← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 59

Sashe 30

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace "saboda ga gwamna ko shugaban qasa ko? Sai an sanar dasu zuwan ki, 🤣kema ai iyayen ki ne, kikirasu da kanki kifada musu, ni bazan saka baki akan zaman ki agidanba, kawai de bazan dauki abinda za'aci zarafin 'yataba"

Murmushi tayi tace "to Baba insha Allah, zankirasu"

Kallanta yayi yaga tanata murna, yasan kuma bazai wuce ace murnar ganin Momy bace, Dan zuwa yanzu kam yasan ai ta cire Abba aranta, daga nan yatashi yayi mata sallama yatafi

Washe gari saida tayi sallar azahar sannan ta shirya cikin doguwar riga Mai adon stones ajiki, sannan tayi rollinga tasaka wani shegen glass a'idonta, sai zuba qamshi take, idan ka kalleta saika sake waigawa, tayi masifar yin kyau, farar fatarta yaqara futowa sosai sai shining jikinta yake

Ya Yusif ne yakai ta Airport sai firar soyaiya suke abinsu gwanin sha'awa, har lokacin tashinsu yayi, sukai sallama yace zai kawo mata ziyara idan yasamu dama, da haka tashige cikin jirgin akaro na farko atarihin Rayuwar ta, wayarta tadauko zata kira Momy, kawai saita fasa, gara tayi mata surprice kawai

Ko awa daya basuyi ba, jirginsu yayi landing, tana futowa daga Airport din mutane suke ta Kallanta, daga ita sai yar qaramar truly dinta tanaja, tayi mutuqar birge kowa, Mai taxi ta tare tashiga tafada masa Inda zai kaita, acikin motar ma kafa daya ta dora kan daya, tana daddana waya, har sukazo bakin get din family house din Mazawaje

Sallamarsa tayi, ta tsaya ta qarewa Babban get din gidan kallo, duk an sassauya abubuwa dayawa, yau gata a Mazawaje family akaro na biyu

Tura get din tayi tashiga, iliya Maigadi yana zaune yanajin radio, taga ya kalleta yayi shiru Kamar besanta ba, cikin mamaki tace "iliya d'anmai qarfi baka ganeni bane?"

Kallanta yasake yi, yaji sunansa radau abakinta yace "Wacece? Bangane kiba wallahi, baquwa mukayi ne?"

Murmushi tayi ta cire glass din idonta tace "iliya nice Nihla fa"

Cikin sauri yatashi tsaye yace "kai kai kai, wai Nihla kece? Aini jinake wata balarabiyar ce wallahi, a a a a, masha Allah, sannu da zuwa, sannu sannu, kice yau munada manyan baqi agidan namu, kawo jakar taki, kawo, kawo"

Nihla tayi Murmushi tace "iliya kenan,"

Sannan tabashi jakar, suka nufi part din Momy, saida yakai mata jakar har cikin falo sannan yajuyo yana qara yimata sannu da zuwa, Nihla ta zube akan sabun kujerun falon da aka sake tace "wash Allah nah, gajiya"

Sannan tadaga murya tace "Momy!!! To futo 'yarki tazo"🤣

Kamar almara Momy Tajuyo Kamar muryar Nihla, amma sai taqi gaskatawa, mezai kawo Nihla kano yanzu? Kawai de kunnanta ne

Nihla tasake cewa "Momy!, koba kowane agidan?"

Dasauri Momy tafuto falon, taga Nihla kwance akan kujera ga jakar tanan agefe, qaraso wa tayi cikeda tsananin mamaki, Nihla na ganinta tatashi ta gudu taje ta rungumeta cikeda murna

Momy tadagota daga jikinta tana Kallanta tace " Nihla 'yata, yanzu Allah kece kika qara girma haka? Gaba daya kin sauya kamar ba Nihla ta tadaba"

Dariya tayi tace "Momy nice mana, wai meyasa kowa yake cewa na sauya ne? Momy girma naqara ne?"

"girman ma Nihla, kin qara kyau, Kamar balarabiya, mezakici adafa miki yanzu?"

