← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 59

Sashe 20

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan page din na'yan la'be ne🤪
kawai sonake yau kuma ku futo kuce wani abu

23&24

Yace "Momy me kike nufi?"

"A a, babu komai Abba, zanyi mata magana saita gyara"

Ajiye cup din yayi "no kibarta Momy, kawai de daga yau karta sake min"

Haka ya juya cikin dakinsa ransa duk ajagule, zama yayi yadauki wayarsa yafara kiran number Nadiya, but number busy, cikeda mamaki yakalli agogo "to Dawa take waya Awannan lokacin ?"

Babu me bashi amsa, Dan haka yayi wulli da wayar ya kwanta

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Har sha biyu suna zaune jugum jugum afalo, Aslam sai hamma yake yanaso yaje ya kwanta, gashi wannan yarinya ta hanashi sakat, tazo tasa shi agaba da wannan shegen towel din nata Wanda dashi ma gara Babu
Ahankali yatashi yayi dakinsa, tatashi tabishi, Bece mata komai ba yahaye gadonsa ya kwanta, kujerar datake dakin nasa tahau ta kwanta itama, saide atakure take
Yakalleta yace "kitashi kibarmin dakina"

Ilham kuwa tana jinsa tayi banza ta qyaleshi
Wai akan masifa ta sameta yake korarta, Hmm zata rama ne, da haka tayi addu'ah sannan tayi bacci, shikuwa kasa baccin yayi yazuba mata ido yana Kallanta dukda ta juya masa baya, daqyar yasamu yayi bacci bayan fama da juye juye dayake, idan Yarufe idonsa, surarta kawai yake gani

Tun kafin tatashi daga bacci asubar fari yatashi yaje toilet dinta ya cire lizard din sannan yatafi masallaci

❣️❣️❣️ ❣️ ❣️ ❣️

Yau daga makaranta gida yawuce, yadade agida sannan yakamo hanyar gidansa
Tun kafin yasako qafarsa cikin falon ya ganshi kaca-kaca, yariqe qugu ya tsaya yana qarewa falon kallo, fillow's din dake kan kujera duk wasu aqasa, matsawa yayi yaje wajan kayan kallo yasaka hannu yataba, yana duba hannunsa yaga qura

Daga murya yayi yafara qwala mata kira "maryam! Maryam!!"

Cikin sauri tafuto daga dakinta,fuskarta cikeda kwalliya, riga da wando ne a jikinta, rigar nan takamata kyam ajiki, wandon kuwa tacika abin ta, Dan qaramin mayafi ne a hannunta tana kokarin nad'ashi akanta tace "gani"

"yanzu maryam abinda kike acikin gidannan yadace kenan? Bakisan mukwana dake acikin gidannan kibudi baki kice Dani ina kwana ba, idan zaki fita unguwa bankai matsayin dazaki tambayeni ba,bakisan kidafawa mijinki abinci ba, now kalli gidannan, kina nema kibar min gida ya lalace, kalli, kalli Dan Allah cikin falon nan "

Yaqarasa magana yana nuna mata cikin falon

Kallansa tayi " yanzu ya Adam duk kokarin danake dannaga na zauna dakai lafiya baka gani? Auren nanfa baso nake ba, sannan kana maganar abinci aikai malami ne kasani, haqqinka ne kaci Dani sannan kashayar Dani, ni bazan iyaba!, bazan iyaba!! Bazan takura kaina ba, in tashi dasafe, inyi wanka, inyi kwalliya, inyi kokarin hadawa kaina abinci, sannan kuma inzo ingyarama gida, na maka girki, saboda samu ma inyi mopping,inturara gida da turaren wuta, saikace a novel? Aljanar inace nida Zan yi wannan aikin kullum? 🤣
To kaga ni gaskya ko agaban iyayena Babu me takuramin ehe! "

Tana fadar haka tajuya takoma cikin dakinta, jagwab Adam Yazauna akan kujera tareda dafe kansa 🤦🏻‍♂️maryam zata haukatashi

Yadade azaune sannan yatashi yatattare hannun rigarsa yadauki tsintsiya yafara share gidan, takan dakinsa yafara sannan kitchen, sai kuma falo, mopper yadauko ya goge falon tas, sannan ya goge kayan kallan yadauko qur'ani adaki yadawo falon yana karantawa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tunda taga ya Fawaz har gida yake shigowa da kayan maye yasaka acikin fridge ta shiga damuwa, ya Fawaz koshi ba dan'uwanta bane yakamata tafara nuna masa abinda yake ba daidai bane, balle ma shidin mijinta ne, haqqin kula dashi yana kanta
Jiya tatuno saida yagama qarewa fuskarta kallo sannan wai ta d'agashi tunda dama tasaba 🤣

