← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 133

Sashe 114

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Anatse Mai Martaba yace "kabani kunya Muhammad Ibrahim, na dauke kai mahaifi ne kai mai adalci, wanda yasan yakamata, Muhammadu a yanzu koda eh da gaske Aneesah ce tazuba ma Aliyu guba a abincin saiya kaita gidan yari kasa akulleta, duka duka guda nawa yarinyar nan take? Metasani aduniya? Bakasan hatsarin dake tattare da gidan yari zai iyasa tazama wani abun da zai zama annoba ga rayukan musulmai gabaki dayaba? Muhammadu akwai hanyoyi da dama na hukunta yaro koda kam kisa yayi, sometimes gidan yari bashine best option ba hasalima shine worse option, banda haka bakai bincike ba, baka zurfafa bincike ba karaba yarinya da mahaifiyar ta, baka kyautaba ko kadan kai kuskure babba" Dady zaiyi magana Mai Martaba yadaga mai hannu alamun yamai shiru sanan yajuyo ya kalli Ammi dayaga tana share idanunta da bayan hannu yakira sunanta. "Rukayyatu" ahankali Ammi tadago kanta ta kalli Mai Martaba, kirjinshi ya nuna mata yace "zuciya kwara dayace kacal Rukayya, koda tai baki kaman gawayi karki bita kema kiyi bakin, yayin dakika bita kukai bakin tare hakan zai dushashe duka hasken dake tattare da ke saidai duhu Rukayya" Mai Martaba yadanyi shiru kafin anatse yacigaba. "a lokacin da zuciya ta kuntata, tai nauyi ta baci sanan tai baki, farin ruwa zaki samo kar kar ki wanke ta dashi saita dawo tai haske ta haskaka, Annabi yafadi a hadisi ingantacce cewa Al amarin mumini akwai abin mamaki, duka alamuranshi gabaki daya alkhairi ne, idan abin farin ciki yasame shi, shakara saiya godema Allah, hakan kuma shine mafi alkhairi agareshi, sa'annan idan abin bakinciki ya sameshi sabara saiyay hakuri kuma hakan shine mafi alkhairi agareshi, nasan kin kuntatu Rukayya anma yarki shairin neman kashe rai sanan aka kaita gidan yari nasan ba'a kyauta ba, amma amatsayin ki na musulma kamata yay kiyi hakuri ki mayar da komi ba komi ba tunda har Allah yadubi zuciyarki ya tausayamiki ya bayyanar da gaskiya ai ya isar miki, inda bahaka ba zai iya yaki bayyanar da gaskiya yabar Aneesah ta karaci rayuwanta agidan yari batare daya bayyanar da gaskiya ba, ranan gobe kiyama saiya bayyanar da gaskiyan agaban jama'an duniya, Allah mai yanda yasone fa sanan mai yanda yaga damane, Allah yariga ya fitar miki da yarki yakuma wanke ta tass soso da sabulu bayan haka yamuku sakayya ta hanyar saka wayanda sukai abun su suka koma gidan yarin yarki tafito bai isaba Rukayya saikin rama da kanki? Saikin nunama Muhammadu kema yarki yace mai daraja? Saikin kuntata ma Muhammadu kaman yanda yakuntata miki sa'annan ta hanyar dazaki kuntatamai ya kuntatu shine ki hana danshi yarki dayake so sabida kinsan duk abinda yasami danshi yasame shine ko?" Mai Martaba yay maganganan yana bubbuga kafa aka yace "to bari kuji wanan maganan da kowa nake afalon nan, da ace Al Umman musulmai zasu kasance nasu rama mugunta da Alkhairi da duk wani ayyukan sabon Allah irinsu gaba, fada, tauye hakkin wasu da sauran su yaragu a doron kasa an zauna lafiya, misali ki dauka bayan Muhammad ya kullemiki ya an wulakantata an mata duka azaban dakika sani na duniyan nan a gidan yari bayan yarki tafito sukazo neman aurenta kikace kin basu da yaya shi Muhammadun zaiji?" Mai Martaba ya wurga mata tambayan, ahankali Ammi ta share hawayen daya zubo mata takasa magana shima Dady kanshi akasa yakasa dago kai, ahankali Mai Martaba yace "dazaiji dana sani, zaiyi nadama, sanan zai baki wani girma da karamci na daban azuciyan shi domin kinada siffofi na mace mumina, saliha kuma mai yafiya, daganan kuma babu abinda zai dinga hadaku sai alkhairi, bari nabaki misali nabiyu dan fashi ne yatareki yamiki mugun duka ya kwace miki kudi da sauran su cikin iko irin na ubangiji yakawo wata hanyan da yan sanda suka kamashi za'a saka case akotu amma kikace ke kin yafemai duniya wa lahira asake shi kina ganin wanan dan fashin bazaiji wani iri ba? To saidai in mutum ne da Allah yariga ya rubuta tun a lauhul mahfuz cewa shi wane baida rabo alahira ahaka zaiyi rayuwanshi yakare shine bazaiji wani iri kota chanza ba amma inhar yanada rabo aduniya saikiga ya shiryu sabida wanan aikin alkhairin naki. Hausawa nacewa rama mugunta ga mugu ibada ne inji wa? Awani hadisi sukaga hakan? Awani ayyan Al qur'ani sukaga hakan? Al Umman musulmi rama mugunta ga mugu ba ibada bane wanan ba koyarwan addinin mu bane! Rama mugunta da alkhairi shine ibada! Shine ibada! Shine ibada! Idan mutum ya cutar dake yanzu haka anjima tazo yace bani ruwa wane inkina dashi dauka ki bashi kinsami lada, Rukayya kindau zafi sosai wanda ba haka yakamata musulma tayiba kome Muhammad yayi miki karki ce zaki rama harki so ki raba soyayyan dake tsakanin danki da Aneesah" shiru yayi yana kallonsu daya bayan daya sanan yajuya ya fuskanci Hafiz da iyayenshi wanda tun shigowan shi yagane shine ango sabida gayun dayaci, ahankali yace "Hafizu" dagokai ahankali Hafiz yayi ya kalli Mai Martaba yace "dazun nan nagama kawo muku hadisi akan idan abin alhairi yasami mumini godiya yakema Allah idan kuma akasin hakan yasamai saiyay hakuri, kasani cewa komi mukaddari ne daga Allah sanan matar mutum kabarinshi, idan Allah bai baka abuba karka zafafa akwai tanadin daya makane, kadau kaddaran da hannu bibbiyu" shiru Mai Martaba yayi sanan ya kalli Sarkin gida dake zaune kusadshi yace "shigo dasu" cikeda girmamawa yace "Allah yaja zamanin sarki mai adalci" sanan yamike tsaye yafita daga fadan da sauri duk akai shiru kowa najira yaga wa akaje shigowa dasu. Wajen mintuna biyar sarkin gida ya dauka sanan yadawo yabude kofa ya shigo kowa na jiran yaga waye zai shigo abayanshi fuskar Aliyu ne yafara bayyana yana sanye dawani sky blue sabuwar shadda da aka mata aikin sarauta yana rikeda hannun Aneesa dake sanye dawani dogon hijabi har kasa mai hula fuskarta babu kwalliya amma tai wani irin kyau da haske na amarci, hada ido datayi da mutane biyu tak afalon Ammi da Hafiz dasuka kasa dena kallonta yasa ta tsaya chak takasa tafiya tana kokarin fizge hannunta dagana Aliyu da baima da alamun sakinta baikuma waigo ya kalleta saima tsayawa da shima yayi ganin taki zuwa, Mai Martaba ne yadubesu sanan yakira sunanta. "Fateema kuzo nan" yanuna musu gabanshi, ahankali tadago kafa suka taho kanta akasa takasa daga kai ta kalli su Ammi harsuka karasa gaban Mai Martaba zama Aliyu yayi inda mai Martaba yanuna musu yana rike da ita sanan itama ta zauna ahankali kusada shi. Akai shiru dakin kowa da abinda ke wakana a zuciyanshi. Andau kusan minti goma sanan Mai Martaba yay breaking silence din yace "Na daurama Aliyu da Fateema aure jiya a yanzu Aliyu Mijine ga Aneesa sanan Aneesah matar sunna ce ga Aliyu wanda dumbannin jama'a suka shaida akan sadaki naira dubu dari!" wani irin mahaukacin shiru dakin yayi da da ake shiru at least kanajin saukan numfashin jama'an dakin amma yanzu kaman an zare musu rai.

