← Book details Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 133

Sashe 89

Atsakanin Soyayya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*see in bakida kudi karma kisake ki karanta littafin nan dan wlh banyafe miki ba zaki biyani hakkina alahira*_

_*keda kika biya access fee kikai joining group dina danki karanta littafi ba littafina kika siyaba so bakida anything kimin sharing book waje, saisa nai free pages, masu neman free pages kuje Wattpad dina "mamanshakur" and read, inhar kika fitarmin da littafi waje wlh keda Allah, Allah baya yafe hakkin wani sai in shi ya yafe miki*_

_kaduna_
Sanin batajin dadi yasa Baffa yahana Inna karta tadata da asuban ya shiga dayan dakin yatado yaranshi maza guda uku dasuke gida, Khaleelu, Ibrahim da Mubarak sukai alwala suka dunguma suka wuce masallaci.

Wuraren tawas nasafiya Baffa ya shigo gidan yabar yaranshi a makarantan asuba da akeyi a masallacin, inda matasa maza da mata suke haduwa amusu karatu sai karfe taran safe ake tashi. Da sallama ya shigo gidan yatsaya wajen akuyoyinshi da shanaye yana dubasu ya kwalama Inna kira. "Maman Hamma" daga kitchen Inna ta amsa. "na'am mai gida kadawo?" "kinbama awaki dusan kuwa?" tana juye tafashashen ruwan zafi a kullin koko data dama tace "eh najuye mai gida" shikadai Baffa ya shiga magana yana dudduba awakan yace "shine sukemin kuka kaman basu ci komiba da safen nan" tashi yayi ya kakkabe hannunshi tareda wankewa dawani ruwan dake cikin botiki sanan ya yarfe hannu yana tafiya cikin gida, Inna daya hango a kitchen tana kokarin hada musu kari yasa yay dakin da Aneesa take da sallama ya yaye labulen tareda tura kofar dakin hasken rana ya shigo dakin ya sauka akan fuskarta, dan motsi tayi sabida hasken daya hasko fuskanta da kyau, karasowa ciki Baffa yayi ganin karin ruwan yakare dayake nurse din jiya tanunamai yanda zai cire mata koda yakare kafin likitan yazo yasa yakarasa yakama hannunta tareda ciremata ya zauna ata baki bakin gadon yana kallon fuskanta yana tunani, gabaki dayan Aneesa da mahaifinta take kama banbancin su shine bata dauko hasken fatar shi ba saita dauko bakin fatar mahaifiyarta, bala'in tausayin yarinyar yakeji yarasa mesa ga mahaifiyarta tai aure, ga abinda mijin mahaifiyar yamata, in sha Allah kome zaiyi sai yayi mata dan yaga tafara walwala tadawo kaman da, zai mata duk wani abu dazai mantar da ita wahalhalun datasha gidan yarin nan dudda baida karfi amma duk inda zai samu saiya samo danya bata jin dadi. Ajiyan zuciya ya sauke yakai hannunshi ya daki filon da kanta kekai bude idanunta dake cikeda bacci tayi tai kini kini da rai kaman dama fada suke, murmushi Baffa yayi yaja hancinta da hannu yace "nine ke tashinki, tashi kiga gari yariga yawaye" yay magana yana dagata danta zauna, ahankali ta tashi ta zauna, hannunshi yakai yataba wuyanta yace "ya kikeji yanzu? Meke miki ciwo?" murya chan kasa tace "bakomi" shiru yayi ganin yanda take amsa shi dai dai kaman tana fada dashi, kaman ance dole saita amsashi, ahankali yace "tashi kije kidauro alwala kizo kiyi sallan safiya" tashi tayi tafita daga dakin tana tafiyarnan daidai kaman yar gidan sarauta tafita tsakar gidan daidai Inna tafito daga kitchen rikeda katon botikin kokon data dama, cike da fara'a ganin Aneesan tafito ga doguwan riganta data bata ya mugun yimata kyau gwanin ban sha'awa yasa tace "har kin tashi ne yar arziki, ya jikin?" ko kallon inda take Aneesa batayi ba tawuce abinta ta buga kofan bayin kaman dashi take fada kofar yabudu ta shiga ciki takara bugo kofan, kofan yarufe, karkada kai kawai Inna tayi tareda yin murmushi taji zafi amma batawani ji zafi ba tasan ba laifin ta bane, ta yaye labulen babban falonta ta shiga ta ijiye botikin a tsakiya tareda kwaso kofuna na robobi irin masu marfin nan ta zuzxubama kowa sanan tafito takoma kitchen din tana hadama Baffa dumamen tuwon jiya, ta hadamai asamiran shi tai dakinshi, fitowa shima Baffa yayi daga dakin Aneesan jin Inna na kwalamai kira......

