Sashe 106
Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kallon Aneesah mai Martaba yayi anatse yace "haka maganganun shi yake Fateemah?" gyadama mai Martaba kai tayi ahankali tace "eh hakane" shiru Mai Martaba yayi yana kallonsu, a ido kadai zaka gane irin son da Aliyu yakema yarinyar, shiru yadanyi sanan yafara jawabi. "Aliyu karkai tunani dan akwai kyakkyawan alaka tsakanina da mahaifinka zaka iya kawomin komi na dauka a'a sainai bincike, amatsayina na sarki inada ikon na aurar da yara irinku wayanda suke son juna tsakani ga Allah amma sabida wata matsala ko gaba dake tsakanin iyayensu da rashin jituwa yasa suka hana auren to a irin wanan case din, yaran kan iya kawo kansu gareni na wakilce su nakira shaidu na dauramusu aure abisa sunna, Fateema tambayoyin dazan miki yanzu shine zasusa na aurar daku dan haka kibani amsa tsakanin ki ga Allah, abinda kikeso shizan miki bazan taba miki doleba kinajina" gyadamai kai tayi ahankali tana goge hawaye, shiru Mai Martaba yayi yana jiran tasami natsuwa, wajen minti biyar yabata sanan yace "Fateema Bintu" ahankali tace "Na'am Mai Martaba" anatse yace "inaso ki gayamin tsakanin ki ga Allah, wanda zaki aura yau kina sonshi koko mahaifiyarki da Baffan kine sukace saikin aureshi? Kifadi mani gaskiya" hawayen daya zubo mata ta share, ahankali tace "nima bansani ba ko ina sonshi ko bana sonshi, amma Ammi na na sonshi tace na aureshi" shiru mai Martaba yayi yana kallonta, yay kusan minti biyu ahaka sanan yace "wanan karan ma baniso kimini karya kaman yanda kika amsamini tambayata ta farko haka nakeso ki amsamini ta biyun nan, tambayoyi uku kacal zan miki, me mahaifiyarki tace miki game da Aliyu?" shiru tayi tasa hannu ta share hawayen ta kafin cikin muryan kuka tace "ta...tace" tadanyi shiru kafin ahankali tace "tace inhar ita ta haifeni na manta da Aliyu arayuwata, zata nuna musu nima y'a ce kaman kowa kuma abin so, dan haka inhar ni yar halak ce babu abinda zanyi da dandan wanda yakaini gidan yari" takarashe maganan tana goge hawaye muryanta na rawa sosai, ahankali Aliyu ya lumshe ido he's so hurt kaman zai mutu yakeji, shiru Mai Martaba yayi yana kallonta duk tambayoyin daya mata na tattare da hikima, saida yabari ta natsu sanan yace "sai tambayata na karshe Fateema, inaso kigayamin tsakanin ki da Allah, Fateema kinason Aliyu?" da sauri tadago kanta ta kalli Mai Martaba ido da ido, anatse batare daya bari ta janye idanunta daga kanshi ba yace "karkimin karya, kinason Aliyu ko bakison shi" wani irin rawa kirjinta yafara kaman yanda na Aliyu ke dukan biyar biyar yana bala'in tsoron amsar dazata bayar, lumshe ido Aneesah tayi maganan ganun Ammi nadawo mata _"kicire Aliyu daga ranki, ki manta dashi, inhar nina haifeki keyar halak ce ki manta da Aliyu, baki ba Aliyu Aneesah, me zakiyi da yaron wanda yakaiki gidan yari"_ bude idanunta tayi ta kalli Mai Martaba tace "ba.....banason shi!" ji Aliyu yayi kaman an katsamai zuciya daga asalin jijiyan dake rike da ita tana lilo bayama jin kanshi, kallonta Mai Martaba yayi yanda tarufe fuska da hijabi jikinta na rawa sosai kana ganinta zakasan kuka takeyi, dauke kai Mai Martaba yayi ya kalli Aliyu dake gefenta yace "kaji amsanta ko Aliyu dan haka bazan taba iya auran da daya bayason dayaba sai in duka biyun keson junansu dan haka katashi katafi ita zansa amaidata gida iyayen ta suganta a daura mata aure, tashi katafi Aliyu" ahankali Aliyu yasa hannu yadafa center carpet din dayake zaune idanunshi nawani irin juyawa da kyar ya iya mikewa tsaye kara karfin kukanta Aneesah tayi sosai jikinta na bari, ahankali Aliyu yajuya yadaga kafa da kyar yay taku daya Aneesah nawani irin kuka da karfi, daga kafa yayi ahankali yay taku na biyu idanunshi na neman rufewa yana hanasu, taku na uku yadaga kafa zaiyi idanun suka rufe ruf yawani yanke jiki yazube asume arude Aneesah ta janye hijabin daga fuskarta ta waigo jin karan dataji, da