← Book details Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 59

Sashe 47

Dangi Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru tayi takasa bata amsa, mezatace mata? Saboda ance na auri danki nake kuka kome? Dan haka tayi shiru, Momy tasa hannu tafara bubbuga bayanta alamar rarrashi, haka tayi shiru amma cikin ranta wani kukan takeji tanaso tayi, Ilham tataso tace" kitashi mukoma can "

Babu musu tabi Ilham suka koma gefe sai Jan zuciya take, Ilham bata tambayeta dalilin kukan ba, tabarta tagama hucewa tukunna

Nihla tayi shiru tana tunani, ita kuma tata qaddarar kenan, sai anzo auren ta afasa, yanzu gashi shima yace ta auri Abba, hakan yana nufin za'a sake fasawa kenan akaro na biyu

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Washe gari Alhaji Basiru da Alhaji Baqir dakuma Daddy da Alhaji habib mijin hajiya Farida suka shirya sassafe suka nufi Abuja
Saukarsu keda wuya Alhaji Isma'iel da baba sukayi musu masauqi acikin falon nasu, baba sai mamaki yake irin wannan zuwan nasu

Saida suka gama gaishe gaishe sannan Daddy yadubi ma hakuri yace "Ibrahim wajan ka mukazo gaba dayanmu nan da qoqon bararmu, haqiqa munyi maka laifi abaya, kuma muna qara neman kuskure, ba kuma komai ne yasa nina aikata hakaba saidon kaunar yar'uwata Aisha dakuma abinda kuka haifa, Awannan lokacin kokadan banaso nayima magana akan Zan dauki Nihla natafi da ita, saboda nasan yanda kake jin mutuwar Aisha kaima bazaka so karabu da yarka ba, nikuma ina qaunar yarinyar, hakanne yasa nadauke ta muka tafi, maganar aure kuma da bamu sanar makaba wannan ma mun dauki laifin mu, amma maganar gaskiya itace banine nayanke wannan hukuncin ba, iyayen mune, bawai ikona bane hakan, amma kayi hakuri "

Baba yayi Murmushi yace"haba Alhaji, ai Babu komai, komai yariga yawuce, rannan ma kuwa Shima Abubakar yazo shida Aslam"

Mamaki yakama su Daddy, ashe su Abba sunyi hankali, Alhaji Baqir mahaifin Aslam yayi Murmushi cikin ransa yace shikkenan ma sun rage mana hanya, yadubi baba yace "ai Abubakar dinma bashida lafiya, yana kwance a asbiti yanzu haka, zuciya ce takeson yimasa ciwo, amma batakai ga farawar ba"

Alhaji Isma'iel yace "subhanallah... Subhnllh, kode shine yaron da Yusuf yake fadamin bashida lafiya?"

Baba yadubi Alhaji Isma'iel yace "A a yaushe Yusuf din yaje kano?"

Alhaji Isma'iel yace "toni jiya yazo yake min kuka waishi afada maka sun hakura da aure shida Nihla, saboda akwai wani dan'uwanta dayake rashin lafiya akanta, wai kada ya mutu a dalilin su, toni kuma ban dauki zancen nasa serious ba, tayaya kuna tareda yarinya zakace kunfasa, ban yarda da maganar tasaba, shiyasa ma ban yiwa mai hakuri maganar ba "

Alhaji Baqir yayi Murmushinsu na manya yace" wallahi shine, ai mungaisa dashi jiya, Yusuf kenan, Yusufa yaron kirki "🤣

Alhaji Basiru yayi gyaran murya yace" ai jikin nasama da sauqi, har yanzu de bai farfadoba,"

Baba ya Jinjina kansa yace " inafa lafiya kana cewa yaro har yanzu bai farfado ba "🤣

Alhaji Isma'iel Yace"Allah sarki, Allah yabashi lafiya, to amma ina ganin tunda yara sun fahimci juna harshi Yusuf din yayi jihadi, to ina ganin kawai ayi hakuri gaba daya tunda kowa ya fahimci kowa yanzu, sai adaura musu aurensu kawai, idan Allah yabashi lafiya duk wata bidi'ah da za'ayi suyi daga baya "

Farin ciki yakama Daddy, da kansa yasauko daga kan kujerar dasuke kai yafara yiwa Alhaji Isma'iel godia, Alhaji Isma'iel yace

" Babu komai ai matar mutum kabarinsa "