Saida tayi farrrr da idonta sannan tace "Momy yanzu banajin yunwa, saide da daddare, but idan akwai cornflakes zansha kadan"

Momy ta lakace mata hanci, tace "Wato bakyason cin abinci Kamar da ko? Ni narasa ya'akayi ma kikai bul-bul dake masha Allah Babu wata rama Kamar da"

Dariya tayi, cikin ranta tace Anty Nadiya ce sirrin, afili kuwa sai tace "Momy bari nakai kayana daki"

Momy tace "a a Barshi, Adala zatazo takai miki, tashi Muje ki gaisa da sauran yan gidan"

Hannunta Nihla ta riqe Kamar wasu qawaye suka futo, kowanne part saida sukaje ta gaida kowa, kuma kowa sai nan-nan yake da'ita, kowa yayi murna da dawowar Nihla, saita zama wata abar sha'awa kowa Kallanta yake yanda ta sauya,Hajiya Farida maman su Diyana kuwa tana ganin Nihla taji tausayin Abba ya kamata 😢 🤣

Haka suka dawo part din Momy, Nihla ta dora kanta akan cinyar Momy tana bata labarin makaranta dakuma service din da aka turota

Suna wannan firar har la'asar tayi, Tatashi taje tayi wanka, tasaka riga da wando na jesy, (kayan ball) na mata, amma nata dogon wando ne Mai launin dark blue, Momy ce da kanta tahado mata cornflakes din, tace "to yata taso kisha, yauda kaina Zan baki"

Murmushi tayi tatashi, suka zauna a kafet din, Momy tafara bata, ita kuwa sai surutu take mata, Momy cikin ranta sai mamakin yanda Nihla ta sauya takeyi, kanta Babu dankwali hakan yasa dogon gashinta dayasha gyara kwanciya a bayanta

Adede lokacin yaturo falon nasu yashigo, yau kwanansa takwas baya qasar ma baki daya, saukarsa kenan

da dogon gashinta yafara tozali, kasancewar tabashi baya baiga fuskar ko Wacece ba, mamakin hakan yasa yaqame a tsaye abakin kofa, Wacece wannan Kamar ba 'yar hausawa ba kuma Momy tana feeding dinta?

Momy ce ta lura dashi takalleshi cikin murmushi tace "a a Abba, shigo mana"

Jin an ambaci sunansa yasa bugun zuciyarta ya sauya, ahankali tajuya ta kalli bakin kofar itama, lokaci d'aya Idanunsu yahade dana juna, cikin abinda baifi second ashirin ba tagama qare masa kallo, yau ne karon farko daga taba ganinsa azahiri sanye cikin kakinsu na Pilot Mai launin fari da baqi banda pic dinsa data gani awayar Anty Nadiya sanye da kayan , sosai kayan sukayi bala'in karbar jikinsa, yaqara girma, yaqara yin kyau Kamar ba shiba yasake zama babba tamkar wani cikakken magidanci, kawarda idonta tayi,ta karbi spoon din hannun Momy ta cigaba dashan cornflakes din ta, shikuwa kasa dauke idonsa yayi akanta, shin anya kuwa ita dince de agabansa? Inda ace baiyi mata kyakykyawan saniba Babu abinda zai hana yakasa ganeta, but ya'akai takoma haka? Dogon gashinta yasake kalla Kamar ba gashin bahaushiya ba, ahankali yaqaraso cikin falon cikin takun izza

Momy tace "Nihla ga yayanki yashigo fa, shima baya qasar yanzu yanzu yadawo, yaude ina cikin farin-ciki yarana duk sun dawo gabana"

Hankalin Nihla yana kan cup din gabanta, ko dago kanta batayi ba, bare yasaka ran zata kalleshi, kanta aqasa Kamar anyi mata dole tace "ina yini"

Ataqaice yace "lafiya"

Sannan yayi gaba, yajuyo yasake kallanta waiko zaiga ta kalleshi amma yaga gaba daya hankalinta ma baya kansa, shi wannan yarinyar zata gaisar asheqe Kamar ta samu sa'anta?

Momy kuwa tayi mamaki guda daya, mamakin daya kamata shine yanda Nihla taqi ambatar ko sunan Abba, da tasaba tanaji yarinyar tana ya Abba kaza, ya Abba kaza, duk da yana shareta bata fasa fadar sunansa ba, Kamar a bakinta aka rada mata sunan ya Abba, amma yau taga gaisuwar ma daqyar tayi 🤔

Dakinsa yashige yafada kan gado yana tunani, inaaa! Bazai iyuba, Sam bayason raini, Dan haka bazai dauki wannan ba, lumshe Idanunsa yayi, meyasa yake jin farin-ciki ne awani bangare na zuciyarsa?

