← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 133

Sashe 105

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Harsuka kai gidan sarkin zazzau Aneesah kuka take, dogarawa ne suka tare motarsu agaban Gate din shiga cikin gida hakan yasa yay wining glass down, dogarin dake sanye da jan malummalum ne yazo yana leka motar yace "kai samari wakake nema kanada appointment ne koko bakasan gidan sarki mai daraja kake ba?" lumshe ido yayi ahankali sanan yabude, ahankali yace "acema mai Martaba Aliyu Ibrahim Muhammad ne, dan gidan senate president of Nigeria" yafada authoritatively, tsayawa chak dogarin yayi yana kallonshi kafin da sauri yace "gyara parking bari ashiga asanar dashi" yay maza yajuya daya daga cikin dogaran dasunkai goma awajen yaje yasama yamai magana a kunne da sauri dogarin yay cikin gida, parking Aliyu yayi agefe yanajin yanda take kuka har lokacin batare data dago kanshi ba dudda kukan natabamai zuciya amma baice komiba, lumshe ido yayi ya jingina da kujera ko kadan baida lafiya, almost 15min suna ahaka yaji anyi knocking tinted glass din motar nashi yaja glass din kasa, cikeda girmama wa dogarin haryana dan dukawa yace "angaishe ka yaron manya jikan manya, dan gidan hutu marika nijeriya kasarmu, Mai Martaba yace amaka iso zuwa fada, shigo da motar" kunna motar Aliyu yayi ahankali yaja motar cikin gidan sarkin, gidan kaman wata kasa tsabagen kyau da girma, parking yayi a inda ake parking yabude mota yafito dogarin na jiransu daga gefe, zagayowa ta inda Aneesah take yayi yabude kofar har lokacin kanta akasa, ahankali ya tsugunna ta wurin murya chan kasa ta yanda dagashi zai ita zasuji yace "tashi mu shiga ciki if not I will carry you a kafada na wlh" yitayi kaman batajishi ba hakan yasa yace "okay" tashi yayi ahankali tsaye yana tattare hannun riganshi yadaura hannunshi daya kan bayanta daya tawajen kafafunta zai dauketa da sauri ta tashi tana goge hawaye tana hararanshi da idanunta dasukai jajir duk hawaye yabata kwaliyan da akamata tace "wlh katabani saina wanka maka mari" murmushi yayi ahankali murya chan kasa yace "okay let's go in bakiso" fitowa daga motan tayi azuciye kaman zata bugeshi kamshin datake yi yawani bugi fuskarshi ahankali yamaida kofar yarufe yana binta da kallo, yakaraso inda take tsaye hannunshi yamika ahankali yakama hannunta ya rike ya kalli dogarin dake jiransu yace "muje" bugemai hannu tayi cikin kuka sosai amma yaki sakinta, ganin tafaramai gardama zatamai rashin kunya yasa yace "wlh zan dagaki, let's go" binshi tayi tana goge kwalla har aka kaisu durmemen fadan sarki dayaji kayan adon sarauta, wasu fadawa ne aciki, da kuyangu saikuma Sarkin Zazzau daya manyanta sosai danya tsufa tukup dake zaune kan kujeran sarauta yana kallonsu ga wasu bayi guda biyu dakemai fifita, faduwa kasa dogarin yayi yace "taakawanka lafiya sarkina sarkin zazzagawa, sarkin sarakuna, gashinan anshigo dashi" da kai sarki yamai alamu daya tafi hakan yasa yatashi yatafi, duk kukan da Aneesah take suna hada ido da sarkin tahadiye kukan tsaf dan gabanta ya mugun fadi, ahankali Aliyu yadan dukar dakai ya daga hannunshi. "barka da warhaka mai Martaba" gyadamai kai sarki yayi kafin ahankali cikin muryanshi na wayanda suka manyanta sosai yace "Aliyu, ina mahaifinka? Meke tafe dakai haka kwatsam kaman anjehoka? Wacece wanan atare dakai dake kuka haka?" yay maganan yana kallon Aneesah datama kasa magana sai goge kwalla take kanta akasa, cikin dakewan zuciya Aliyu yace "satota nayi Mai Martaba, yaune bikinta" shiru Mai Martaba yayi yana kallon Aliyun yanda idanunshi sukai jajir kallo dayama yamai yagane baida lafiya, sanan yasake kallon Aneesah, cikeda fikra irin na wayanda keda ilimin rayuwa yace "meke faruwa tsakanin mu biyun nan" ajiyan zuciya ahankali Aliyu ya sauke yace "sonta nake mai Martaba, itama kuma tana sona, iyayen mu sun sami matsala dake neman kawo nakasu a soyayyan mu dan aurar da itama yau zasuyi, bazan iya jurewa ba na shirya nai shigan mata naje na sato ta, nakawo ta nan dan kama soyayyar mu adalci da abinda yakamata" Aliyu yakarashe maganan ahankali yanadan taba kirjinshi dayakeji kaman zai tsage, ganin yana fama da ciwo yasa Mai Martaba bai cemai komiba yana kallon yanayin shi har na kusan minti hudu saida yaga yajanye hannun daga kan kirjinshi sanan yakira sunanshi cikeda natsuwa. "Aliyu, yimin magana da kyau, kafadi iyakar gaskiyan dakasani domin kuwa Allah nasama yana kallon mu gabaki daya, meke faruwa fadimani daga farko zuwa karshe kafahimtar dani" ajiyan zuciya Aliyu yasauke yace "mahaifina nada mata uku, wata hudu zuwa biyar dasuka wuce yakaro tahudu..........." anatse yake bama Mai Martaba labarin komi tundaga farko har karshe har zuwa Prison Aneesah da kuma yanda akayi yasato ta yau sanan yay shiru.
Chapter 105 · 0% Book details