← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 133

Sashe 61

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ahankali ta zauna kan gadonta rikeda plate din abincin tana murmushi tana juyawa tana tunanan kalaman Aliyu dake ratsa mata zuciya, tana wani irin karajin maimaicin kalaman shi a kunnuwanta, tabatan da akayi yasa tadago kanta da sauri Ihsan ne kaman zatai kuka tace "kinki kulani, ba Momma tacemin mun zama friends ba, kodai bakisona ne a matsayin kawarki" da sauri Aneesa ta girgiza kai tareda ajiye abincin agefe ta zare hijabin jikinta ta ijiye tace "laaaa, no bahaka bane ina sonki a matsayin kawata sosai ma" murmushi Ihsan tayi cikedajin dadi tana kallon jikinta, wani milk color shimi tasaka ya kwanta a jikinta bulbul ya bayyanar da kirjinta sosai kaman zasu yaga sufito, murmushi tayi tace "to yaushe zakizo gidanmu ki kwana?" ahankali Aneesa tace "nima bansaniba amma zan tambayi Ammi da Abba insun barni zanzo I promise" murmushi Ihsan tayi tace "to shikenan dau abincin ki to kici hudu takusa zaku koma islamiya kumako" gyadamata kai Aneesa tayi ta faracin abincin haka Ihsan keta mata hira babu labarin makarantan su dabata bataba harta cinye abincin hira takemata, kwalama Aneesa kira da Ammi tayi yasa ta amsa da sauri. "na'am Ammi" daga tachan Ammi tace "kin manta zaki islamiya ne ko" da sauri ta kalli agogo hudu saura minti biyar, da sauri Ihsan tace "la mun manta tashi da sauri ki shirya" tashi tayi ta shiga bayi tadauro alwala tazo tai sallan la'asar sanan tai wajen wardrobe dinta, wani dogon rigan yar kanti tadauka baki ne color tasaka, tazaro wani clean ironed mustard color hijabinta har kasa tasaka tasaka safa sanan tadauko wani dan babban jakanta ta kwashe littatafan da aka bata aciki ta rataya ta kalli Ihsan dake ta binta da kallo itadai tanason wanan Aneesan tarasa mesa, waya Aneesa ta mikamata tace "gashi samin number ki zamu dinga WhatsApp" sakamata number Ihsan tayi sanan tarakota suka fito afalo sukaga Ammi da Momma sai hira suke Momma tace "har anfito yan islamiya to adawo lafiya" Ameen tace tana kallon Ammi dake binta da kallo batare datace mata komiba, turobaki tayi a shagwabe tace "Ammi bazakimin addu'a ba" dariya Ihsan tayi tace "laaaa ashe kina shagwaba katuwa dake" murmushi kawai Ammi tayi tace "wanan Ihsan, aina kosa Allah yakaimu ranan aurenta nayi na tarkatata nakaita gidan mijinta nagaji" kaman zatai kuka tace "niba inda zani ina tare da Ammi na" dariya dukansu sukayi Ammi tace "bazaki wuce kitafi ba kin tsaya surutu sai kinyi latti, kyasha dukan latti, adawo lafiya to Allah kiyaye, banda wasa kuma adage da karatu" bye tama Ihsan sanan tawuce tabude kofa tafita daga dakin already taga har yara sun cika wurin motar ana jiran driver yazo yabude su shiga, ahankali take tafiya tana nufan parking space din kaman ance ta daga kai da Aliyu suka hada ido dake gaban shashin shi yana mata wani irin kallo yay folding hannunshi a kirji, dauke kai tayi kirjinta na bugawa tarasa mesa kirjinta ke bugawa duk inta ganshi kasa daurewa tayi tadan dagokai ta kallai sake hada ido sukayi har lokacin itayake kallo kaman zai cinyeta da idanu, samin kanta tayi da dagamai hannu kaman wata yar koyo taimai waving hand din alamun bye da sauri ta kalli hannun nata kaman ma batasan lokacin data dagashi ba, dan murmushi yayi tareda lumshe ido yabude su ahankali yana kallonta ahankali yay waving nata back irin waving dinan na yaron dabayason maman shi tafita, dauke kai tayi da sauri tadena kallonshi dan hakanan taji yawani irin bata tausayi kaman zuciyanta da nashi na communicating, kaman zuciyanshi nace mata karki tafi kidawo ki zauna dani.

Karasawa wajen motan tayi har direba yabude yaran duk sun shiga Hajar ne kadai agaban motan, wani matsiyacin kallo tama Aneesan tace "gasu agola nan anzo" daidai Aneesa takaraso wajen Rauda dake cikin motan dan ciwon cikin yasaketa sosai yanzu tace "kai Anty Hajar wlh babu kyau fa" ta kalli Aneesa datai kaman batajisu ba tasakin mata murmushi tace "shigo ki zauna Aneesa" murmushi itama tamata dan sai yanzu ne tagane Rauda itace yarinyan data taimaka ranan data fara ganin Aliyu sarkin kallo sai kallonta yake kaman baitaba ganintaba, shiga cikin motan tayi ta zauna kusada Rauda, Hajar ta shigo itama sanan direba yarufe kofan yakoma gaba ya shiga yaja.