Alhaji Baqir yace" toni ina ganin, tunda abin yazo da haka, memakon Muje musake dawowa, kawai asiyo goro yanzu adaura, shikkenan anhuta "

Alhaji Isma'iel yace" A a akwai goro, Muje masallaci anemi liman yadaura musu auren, ni Zan zama waliyin Nihla "

Baba yakasa magana ganin irin karamcin da Alhaji Isma'iel yayi masa, haqiqa samun irinsu a yanzu sai antona

Gaba dayansu kuwa suka futo, kai tsaye masallacin unguwar sukaje aka kira liman, da maqocin Alhaji Isma'iel Wato baban Nadiya, Alhaji Baqir yaje banki da kansa yaciro kudi, yace shine zaiyi wa Abba waliyi, nan take kuwa aka daura musu aure akan sadaki nera dubu dari, aka danqawa baban ta sadakin, kowa aka bashi goro, suka yiwa limamin ihsani, sannan suka futo kowa zuciyarsa fes

Daga nan su Daddy sukayi wa su Alhaji Isma'iel godia, suka nufi Airport

Mamy da taji labarin abinda yafaru ta tausayawa Abba, saide wani bangaren na zuciyarta yana jimamin rabuwarta da Nihla, taso ace danta Yusuf yasameta, amma yaya za'ayi, matar mutum kabarinsa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Zuwan su kenan asbitin itada Dida da Ilham, Diyana bata zoba tana fama da cikin ta, Ilham sai fada take mata "kintashi kinsaka wa kanki damuwa ina dalili? Tunda shine yace zaiyi hakuri yaya zakiyi dashi, amma Tun jiya kidinga kuka,Yaya zakiyi da qaddarar da Allah yadora miki, kokuma zuwa zakiyi wajan Yusuf din kijashi ta qarfi, kuma Momy tayi miki Tambayar duniya kinqi bata amsa, yanzu idan taji saboda Yusuf yace yafasa aurenne saboda danta ya warke kike kuka ai ba zataji dadi ba, menene amfanin rashin mantuwa da ruqo Nihla "

Itama Dida tace"wallahi de kam, idan ma kina tunawa da lokacin da yace baya son ki ne agaban family ai yakamata ace zuwa yanzu kisan cewa saboda ke dinne ya kwanta jinya, idan mutane kowa da kowa yaji ya Abba yace baya sonki to yanzu kowa ya shaida ya Abba yadawo yana sonki, kuma gashi Akwance baisan wake kansa ba saboda ke, duk cikin mu waye yasamu irin wannan soyaiyar? Yakamata ki godewa Allah Nihla "

Nihla tayi shiru tana jin maganganun yan'uwanta, ahaka suka qaraso cikin asbitin da hannunsu dauke da abinci, kasancewar ba'a barin kowa yashiga dakin dayake shiyasa suka nemi waje suka zauna, sai Momy ce kawai acikin dakin nasa

Daddy ne yashigo asbitin fuskarsa dauke da farin-ciki Kamar ba dansa ne baida lafiya ba
Su Ilham suka gaida shi, sannan Nihla takira wayar Momy tafuto daga cikin dakin

Gaisawa sukai dasu Ilham suka qara yimata, yamai jiki sannan suka bata Abincin, Momy taji dadi sosai tayi musu godia sannan sukai mata sallama suka tafi, sukabar Nihla awajan

Tazauna tana duba wayar hannunta, Momy dake gefe itada Daddy tace "Alhaji yanaga kanata Fara'ah ne? Allah yasa lafiya"

Murmushi yayi yace "daga Abuja muke"

"Abuja kuma Alhaji, meyake faruwa"

Hannu yasa a aljihunsa yadauko goro yace "riqe wannan goron"

Momy ta karba tace "na menene Alhaji?"

Yace "goron daurin auren Takwarana ne shida yarki"

Momy ta zaro ido tare saka hannu abaki cikin mamaki, takai Kallanta wajan Nihla taga hankalinta yanakan waya
Tace "Alhaji da gaske kake?"

"da gaske nake, ga shaida nan kingani, shikkenan Abba sai hankali ya kwanta"

Momy tasaki ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah... Allah nagode ma, to Alhaji binka zanyi mutafi gida nayi wanka nahuta nima, tunda ga matar sa nan ita saita zauna ta dora daga ina na tsaya"

Daddy yayi Murmushi yace "to zo mutafi"

Abincin hannunta takai wa Nihla tace "Nihla riqe wannan Abincin, idan Allah yasa yau yafarka shikkenan sai kuci, akwai kayan Tea aciki, idan kuma bai farkaba sai kici, ni natafi gida sai munyi waya"

Mamaki yakama Nihla, tace "Momy gida kuma? Ba anan zaki kwana ba?"

