lokaci cikin kwanciyar hankali, wadanda suka rasu acikin wannan family Aisha, da takwararta Aysha, muna yi musu addu'ah Allah yaji qan su"
Gaba daya aka amsa masa da "Amin"
Sannan yaci gaba da fadin
"insha Allah yanzu zamuji dalilin daya taramu anan wajan "
hall yaqara yin tsit, Daddy yabude takardar yayi tozali da rubutun Ajami, yadaga kansa yasake duban Adam yace"da Ajami sukayi rubutun, Adam kaine malami zoka karanta mana"
Hajiya na'ila tafara karkad'a kafarta tana hura hanci , jin ansake kiran dannata akaro na biyu
Jikin Adam a sanyaye yaje gaban iyayen nasa ya karbi takardar yafara karanta wa :Assalamu alaikum jama'ar wannan dangi Mai albarka, ni Abubakar Mazawaje mun zauna tareda matana guda biyu mun rubuta wannan wasiyya badan komai ba saidon hadin kan wannan zuri'a,mun yanke shawarar hada jikokinmu aure domin zumunci yaqara qullu wa,...
Adam yana zuwa nan yaji gabansa yafadi, jikinsa yafara rawa, hannunsa sai karkarwa yake yaji maganar akansu ne Wato jikoki
Cikin daure fuska Alhaji Baqir ya kalleshi "kai menene haka? Cigaba mana"
Muryar Adam na rawa Kamar ba namiji ba yaci gaba da karatun
"Duk mazan da suke cikin wannan family an mallaka wa kowa filin dazai gina,duk Wanda yayi aure acikin wadannan yara dazamu ambata, to lalle lalle ya tabbatar yasake wani auren yacika namu Burin
munyanke shawara tareda umarnin cewa Ilham 'yar gidan Basiru zata auri Aslam Dan Alhaji Baqir
Dida yar gidan Farida zata auri Fawaz yaron Alhaji Basiru
sannan Adam yaron Alhaji Baqir zai auri Diyana, yarinyar hajiya Farida
saikuma na qarshe takwarana Abubakar Wato Abba, zai auri Aisha yar gidan Alhaji Basiru tareda Nihla yarinyar Aisha "
Wannan dalilin ne yasa mukayi muku hani akan duk wani taro acikin family, na suna kona aure, saboda gagarumin taron dazaku hada na auren jikokinmu, muna yiwa kowa fatan alkhaairi "
Takardar ya ajiye, saboda jiri-jiri dayake gani 😃
Cikin fishi hajiya Na'ila ta miqe tsaye tace "wallahi bazata sa'buba, kowa yasan kaf family dinan yarana sunada hankali, babu wanda yakai Adam sanin Allah yace, annabi yace, 😃
amma arasa yarinyar da za'a liqa masa sai Diyana, yarinyar dakowa yasan tagama tambad'ewa atiti, shikuma Aslam wai Ilham, da rashin kunyar ta zaiji koda aikin gabansa "
Hajiya Farida cikin sauri itama tatashi tsaye ta maida wa hajiya Na'ila martani,
" ke saurara hajiya Na'ila, dakike cewa 'yata tagama tambadewa ambawa danki jinake yata Dida aka hada da qungurumin Mashayi 🙆🏻♀️, ni nace wani abu ne? Saike me bakin magana?"
Hajiya abia tayi shiru, tabbas taji haushin furucinsu akan yayanta, sai yau take dana sani akan halin Fawaz na shaye shaye, ta kalli hajiya Farida tace
" Farida Karki sake danganta min dana da sunan shaye shaye, "
Hajiya Farida tace " besha bane? Jinake Tun yana yaro kika gama lalata masa tarbiya, antashi an Auro mana baragurbi cikin family"
Gaba daya hall din ya kaure da surutu, da hayania, Aslam yayi shiru yana tunani, tayaya zai iya Rayuwar aure da qanwar Aysha? Yanzu kenan da ace tana raye ma Abba zata aura? Innalillah...wannan wacce mahaukaciyar wasiyya ce?
Momy kuwa hamdala take cikin ranta, shikkenan Abbanta zai auri nihila
Adam kuwa me karanta wasiyya yana ganin Ance Diyana zai aura yatuna lokacin data futo daga motar wani qato
Shikuwa Fawaz tunani yafara wai A'ina yakejin Dida ne? 🤔 Wacece Dida ne acikin yaran?
