← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 133

Sashe 90

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ahankali yasa hannunshi yashiga laluba aljihun gefen riganshi kaman mai neman abu, waya yaciro yakira number Na Sani bayan ya dauka yace "anjima kazo Na Sani, ina neman ka" da sauri yace "to Yaya, dama inada niyyan zuwa zanma kawo Jamila taga Aneesan itama" ajiyan zuciya Baffa ya sauke yace "shikenan saikun tahon" marfin samiran dumamen shi yadauka yarufe, sanan yay shiru yakai kusan minti goma ahaka yana tunani sanan yamike tsaye yafita daga dakin.

Dakin Inna ya shiga tana zaune ita da yaran sunashan koko da kuli kuli, Mubarak kuma yanasha da biscuit data bashi idanunshi sunyi jajir sai sannu takemai, Inna ya kalla ganin babu Aneesa adakin yace "maisa baku kira Aneesa ba tazo kuyi karin kumalon tare?" cikin fushi kaman jira Inna take tace "sokake naje kokuma natura yarana ta farka min cikin su, inta illatamin yara hakuri fa kawai za'a bani bayan ancuceni, inhar yarinyar nan yanka mutane take wlh mai gida bazan iya zama da ita ba uwarta nachan gidan miji tanashan dadi ni ina nan ina fama da wahalan ta dakuma jinyan yara, iyakan gaskiyata nafadi maka dan naga ba Aneesan dana sani bane, Allah kadai yasan iyakan yawan abubuwan data koyo a gidan yari wanan Aneesan yar daba c........" hannu Baffa yadaga mata yana mata wani irin mugun kallo batare dayace mata komiba, yaransu sunriga sun tasa so ko kadan bayason suna fada da Inna agabansu banda hakama Inna mace ce mai kirki, matace ta gari, ga hakuri, yasan Aneesa ce tabata mata rai dan yana kallon yanda Aneesa tamata dazu dayace taje tai alwala, gashi kuma ta yanke Mubarak amma to Yaya zaiyi? Hanunka na rubewa ka yanke kayar ne? Aneesa yarshi ce, koyaya ta dawo dole ya so ta sanan ya kula da ita, shine waliyunta shine komi nata, dole yarike ta a hakan yana kuma mata addu'a Allah ya gyara mai ita, sanan Allah yafito mata da miji nagari. Ahankali ya zauna kan kujeran falon sanan ya kalli Ibrahim yace "jeka kiramini Aneesa Ibrahim" tashi Ibrahim yayi yafita, yaye labulen dakin Aneesan yayi da sauri tadago kanta ta kallai tana kan dadduma, tashi tayi da sauri tana dunkule hannu kaman wacce zatai dambe tace "lafiya kokazo ramamai ne?" daga sama zuwa kasa ya kalleta wani masifan haushin ta yakeji sabida yanda takeyi, tabe baki yayi yace "kinzaci kowa irinki ne mahaukaci eh? Nidai Baffa yace nazo nakiraki" yana fadin haka yajuya abinshi dawani irin mugun gudu Aneesa tafito daga dakin nata, tsugunnawa tayi tadau dutse gaban bakin kofanta ta daddage ta jefama Ibrahim din sai bayanshi tace "uban waye mahaukaci eh? Uwarka ce mahaukaciya baniba" wani irin juyowa Ibrahim yayi dutsen data jefamai ya bala'in shiganshi daurewa sosai yayi dan baiso yay ihu ko kuka ta rainashi kaman yanda Mubarak yamata dazu, dawani irin zuciya yayo kanta tana tsaye babu alamun guduwa tace "kataba ni kaga" baiyi wata wata ba ya wanka mata lafiyayyen mari mai kyau bai sauke hannunshi ba kaman ba ita ya maraba ta daddage ta kama hannunshi da duka hannayenta takai bakinta sai bakinta ta datse hakoranta akan fatarshi ta dannamai wani azababben cizo, dayan hannunshi yasa yana tura mata kai baya yana huci sabida tsaban azaban dayakeji amma ko gezau, jin tayago fatarshi da hakoranta tadago fatar sama kaman wata vampire yasa yay wani irin tsandara masifaffen ihu. "Abbbaaaaa!" jin ihun Ibrahim yasa daga Baffa, Inna da yaran suka zabura suka mike har ana rike rigen fita.
[15/04, 07:53] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

_✍🏿M Shakur_

6️⃣0️⃣

_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461, marasa banki can also send katin MTN to WhatsApp number na_

_duk wacce takarantamin littafi batare data biyaba wlh ban yafemata ba_

_duk wacce ta fitar min da book waje itama ban yafemata ba_
Chapter 90 · 0% Book details