Momy tace "a a, aina dena wannan zaman Nihla, yanzu kam saike" 🤣

Jikinta yayi wani iri, tayaya Momy zatace tazauna da ya Abba bayan tasan hakan bai kamata ba? Tace "to Momy kuma...."

Cikin sauri Momy ta katseta, "Nihla bafa Zan zauna ba, yau kema ki d'ana"

Tadubi Daddy tace "Alhaji Muje"
Har sun fara tafiya Tajuyo tace "yawwa Nihla Karki Manta likita yace kullum dasafe ana goge masa jikinsa da ruwa Mai Dan dumi, duk abinda kike buqata yana cikin dakin, idan baki ganiba saiki kirani"

Nihla ta kalli Momy takasa cewa komai, wai me Momy take nufi ne, ya za'ayi takama taba jikinsa bare har dasu goge jiki? 🤔

Momy kuwa bata jira amsar taba, suka tafi itada Daddy

Kuyi hakuri da wannan ba yawa

Sharhi please 🙏

Amnah El Yaqoub ✍🏻
[7/14, 2:19 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

53&54

Jiki a sanyaye tajuya cikin dakin, ahankali ta tura kofar dakin tashiga, idonta yasauka akansa, babu oxygen din ancire masa, amma fuskarsa tayi wani irin fari, Dan qaramin lips dinsa ta kalla duk yafara bushewa, gashin idonsa sun kwanta gwanin sha'awa

Kujerar dake gefen kansa tazauna ta ajiye Abincin, sannan tayi shiru tana tunanin irin wannan zaman jinya, ko yaushe zai farka? 🤔

Ya Yusuf ne yafado mata, Allah sarki, tunda sukai maganar rabuwa dashi basu sake waya ba, tana mamakin yanda lokaci daya yace zai sadaukar da soyaiyar ta ga ya Abba, bayan tasan ya Abba da kishi idan shine ba lalle ya'iya hakura da itaba

Haka tazauna shiru ita kadai a dakin, lalle idan hakane Momy tayi kokari, amma tarasa Inda Momy tasa gaba, tayaya zasu barta daki daya da ya Abba?

Ajiyar zuciya tayi tajuya ta kalleshi, saikuma ta dauke kanta cikin sauri Kamar tana tsoro karya kamata

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Mutanan gida kam, kowa labari ya sameshi, saboda su Alhaji Baqir kowa daya koma gida yafadawa iyalansa, Aslam Kamar yayi me saboda murna, Ilham kuwa bakinta Yaqi rufuwa, haka tadinga d'aga lil Abba sama tanayi masa wasa Yaron kuwa sai dariya yake shima Kamar yasan abinda ake

Aslam Yazauna yanemi number Yusuf domin su tattauna kuma yaqara yimasa godia amma kiran duniya ya Yusuf bai dagaba, haka ya hakura, ya shirya da daddare domin suje asbitin shida Ilham, Ilham tazuba musu abinci, sannan tahada wa Nihla wani maganin mata, tatafi mata dashi, cikin ranta tana cewa gara tafara bawa qawar tata Dan abubuwan nan tanasha, tunda auren yazo a qurarran lokaci, kuma tasan halin Nihla yanda batason ya Abba yanzu tsaf zataqi sha, Dan haka gara tana zuwa dashi tana bata tanasha a gabanta

Zuwan su asibitin kenan suka kira wayarta tafuto, fuskarta Babu yabo Babu fallasa, ya Aslam sai Fara'ah yake yace "Amarya kinsha qamshi"

Nihla bata kawo komai ba, tunda kowa yasan ansa mata rana Dan haka tace "na'am ya Aslam"

Yace "yaya marar lafiyar naki kuma"

"ya Aslam namu de"

Yayi Murmushi yace "A a, mun barmiki, keda dan'uwanki, kinga ai yanzu yazama naki"

"duk da haka de ya Aslam, kaima ai dan'uwanka ne"

Ilham ce tajata gefe tace "ke rabu dashi, zomu zauna"

Tabashi Abincin tace "ga Abincin nasu, ka shiga musu dashi ciki tunda zakaga jikin nasa"
Chapter 47 · 0% Book details