Daddy yayi shiru yana kallan kowa, matan sai hayaniya suke, Alhaji Baqir ne yatashi yadaka musu tsawa sannan suka nutsu kowa takoma wajan zamanta tazauna
Cikin ransa yafara magana, mata biyu!! amma wad'annan tsofaffin sunfi kowa cimasa mutunci, to aishi guda d'ayanma bayajin zai iya zama da ita, Dan haka yadago kansa Ahankali ya kalli Daddy yace
" I'am sorry Daddy, amma i can't marry her, Daddy bazan iya auren taba, inada wadda nakeso"
Gaban Nihla yayanke yafadi, ita yaya Abba yake cewa bazai aura ba agaban jama'a?
Lokaci daya hawaye suka wanke mata fuska, babu wanda yafado mata sai Diddi, tabbas sai kayi rashin uwa zakasan wani bangaren na rayuwa
Momy ta kalli Abba da sauri tanaso ta gaskata abinda kunnanta sukaji, ba ita kadai ba hatta Usman, Aliyu, farouq, shi suke kallo cikin tsananin mamaki
Daddy kansa maganar Abba tadaki ransa, amma saiya basar bai nuna ba ya kalli Abban yace "Amma kasan cewa yanda 'ya'yan wasu sukabi umarni bazai iyu d'anda nahaifa acikina yaqibiba ko? Tunda kace baka sonta tokaje kanemo son aduk inda yake, idan kuma kanakan bakanka har yanzu to kasa aranka cewa, qin auren Nihla dede yake da fitarka daga cikin Mazawaje family,sannan ni kaina nacireka acikin 'ya'yana, Zabi na gareka, koka amince kokuma daga nan katashi kafita baka cikin Mazawaje family "
Hall yasakeyin tsit, maganar Daddy ta daki kowa, tabbas yanda yayanke wannan hukunci akan d'ansa nacikin sa tofa bazaiji kunyar yankewa Dan wani ba
Babu musu Abba yamiqe, yafuto daga cikin Hall din
Momy tafara kuka wiwi, tace" Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, meyake shirin faruwa damune?"
Ta kalli Abba dayake dab dabarin cikin hall din ta qwala masa kira tace "Abba!!!"
Amma ko juyowa baiyiba
(wai ina labarin yusif ne,?🤔Yaje China ya maqale)
(tab bari na fece kar masu dukan Abba sudawo kaina 🤪}
Mutara zuwa gobe🙏🏻
Kada ku Manta da sharhi, Comments, dakuma share, please
Amnah El Yaqoub ✍️
[6/19, 10:55 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance & Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
15&16
Baqin ciki yakama Momy, batasan lokacin data rungume Nihla ba suna kuka tare, Nihla kukan abu uku takeyi, na farko yanda ta dauki Abba aranta, take jinsa na daban acikin zuciyarta Tun tana qarama, amma karshe ga irin abinda yamata, na biyu Diddi, ta tabbatar da ace tana raye, zataji Dan sauqi acikin zuciyarta, na uku mafi munin yanda yafadi kalmar baya sonta acikin bainar jama'ah
Momy kam Baqin ciki yahanata magana tama kasa Dagowa ta kalli idon kowa saboda abin kunyar da d'ansu ya aikata
Hajiya Farida bataji dadin abinda akaiwa Nihla ba, yanda take shiri da Mai Hakuri bataso wannan abu yafaru akan yarsa ba, kowa yasan cewa yaran Babu Wanda yakeso, amma dukda haka ai basuyi magana ba
Hajiya Abida mahaifiyar Ilham tayi shiru abun duniya yayi mata yawa, wannan abin takaici da yanzu harda Ayshanta za'ace baza'a iya aura ba
Ran Daddy yayi mutuqar baci akan abinda Abba yayi, haqiqa ya kunya tasu agaban mutane, ya nuna musu cewa ba'a isa dashi ba
Ahankali yadago kansa ya kalli al'umar dake gabansa yace "amatsayina na babba acikin wannan family daga ranar yau, na yankewa wannan yara ranar aure, nanda wata daya Mai zuwa"