← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 133

Sashe 59

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Gabaki tayi tayi loosing control bama tasan metakeyiba kokarin tashi take takasa, kalaman shi nada wani irin asirtaccen power akanta data kasa fassawara, ganin yanda takeyi takasa tashi jikinta sai rawa yake yasa cikin wani low voice yana kallon fuskarta yace "in dagaki wife?" ko kallonshi batayiba saima wani karfi dataji yazo mata ta mike tsaye da kyar daidai lokacin Dady yabude kofan flat din Ammi yafito, wani irin murmushi tayi tajuyo ta kalli Aliyun dake kallonta tace "kagani ko zakajama kanka, ga Abba nanan yafito yau sunanka sorry banga abinda zai hana Abba na karya kulleka ba, bazaka tashi katafi ba" make mata kafada yayi a shagwabe yace "uhm'uh jiran shi nake yazo yabani auren ki inba hakaba zan mutu" dauke kai tayi da sauri ita yanda yakemata shgawaba ma wani bambaran yake mata but she must admit he looks damn handsome idan yanayin, harara ta watsa mai tace "chab Allah kyauta na aureka, huu'um bari Abba na yazo nagayashi dakai kaga abinda zai faru" tai kwafa tajuya tai wurin Dady dake tahowa wurin su da sauri yana kallon Aliyu da kafafunshi ke kasa kaman wanda akasa punishment, wurin Dady tayi kafinma tai magana Dady da hankalinshi gabaki daya kekan Aliyu yace "wat are you doing haka Son akasa? Eh Gadanga na menene?" da sauri yayi wurin Aliyu yana maganan, dagoshi yayi yanabin jikinshi da kallo tareda kakkabe mai guwiwan farin wandon shaddan shi dayadan yi datti kadan dan gidan fesfes ne yace "me kake yi akasa haka?" murmushi yayi batare dayace komiba yanuna Aneesa data tsaya turus tana kallon ikon Allah zatakaima Abba karan Aliyu taga kuma yanacemai Son, ahankali yace "Aneesa ne tafadi akasa Dadd!" yawani irin fadan Dad din da karfi dayasa Aneesa tadago kai ta kallai suka hada ido yamata wani shegen kallo mai tafiya da zuciyan mace, juyowa Dady yayi ya kalli Aneesa yana sakin Aliyu cikeda damuwa yace "subhanallahi garin yaya kika fadi Aneesa?" murmushi takakalo tana kakkabe kumatun ta da hannu tama rasa me zatace da bakinta yabushe tace "ahhh, ummm Abba, dama littatafan da aka banine sukamin yawa a hannu banje da jakaba shine nai tuntube nafadi" cikeda tausayinta Dady yace "sorry bakiji ciwo bako?" gyadamai kai tayi ahankali, yace "okay ga yayanki nan" yajuya ya kalli Aliyu yace "kai kuma tayata kwashe littafan ka kaimata daki kadawo wurin Nafisa ka barta ita kadai" yay maganan yana kallon Nafisa dayaga tana zaune kan kujera a bukka tana kallonsu, yace "akwai wanda zangani awaje am coming" yay hanyar gate, ahankali Aliyu ke kwashe books din yana kallon fuskanta yana murmushi yace "mai Abba" da sauri tarufe fuskanta da hijabi cikeda kunyan abinda tayi, fitowa daga bukkan Nafisa tai zuciyanta namata zafi ganin yanda Aliyu yama manta da ita, taya za'ayi tazo wurinshi amma baida lokacin ta, tana tafiya takalmin ta na kara kwas kwas kwas hakan yaja hankalin Aneesa yasa ta dago kai ta kalli direction din, wata kyakyawan yarinya daga gani zata girmeta tana sanye dawani hadadden lace ne tagani ke karasowa inda suke, daidai inda Aliyu yake a tsugunne yana kwasan books din Aneesa ne ta tsaya akanshi tadan kalli Aneesa dake binta da kallo, yatsine fuska tayi kaman taga kashi ta kalli Aliyun cikin muryanta nayan gayu tace "baby leave the parking of the books for her, tana tsaye kana kwashe mata littatafai kaman wani dan aikinta" dagokai ahankali Aliyu yayi ya kalleta batare dayace komiba yadau last book din kasan ya mike tsaye ahankali yajuya zaiyi wurin Aneesa kaman baimasan anamai maganaba, cikin jin haushi ganin iskancin dayake mata Nafisa tace "am talking to you fa Aliyu kakuma shareni, kan yarinyar nan kake shareni, who is she by the way? Ba Rauda bace ba kuma Hajar bace who is she, banma santa ba I know all the girls in this house, kabar mata book dinta muje muyi hiranmu" wani irin haushi da bakin ciki Aneesa taji yatokare mata wuya batasan lokacin data juya azuciye tai hanyar flat dinsu ba, juyowa Aliyu yayi ranshi abace yama Nafisan dake bayanshi dab dashi kaman zata shige jikinshi wani irin mugun kallo yace "you see that girl" yanuna mata Aneesa dake kokarin bude kofar flat dinsu yace "wanan zuciyan dakike gani" yanuna mata zuciya shi da hannu yana kallon fuskanta yace "my heart beats for her only, Only Her! She occupy every single space aciki babu ragowan waje dazan iya sakala ki Nafisa, I can't love mata biyu, she's the definition of the woman I want in my life, so goodbye and thanks for the ziyara bani nakiraki ba daman, Pops nawaje" yajuya yay hanyar flat din Ammi yana tafiyan nan cikeda isa.

