← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 133

Sashe 107

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Gidan Biki_
Paracetamol Inna taballo tabama Ammi da kanta kewani irin ciwo zazzabi yarufeta sosai tace "sannu ga paracetamol kisha ina za'ai haka yau bikin yarki ko daurawa ba'a yiba zazzabin yarufe ki, su Baban Hamma ma sunje su dauko limam a mota dan ruwa yahanashi fitowa gashi babu abin hawa su ango har sun iso da mutanenshi duk ana waje ana jiran dawowan su, yanzu kinga har biyu da rabi Baban Hamma yakira yace suna hanya kawai daurin auren karfe uku ne, ungo dan Allah sha ko zaki warware kisami karfin yin hadamar bikin Yarki" ahankali Ammi tamika hannu ta karba tareda tashi ta zauna tana karanto addu'a sabida gabanta sai fadi yake daidai lokacin Mubarak Auta ya yaye labulen dakin Aneesah da Ammi da Inna keciki yaci gayu sosai yana kumbure kumbure, kai Inna tadago ta kallai tace "kai lafiyan ka zaka fadomana daka ba sallama har a dauro auren ne ka shigo cikin mata ko kunya bakaji ka kadai namiji a gidan dake cike da mata" turo baki yayi yace "ni har yanzu ba'a dauraba Baffa basu dawoba, kuma yunwa nikeji kibani abinci inna" hararanshi Inna tayi cikeda takaicin wanan sakarcin irin nashi tace "wai kai Hamma wani irin sakaran yaro ne, yunwa yunwa saikace ba'a baka abinci, yanzu ka tsayane a daura auren dakai bazakayi ba saika shigo gidan nan dake cike da mata kazo cin abinci eh Auta to bazakaci abincin ba" turo baki yasake yi ya bubbuga kafa akasa kaman zai fashe da kuka yace "wlh ni saikin bani abinci na" murmushi Ammi da kanta ke masifan ciwo tayi tace "kaji jeka kiramin Aneesah kuzo tare kafin kadawo zaka tarar da abincin ka na zuba maka harda nama" tsalle yayi yafita da gudu dan zuwa kiran Aneesah, da sauri Inna ta kalleta tace "Aneesah dake wajen kawayenta kuma kike nema? Ba dazun nan kukabar wurin ba, bazaki bar yarinya ta shakata da kawayenta ba yau bikinta" lumshe ido Ammi tayi tana wurga paracetamol abaki ta kurbi ruwa tace "Inna gabana ke faduwa sosai, kuma sai fadomin take arai, sabida kaina dake ciwone dani dakaina naje naganta amma bazan iyaba saisa nace a kiramini ita" dan dariya Inna tayi tace "kinada abin mamaki Maman Aneesah, banda abinki yau zaki aurar da yarki yau zaku rabu na dindindin saidai intazo wajenki ziyara ko tunanin wanan kadai ya isa yasa gabaki yafadi, mudai yau zamusha kallo in akazo kai Aneesah gidan mijinta" murmushi dukansu sukayi atare daidai Mubarak din ya shigo da gudu yace "Ammi Salamatu tace bakin aiko akirata ba wai tana wurinki, cewama tayi karya nake dan Aneesah na wurinki tundazu kika aiko akirata" da sauri Ammi ta tashi tazauna kafin ma tai magana Inna tace "wani irin shirme Salamatu ke fada kuma tun dazu ina tare da Ammi yaushe muka aiko a kira Aneesan" da sauri Mubarak yace "to wlh batanan Inna, su Salamatu kadai ne da kawayenta keta rawa agidan hartana cewa inna koma nace mata tayo sauri tadawo suna jiranta" wani irin faduwa gaban Ammi tayi da sauri ta tashi daga gadon tadau hijabinta Inna tace "tsaya ina zaki keda kanki keciwo karkije kifadi fa ga ko ina chabali" da sauri Ammi tace "ban gane me Mubarak kefadi ba gwara naje naji dakaina" tai hanyar fita da sauri Inna tace "bani hijabina Mubarak bari na biki" Hijabin Inna Mubarak yabata ta karba tasaka duk suka fito wajen yacika da maza sosai ganin Ammi da Inna harda Mubarak yasa Baffa da isowan shi kenan yana gaisawa da Mahaifin Hafiz yace "ina zuwa Alhaji" da sauri shida Na Sani suka karasa wajen su Ammi dasuka fito taresu yayi yace "me haka ina zaku maza duk sun cika waje yanzu fa za'a daura auren" da sauri Inna tace "Baban Hamma Aneesah ce wai aka aiko agidan patin su wai Ammi nakiranta suka tafi nikuma bamu muka kirata ba to yanzu bata gidan shine zamuje muduba da kanmu" da sauri Baffa yace "mene" arude Inna tace "bari muje mugani" gidan su Salamatun suka shiga shima Baffa kasa hakuri yayi yabisu ciki shida Na Sani suka tsaya wajen jikin Gate.