Ahankali tatashi tashige cikin dakinsa, ta gyara masa dakin tas, ta lailaye masa gadon tsaf, fridge din dakin tabude kwalaben maganin maye dana mura gasunan birjik, shiru tayi tana tunani, tarasa mafita Dan haka tadau wayarta takira yayarta, bugu daya ta dauka tace "Diyana kinga dakin ya Fawaz nake gyara wa bakiga kayan maye ba, nikuma banaso yanasha wallahi, Yaya zanyi dasu ne?"

Diyana tace "um lalle Dida agaisheki, ke har gyaran dakinsa ma kike, tab!"

Dida tace "toya zanyi Diyana, mijina ne ko mahaukaci ne shi dole Zan kula dashi ahaka"

Batare da tunanin komai ba Diyana tace "kidebesu kizubar kawai"

Dida tace "to shikkenan nagode Diyana" daga haka takashe wayar, takwashe duka magungunan tafitar dasu waje ta tsiyayar dasu sannan tayi watsi da kwalaben
Tadawo ta goge fridge din, ta dauko lemuka a kitchen da ruwa tazuba masa su sannan tafuto daga dakin

Abinci taje tadafa musu bayan tagama tayi wanka tadawo falon tazauna tana game a wayarta
Ta dade azaune awajan sannan yashigo gidan, yau yayi mata sallama, cikin ladabi ta amsa masa, tace "a kawo ma abinci ne?"

Yatsina fuska yayi "no kibarshi kawai, ke kidena dafa abinci Ma Dani, kiyi rayuwarki kawai"

Batare data ce masa komai ba ta kwanta taci gaba da abin datake

Yana shiga dakin ya ganshi yasha gyara sai qamshi yake, zama yayi agefen gadon afili yace "wannan yarinyar da naci take wallahi"

Fridge dinsa yabude nan yaga Babu komai, cikin bacin rai yace "kan ubannan!!!"

Belt din jikinsa ya cire yafuto falon afusace, Dida tanayin game kawai sai Saukar belt din taji a jikinta, cikin sauri tatashi tana sosa wajan, be tausaya mata ba yaci gaba da dukanta, tatashi tana kuka sosai tana bashi hakuri, yana binta da duka tanayin baya har sukaje bangon falon ta tsugunna aqasa tana kuka sosai, cikin hucin bacin rai yace "ke Dan uwarki nizaki renawa hankali eh ? Okey wato saboda na sakar miki fuska acikin gidannan kina abinda kikaga dama shine zaki nemi ki takurawa rayuwa ta ko?, to bari kiji duk lokacin dana sake ajiye kayana cikin fridge tsautsayi yasa kika dauke min, saikin yabawa aya zaqin ta "
Yayi wulli da belt din awajan ya koma dakinsa, Dida kuwa kanta yana cikin qafafunta tana kuka, Dagowa tayi ta kalli jikinta, gefen hannunta harya shata

(Allah karabamu da mazaje masu dukan iyalinsu 🙏🏻)

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Nihla karatu yayi nisa, alhmdlh tafara kwantar da hankalinta, saide damuwarta daya ya Abba, yana nan daram acikin ranta, amma alqawarin data daukar wa kanta yana nan Babu shi Babu ita,fatanta daya tasamu miji nagari Wanda zai nuna mata soyaiyar dazatasa ta Manta da Abba kwata-kwata, tana fatan samun wannan mijin

Gefe daya kuma shaquwa Mai qarfi tashiga tsakaninta da abdallah, kullum suna tare, tana karatun ta cikin kwanciyar hankali, abdallah yazame mata tamkar aboki, gashi yanada abin dariya, idan suna tare dole nema saiya bata dariya, shiyasa take ganinsa Kamar qawanta, gashi duk abinda bata ganeba yana temaka sosai harsai tagane, fatarta kadai zaka kalla a yanzu kasan cewa lalle tasamu canji, Anty Nadiya tayi mata komai a rayuwa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Bayan tagama gasa jikinta tabawa megadi kudi yasiyo mata magani tasha sannan ta kwanta, amma hawaye take sharewa, kanta har ciwo yake saboda kuka, yakamata tabarwa yaya Fawaz gidansa, Tun ranar da aka kawota gidan nan tafara cin karo da mari, to tunda yafara duka bazai dainaba gara tafara tunanin barin gidan Tun wuri,kuma yazo ya kwanta a jikinta yace itace, bayan duka ga sharri, inaaaa! Da sake