_not edited_

Wani irin kukane Nafisa taji zaizo mata da sauri tabi bayan shi hanunshi tarike gam hakan yasa Aliyu ya tsaya chak zagayowa tayi ta gabanshi bakinta na rawa tana kallon fuskarshi kaman zatai kuka tace "please karkamin haka Aliyu cus I love you so much from the first time I set my eyes on you" dan yatsine fuska yayi yace "hardlock, nima from the first time I set my eyes on you naji bakimin ba, excuse me my hand" yanuna mata hanunshi data rike ahankali tasaki hannun yajuya yabude kofan flat dinsu Ammi ya shiga tabi bayanshi da kallo kafin ta kwasa da gudu tai flat dinsu maman Rauda fadawa dakin tayi daga Mama sai Hajar afalo tanacin white rice a plate fadawa jikin Mama tayi tasaki kuka sosai arude mama tace "subhanallahi, ke lafiya Nafisa zaki shigo gida da kuka kaman wacce akama rasuwa, minene?" cikin kuka tace "Mama Aliyu yace bayasona wai" daure fuska Mama tayi tace "wani Aliyun dai tukunna" cikin kuka tace "na gidan nan" tsaki daga Mama har Rauda sukayi atare Mama ta turata tace "uban me ya hadaki da Aliyu dama kinsan shine" girgizama Mama kai tayi tace "Dady yazo gidanmu wurin baba ranan shine yace nazo naga Aliyu innaumai ahada auren mu, wlh ina ganinshi yau naji ina sonshi sosai kuma wai bayasona" tsaki Mama takaraja tace "Allah na sonki ne yasa yace miki haka, me zakiyi da miji a matsayin Aliyu? Yaron daya rako maza duniya kina ganinshi haka koke a matsayin ki na mace kin fushi karfi, inda nabar Hajar tsaf zata iyamai lilis billahillazi, ki gujema kanki Aliyu ina miki fada, bari kiga neje nadubo Rauda da ciki kota tashi ga kawarki nan zata fadamiki waye Aliyun in kunne yaji ganganjiki ya tsira idan ma bakiji ba mamanki zan kira wlh" tai maganan tana tafiya.
Chapter 59 · 0% Book details