Ahankali Rauda tasa hannunta takarbi hannun Aneesa data danyi wani zanen lalle ta around kumbunan ta tace "wow Aneesa wanan wani irin zanen lalle ne? Bbu kodaya a hannunki saita wurin yatsun ki it really looks nice, waya miki ya bala'in burgeni, waya miki?" murmushi Aneesa tayi tana kallon yatsun nata zanen datayi ne da bikin Ammi saitama Ammi kuma lalli mai kyau, ahankali tace "ninayi" "iyye kin iya lalle ne daman?" gyadamata kai tayi tace "na iya, kinaso namiki?" da sauri Rauda ta gyada mata kai tace "inaso mana, sosai ma" ahankali Aneesa tace "shikenan duk randa kika shirya zan miki wanda ma yafi wanan kyau" washe baki Rauda tayi tace "nagode, Awani aji aka saki dazu a hadda?" ahankali tace "aji hudu, islamiya ma aji hudu" bangaje mata kafada Rauda tayi cikeda jin dadi hira irin na kawayen nan tace "iyye ajinmu daya ashe, nima dazu dasafe cikina keta ciwo saisa banjeba wlh" ahankali Aneesa tace "sorry Allah ya sawake" cikeda damuwa Rauda tace "kema kinayin ciwon ciki idan zakiyi?" gyadamata kai Aneesa tayi batare datai magana ba she's not just comfortable sabida Hajar dake wurin, dan tana ganin yanda Hajar ke hararanta itada Raudan kaman ta bubbuge su, cikeda damuwa itama Rauda tace "sannu kinji Aneesa, ance inkai aure yana denawa" "dalla malama kimana shiru ko kina maganan iskanci agaban yara" Hajar tafada cikeda masifa, cikin tsiwa Rauda tace "to wai me ruwanki dani Anty Hajar, yaran sunsam menake cewa ne, kinamin wani ihu saikace nayi dake" ta harari gefen side din Hajar din, murmushi Aneesa tayi hakan yakara harzuka Hajar tace "dan ubanki nikekema rashin kunya?" cikeda rashin kunya Rauda tace "karki kara zaginmin uba nidai, Dady na nagida yana hutawa abinshi kina duramai zagi, kuma ai badake nakeba daga ina firana da kawata saikiyi ta zagina, dakenayi? Neman tsokana kawai" kwashe wa da dariya yaran motan sukayi, wani mugun kallo Hajar tamusu hakan yasa at ukai shiru, Hajar tai kwafa tace "zamu koma gida kaman Mama taji komi" dauke kai Rauda tayi tacigaba da hira ta da Aneesa batakara cemata komiba harsuka kai makaranta suka tafi ajinsu a binsu.

***

Wuraren magrib suka shigo gidan, derevan su yay parking yafito tareda zagayowa yazo yabude musu, saukowa sukayi Rauda ta dubi Aneesa data sauko bayan ita tace "saida safe ki gaishemin da Mummy, gobe zanzo na gaisheta kinji, bari naje part din Ya Aliy...." fizgan hannunta Hajar tayi kaman tafizgo barauniya tace "dan ubanki bazaki ba, ba Mama tahanaki zuwa bangaren shiba" cikin tsananin jin haushi Rauda tace "wai me haka Anty Hajar, wlh kisakeni kona hadaki da Dady me ruwanki dani sai samin ido kike kina sauraron conversation dina" cikin fushi Hajar tadunkule hannu ta sakin mata mugun dundun abaya da har Aneesa saida tajishi har cikin ranta sabida karan dayayi dumm! wani irin ihu Rauda tasaki kaman zata fasa gidan tai kasa tana bankarewa daidai Aliyu ya shigo gidan daga masallaci, rike ciki Rauda tayi dan har cikinta taji dundun tasaki wani irin mugun kuka tana kama cikinta, kaman Aneesa zatai kuka ta kalli Hajar dake huci kaman wata kumurcewatu😎 tace "me tamiki zaki mata wanan dukan bayan kinsan cikinta naciwo" da yatsa Hajar ta nunata tace "ke kalleni nan am 25 niba tsaran wasan ki bace, ba ruwanki idan nida kanwata na fada agol...." wani irin wawan mari da aka dauketa dashi yasa takasa karasa kalman dazata fadi tadago idanunta da sukai mata dishi dinshi tsabagen zafin marin tana sosa wurin ta kalli wanda ya mareta Aliyu ne yana sanye dawata white riga mai dark blue short hands sai dogon black jean dayasaka kamshin turaren shi yabi yacika wurin, hanunshi yadaura kan wandonshi yana kwanto belt dinshi dama bala'in haushin ta yakeji tun ture Aneesa datayi dazu tafadi, cikeda rashin kunya Hajar ta kallai tana ganin belt din dayake shirin kwancewa ita tafi karfin tagudu tace "wlh karma kasake kayi gigin ciro belt dinan kace zaka dakeni dashi agaban kannina kajamin raini agaban yaran da aka haifesu jiya, meruwana dakai nasan kane shiga shara ba shanu, wlh ka zaulamin belt dinan saina hadaka da Mama na tafito ta ramamin mugu kawai" wani irin zuciyane Aliyu yaji tarufe shi ya tsani rashin kunya, ahankali Aneesa ta saukar da kanta kasa jitake kaman tarufe Hajar da shegen duka yanda takema Aliyu rashin kunyan nan harda zagi.
Chapter 61 · 0% Book details