sauri fadawan dake wajen suka zabura zasukai doki da hannu mai Martaba yamusu alamu karwanda yaje, wani irin kyafkyafta ido Aneesah tayi tana kallonshi ganin dai shine zube akasa asume yasa dawani irin gudu tamike. "Ya Aliyuuuuu" tsugunnawa tayi akanshi da sauri tasa hannu tajuyo dashi tana kuka sosai, ta bubbuga kirjinshi. "Ya Aliyu me haka? Katashi, Ya Aliyu dan Allah karka mutu kabarni?" arude tace "suma" wawwigawa tashiga yi ahaukace bottle water data hango agaban mai Martaba yasa ta tashi da gudu bamatasan inda kanta yakeba taje gaban mai Martaba tazuri ruwan tadawo da gudu tana kuka tabude bottle din ruwan ta yayyafa mai a fuska tana kuka sosai, ganin bai ko motsi ba yasa tasa hannuta kan fuskarshi tana wani irin sharemai ruwan fuskan tana kuka sosai tace "Ya Aliyun dan Allah katashi wlh ina sonka, ina sonka Ya Aliyuna, I love you so much wlh" ganin ko motsi baiyiba yasa tadaura fuskarta kan fuskarshi tana wani irin kuka mai tsumma rai hawayen ta na gangarawa suna sauka kan fuskarshi tace "Ya Aliyu dan Allah katashi, I love you so much, babu soyayyar data isa ta shigo TSAKANKANIN SOYAYYAN mu, I believe you, am yours Ya Aliyu na, wake up" tafashe da kuka sosai, dan motsin dataji yayi yasa tadago kanta ta kallai arude tareda kamo hannunshi tarike gam tace "Aliyu, am here wake up, inasonka kaji be stay with me" bude jajayen idanunshi dasuka kankance yayi yadaura akanta, fuskarshi tai cupping da hannayenta dasuka sha lalle sosai tana wani irin kuka ta gyadamai kai tace "yes I love you so much" hannunshi da baida karfi sosai yadaga yakai yatsar shi ahankali yashare kwallan datakeyi yana girgixa mata kai alamun tadena kuka, murmushi kuka tayi hawaye na zubowa ta gyadamai kai da sauri tace "okay bazan kara kukan ba" wani irin murmushi mai Martaba yayi ya kalli kunyangin wajen yace "adau Fateema akai cikin gida" ya kalli sarkin gida yace "akira likitan Mai Martaba sarkin gida, sannan akira jama'a yanzun nan suzo su shaida daurin aure tsakanin Aliyu da Fateema" da sauri kunyangin da mai Martaba ya tura suka karasa inda Aliyu da Aneesa suke suka daga ta sukace muje cikin gida a shiryaki za'a daura muku aure, ahankali ta share hawaye tana waigen Aliyu dake kallonta da idanunshi dasuka kasa buduwa duka, daga Aliyu fadawan sukayi aka kaishi kusada mai Martaba, fadawa da duka ma'aikatan gidan Mai Martaba suka cika falon danya bada izini akira kowa nan mai Martaba yadauka aure tsakanin Aliyu da Aneesah akan sadaki dubu dari dashi mai Martaba yabiya mai, wani irin ajiyan zuciya kawai Aliyu ke saukewa kafin hawaye su shiga saukowa daga idanunshi he just can't believe he's now Aneesah husband, wani irin nishi daya fara yasa Mai Martaba yace adaukeshi ayi chan wani kebantaccen flat da bakin Mai Martaba masu mahimmanci ne yakesawa akai wajen yasa aka kaishi daidai likita ya iso aka shiga dubashi, dubashi likita yayi tsaf sanan yamai allura bayan yama mai Martaba bayanin ciwon zuciyane da kuma tsantsan damuwa, saikuma zazzabi dan ruwa ya dakeshi amma wanan alluran zai saukar dashi, zai dawo da daddare yazo dubashi, godiya mai Martaba yamai sanan yatura kuyangi yace "ace in angama shirya amarya akawota bangaren mijinta".
_duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafeba, in kinason book dinan, chat me up 07012181461_
[23/04, 08:19] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
7️⃣1️⃣
_how to pay_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to my watsap number sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa bank zaku iya turo katin MTN_
_duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafeba, in kinason book dinan, chat me up 07012181461_
[23/04, 08:19] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
7️⃣1️⃣
_how to pay_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to my watsap number sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa bank zaku iya turo katin MTN_