In baki da dari uku karma ki karanta dan wlh banyafe mikiba
Da Salamatun suka hadu daidai tafito da kwanukan dawasu kawayensu suka gamacin abinci, ganin Ammi da Inna yasa tace "Ammi kinga Mubarak kwar kwar yazo wai kina kiran Aneesah bayan tun dazu Aneesah na wurinki" kafin ma Ammi tai magana Baffa daya kasa hakura ya karaso tsakar gidan yace "ke Salamatu kaman ya Aneesah na wurin su, su tuntuni suna gida basu aiko a kira Aneesah ba" cikeda mamaki Salamatu ta zaro ido tace "ha'a amma dazu wata doguwar mata mai jiki tasaka bakin hijabi har kasa da nikabi da glass ta shigo duk kawayen muma sun ganta, dan Summaya ma ta tambaya inane dakin da Aneesah take tanuna mata dakinmu, ta shigo tace wai Ammi kince ta taho tareda Aneesah yanzun nan sutaho tare, shine ta tashi tasaka hijabi, tace nazo muje natare nace mata Inna bita wazai bama kawayen mu abinci saisa ban bitaba" arude Ammi tace "innalillahi wa innailaihi raji'un saisa gabana keta faduwa, wlh niban aiko wata mai nikabi tazo kiran Aneesah ba, munada ma mai nikabi acikin mutanen dasuka zo bikine?" da sauri Inna tace "wlh ko daya, ko mutum daya babu mai nikabi, to me kenan ina Aneesah jama'a?" da sauri Baffa yace "kira number ta" da sauri Salamatu tace "wayanta da duka kudadenta na wurina, suna cikin purse dinta ajakan dana rike mata" wani irin baya luuu Ammi tayi zata fadi da sauri Inna tarike ta tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Ke maman Aneesah tashi in sha Allah babu abinda yasami Aneesah, hala wani wuri taje, toko tana tareda ango ne?" da sauri Na Sani yace "ga ango nan dake tare duk damu wajen daurin aure" kawayen Aneesan ne dasuka ji hayaniya suka fito Baffa yace in kika karanta baki biyaba Allah ya isa "kai ku dudduba ko ina kuga, dagota mu kaita gida ta kwanta" taso da Ammi Inna tayi tabude ido da kyar saikuma tafashe da kuka tace "ina Aneesah na sace mini ita akayi kome gabana nafaduwa sosai wlh" tana kuka Inna tawuce da ita cikin gida, Hafiz sai kallon Ammin yake jikinshi nabashi kaman dawani abu, ahankali Baffa da duk yay wani iri yakarasa wajen Baban Hafiz, Baban Hafiz yace "lafiya daiko? Azo afara daurin auren ga limam nan ya shirya" cikeda tashi hankali Baffa yace "Alhaji a dakatar da daurin auren wlh ba'aga Aneesah ba saisa kaga maman ta ma nakuka yanzun nan" chak Hafiz ya tsaya yana wani irin kallon Baffa a rude, Baban Hafiz ne yace "kaman ya ba'a ga Fateema ba" cikeda tashin hankali yace "to yanzun nan maman Fateema taji gabanta nata faduwa shine ta aika Mubarak yakira Aneesah yaje yadawo yace ai kawar Aneesah tace bata kirata ba tun dazu, shine fa kukaga sun fito nima nabisu gidan ganin yanda suka rude, kawar kecemana dazunan nan taga wata nata mai nikabi doguwa mai kiba tasaka glass tazo tace wai Ammi nakiranta tace tabiyota suzo yanzu shine fa she's no where to be found wlh, kuma duka gidan bikin nan daidai da mutum daya bamuda shi mai nikabi" wani abokin Hafiz be dake tsaye kusada Hafiz yace "dazu danake shigowa naga wata katuwar mata sanye da bakin nikabi da hijabi harda glass achan ta baki bakin anguwa tafito daga wata brand new car ko ledan seat din ba'a cireba ferrari" "innalillahi wa innailaihi raji'un, meke faruwa ne haka? Lahaula" Baffa yafada cikin tsantsan tashin hankali, da sauri wani cikin mazan abokan Hafiz yace "nima exactly naga wata haka data shiga wanan gidan" yanuna gidan fatin, yace "kuma naga fitowanta tareda wata data saka milk color hijabi mai hula tajawo hulan gaba banga fuskarta ba sukai wajen layi" cikin tashin hankali Na Sani yace "Aneesah ce, itakeda Milk color hijabi, towai wacece matar nan? Me zatama Aneesah, yanzu a ina zamu nemo Aneesah?" ahankali Hafiz yazare malum malum din jikinshi ya mikama best friend dinshi tareda zaro key mota da sauri Baban shi yace "ina zaka Hafiz?" da idanunshi dasukai ja sosai yace "police station zani" yana maganan yafice da sauri best friend dinshi yabi bayanshi Su Baffa da sauran mutanen daurin auren aka babbazu ana shiga lungi lungu na anguwanni around ana neman Aneesah.
Inkika karanta baki biyaba Allah ya isa.

Wasa wasa fa tun ana ganin abin kaman wasa abu yadawo gaske dan gashi ana kiran sallan isha'i babuma alamun Aneesah, Ammi tasha kuka tasha kuka daga bayama amai tafara kwarawa mugun zazzabi ya turniketa saida Baffa yakiramata nurse tazo aka mata alluran bacci dantaki dena kukan sanan aka samu tai bacci aka cigaba da neman Aneesah.

Wanan kenan!!!!
[23/04, 08:21] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

_✍🏿M Shakur_

7️⃣2️⃣

Wasu irin hadaddun kaya sarki yasa aka shigo dashi adakin da aka kai Aneesah dan shiryata, baban Aliyu mutum ne da baijin zaitaba manta alkhairan shi agareshi ba sunsan juna da dadewa tun kafin yazama senate president, tun yana matsayin ambassador din Nigeria na US yasan baban Aliyu, dan awurin nema yahadu da mahaifiyar Aliyu sukai aure abinsu, aturai aka haifi Aliyu shi citizen of US ne, har yazo yabar aikin yakawo ta Nigeria kafin daga baya Aliyu na around 5 zuwa 6 years tarasu.
Chapter 107 · 0% Book details