(ko a film fad'an boss shine qarshe 🤪dafatan za'a min Comments 🙏🏻)

Amnah El Yaqoub ✍️
[7/3, 12:43 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

33&34

Nihla ta kalli Momy "Momy kibani wayarki nakira su Ilham, banda number kowa acikinsu"

Momy tace "wayarki tada tana nan a dakin naki, ki kunna saiki dauka, ai Babu wadda ta sauya number acikinsu, nima Bari nakira Daddynku dasu Usman nafada musu zuwanki"

Tace "to Momy" sannan tashige dakinta

Da daddare kuwa su ya Usman sukazo dukansu, dama Momy tasa Adala ta shirya musu abinci Mai kyau

Alokacin Nihla tasake wanka tasaka riga da siket na atamfa Mai launin Jan duhu, dinkin yayi mutuqar yimata kyau, siket din kuwa hips dinta yacikashi dam, daurin dankwali nede tayishi simple amma gashinta awaje yake daga baya

Babu Wanda bai rude ba, lokacin dasuka ganta, gaba dayansu suna zaune acikin qayatattun kujerun dakin, Adala kuma tana dauko abinci daga kitchen zuwa kan dining, firarsu suke cikeda farin-ciki but Abba kam baya saka musu baki, baya cewa um bare um um, asali ma waya ce ahannun sa yana danne-danne, yayinda yadora kafa daya kan daya

Farouq yace "Momy, yarki fa tagama rikicewa, gaba daya ta sauya kamar ba ita ba, ni sai yanzu nema nakejin naqara matowa, inba itaba sai rijiya" 🤪

Ahankali yadago kansa ya kalli farouq, amma Bece masa komai ba

Murmushi Nihla tayi, har dimple dinta yana lotsawa, tace "ya farouq bakada dama, aina fadama dakai za'ayi, tunda kaji sharadin"

Wannan karon ma tana fara magana Abba yadauke idonsa daga kan farouq yadawo dashi kanta, har yanzu de wannan dimple din nata yana nan, yayi tunanin zata kalleshi amma kwata kwata saiyaga ko kujerar dayake kai bata kalla ba

Aliyu yace "ai farouq, bazan baka qanwata ba, mijinda Nihla zata aura ai sai Wanda duniya tasan dashi"

Usman yace "Kamar ni kenan" 🤣

Gaba dayansu sukasa daria, Momy tace "Dinner is ready kutashi Muje kowa yaci abinci"

Usman da farouq da Aliyu gaba dayansu ajere suka zauna, Momy ma tazauna akusa da Usman, kujeru biyun dasukai saura kuwa na Abba ne da Nihla, hankalin ta kwance taja kujerar tazauna sannan tafara cin Abincin ta, shima Abba daya qaraso wajan yaga saura kujera daya ta kusa da Nihla, haka yaja Yazauna, idonsa akan wayarta data ajiye a gabanta, yana zama wani irin sihirtaccen qamshi yabugeshi, baisan lokacin daya lumshe idonsa ba yabude, kowa shiru yayi yana cin abinci, wayar Nihla tafara qara, kowa yazuba mata ido yana Kallanta, Abba yakai dubansa kan screen din wayar yaga ansa
❤my Yusif❤ harda alamar hert ajikin sunan, Nihla tasa hannu tasaka wayar a silent, idonsa ne yasauka akan kyawawan yatsun hannunta, dogaye gwanin sha'awa, janye idonsa yayi, Nihla kuwa ko a jikinta taci gaba dacin Abincin ta, ana jimawa ya Yusif yasake kira, tasake sakata a silent, akaro na uku ma yasake kira, ahankali ta miqe tsaye tace "Excuse me, zan amsa waya"

Tana fadar haka ta nufi hanyar dakinta, Hips dinta Abba yabi da kallo, anya kuwa yarinyar nan itace bawani abu take sakawa a jikinta ba? gashi sai yawo take tana fitarda gashinta waje kowa yana kallo, amma Momy tana gani ko magana bata taba yiba

Har suka gama cin Abincin Nihla tanacan tana waya, da dade tana shan wayarta dashi sannan tafuto sukai sallama dasu ya Aliyu

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Chapter 30 · 0% Book details