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Yau agajiye yadawo gida,gashi ya Manta bai siyo abinci ba awaje, tsaki yasaki yafara qwala mata kira "Ilham"

Daga kitchen tafuto, ya kalleta daga ita sai wata qaramar riga da bata wuce gwiwarta ba
Ya Girgiza kai, yarinyar nan bazata dena halin ta ba, batada kunya, batasan shigar kamala 🤣
Yace "jeki kawomin abinci"

Babu musu tajuya takoma kitchen, Aslam yabita da kallan mamaki, yau shine yace wa Ilham tabashi abinci Babu musu Babu rashin kunya tajuya zata kawo masa? Lalle yau za'ayi ruwa da qanqara

Ilham kuwa tana shiga kitchen tazuba masa Abincin, sannan tad'ebo gishiri Mai uban yawa tazuba masa aciki, tasa spoon ta jujjuya Sanna tadauko takawo masa, zuciyarsa daya yadebi Abincin yakai bakinsa, lokaci daya ya yatsina fuska, gaba daya gishiri yahade masa baki, daqyar ya iya hadiyewa, yadauko Abincin yakawo mata gabanta ya ajiye, tadago kai ta kalleshi dariya ta nasan kamata, cikin fishi yace "Ashe ke zero ce bansaniba?"

Ran Ilham yabaci, ita ya Aslam zai kalla yace mata zero? Itama cikin bacin rai tace masa "To sannu 1"

Tas kakeji yadauketa da mari, yace "Ilham idan kinaji da rashin kunyar ki kiyi abinki ke kadai, tayaya Zan kashe kudi na kawo miki abinci gida na ajiye, banda damar dazaki dafamin, Sannan yanzu nace kikawo min abinci zaki zuba min gishiri aciki?to gashinan zauna tas saikin cinye shi"

Hawaye ne yazubo mata, tasa hannu tashare tana magana cikin kuka "Allah bazanci Abincin nanba"

Yace "nikuma kika sakamin naci namutu, baki damuba, zauna saikin cinye Abincin nan"

Haka Ilham tasa hannu acikin Abincin nan tanaci tana hawaye, fakar idonsa tayi tatafi dakinta dagudu tana kuka, Kallanta yayi yafara fada cikin ransa, haba yarinya sai Jan magana da rashin kunya, in banda yana mata kallan qanwar budurwarsa yau dasai ta cinye Abincin nan tas

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Futowa tayi tatafi dakinsa kanta tsaye, shi kansa yayi mamakin ganinta a dakin, saboda ba kulashi takeba, agefen gadon tazauna "yaya Adam inason kudi zanyi amfani dashi, banda kudi"

Kallanta yayi yace "banda shi"

"yanzu yaya Adam kaine zakace bakada kudi? Idan ban tambayeka kudi ba wazan tambaya?"

Yace "Allah masani"

Tace "Ok to sata zanje inyi insamu kenan?"

Yace "maryam koma menene kije kiyi, amma nide bazan dauki kudina nabaki kitafi yawon banza ba, kokuma kisa kati ki kira samari, qarya haram!"

"Ok haka kace?"

"yes haka nace maryam, kije kiyi duk abinda kikaga dama"

Tashi tayi tafuto tabar masa dakinsa
Tunani tafara maranta ciwo yake, A'ina zata samu kudin dazata siyo pad, shikuma besiyo mataba sannan yahanata kudin, haka takoma daki ta kwanta ga ciwo da takeji sosai, Tun tanaji kadan-kadan harta faraji dayawa, daga qarshe ma zazzabi me zafi Yarufe ta

Washe gari dasafe ya shirya zai tafi makaranta saboda yanada lacture, yayi kyau sosai cikin farin yadi sai qamshi yake
Har zai shiga Mota ya tuna yarinyar nanfa Tun jiya beji motsinta ba, Dan haka ya koma ciki kai tsaye yashiga dakinta, tozali yayi da ita akan gado tana cikin blanket amma karkarwar sanyi take

Cikin sauri ya qarasa wajanta yace "subhanallah... Maryam!"
Chapter 20 · 0% Book details