Ahankali Mai Martaba yace "ajiya misalin karfe biyu na rana ana wanan zabga ruwan saman Aliyu ya shigo garin kaduna cikin tsananin ciwo, da kyar da tambayan sunan Baffan Fateema yagano gidan, yay shiga irin ta mata ta hanyar saka dogon hijabi har kasa da nikabi da madubin idanu yaje yasato Aneesah" dagokai Dady yayi ya kalli Aliyun wani murmushi ne ya subuce mai yadaki zuciyarshi yace "that's my son!!" Mai Martaba yace "bai kawota ko ina ba sai wanan masarautan, bayan series of bincike da kuma lura danayi nagano cewa yaran nan are made for each other dan suna bala'in son junansu iyayensu sune suka shigo TSAKANKANIN SOYAYYAn su hakan yasa na aurar dasu! Dan nasan bazaku taba daura aure ba in akasan Amarya ta bata ba".

_like I said, the doors of VIP is always open for marasa son jira_
[29/04, 21:02] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_

_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤

_✍🏿M Shakur_

7️⃣7️⃣ & 7️⃣8️⃣

_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa bank can also send MTN card 300_

_littafin nan na kudi ne karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi, pay anan or pay achan_

_please note, read only at night_

Wani irin murmushi Dady yayi yana kallon Aliyun da kanshi ke kasa a ranshi yace "shege Aliyu, that's My Son".

Allah kadai yasan me Hafiz keji, hannuwanshi rawa suka shiga yi sosai yakeson Aneesah bana wasaba, tunda matarshi tarasu she's the only yarinyar daya taba gani yaji yanasonta har cikin zuciyan shi, zafi da zuciyan shi kemai yawuce misali, ahankali baban shi daya lura da yanayin shi ya mika hannunshi yakama mai kafada gamgam irin alamun be strong dinan, ajiyan zuciya ya fuzar yana karanto addu'a dazasu sama zuciyar shi natsuwa.

Ammi taji saukan zancen nan kaman aradu ne, she couldn't believe wat her ear just heard, Aliyu da Aneesah tane sukai aure haka Aneesah zata mata, haka zata mata.....
Chapter 114 · 0% Book details