Inkinsan bakida kudi karma ki karanta min littafi dan wlh banyafe miki ba, duk wacce ta karanta bata biyaba Allah ya isa.
Fitowa Aneesa tayi daga bayin bayan tadauro alwala daidai lokacin yaran Baffa sun shigo gidan, dawowan su daga islamiyan safe kenan suna dan hiransu, Khaleelu da Ibrahim sun girmeta, Khaleelu yanzu yanada 25yrs, saurayine kawai yanada karamin jiki ne dan jikin Innan su yadauko saisa baka gane ya girma, sai Ibrahim shikuma yanada 23 shi yamafi Khaleelu girma inka gansu zaka zaci shine babba dan har gemu gareshi gashi ustazu yanada kokarin sosai a fannin islamiya shi capinta ne, sai Mubarak wanda yake sa'an Aneesan yadan bata watanni da bazasu wuce uku ba zuwa hudu, washe mata baki dukansu sukayi ganinta tafito daga bayi, tun jiya da daddare suke so suje dakinta Inna tahanasu akan batada lpy, wani irin mugun tsaki Aneesa taja ganin yanda suke kallonta suna washe mata baki kaman tace sumata dariya. "mtswwwwww" tawuce tagabansu tai dakinta batare data kallesu ba, da sauri Mubarak dake sa'anta yace "kai badai ni kikama tsakin nanba yarinya? Wlh saidai su Ya Ibrahim kikamawa dan lallasaki zanyi mara kunya kin san halina ai yanda nake daddakaki in munzo Suleja" Aneesah harta shiga daki taji maganan Mubarak din karaf a kunenta da sauri ta daga labule tafito ta tsaya abakin kofa da kyau tana kallonsu daga wurin ta kalli Mubarak tareda nuna kanta da yatsa cikin kunan rai tace "dani kake wayan nan maganganun?" da sauri Mubarak shima cikin zafin kai irin na saurayin dake tasowan nan yace "a'a da wata nake tunda akwai wata bayan ke a tsakar gidan ne" kwafa Aneesa tayi tace "Allah yasoka dan inda dani kake da banga abinda zai hanani parke ma bakin nan dakai magana dashi ba, dogo ba hankali kawai" cikin fushi Mubarak yataso zaiyo kanta Khaleelu baban wansu yarike shi yace "me haka bakasan bakuwar mu bace? Aneesa cefa dakuke wasa tare lokacin da ake zuwa da ita datana yarinya, ka manta Aneesan da Abba ke kwasan mu muje Suleja ganinta, me haka? Common yar uwan ka ce, share, forget" cikin fushi Aneesa tace "barshi karma ya share baisanni bane, zan gwadama hankali yaro, dogo ba hankali kawai" cikin fushi Mubarak keson kwashe hannunshi daga hannun Ya Khaleelu yace "Ya kagani nitake cema dogo ba hankali ko, wlh takara cemin dogo ba hankali saina fasamata baki wlh kuwan" da sauri Aneesa tace "shege kafasa ance dogo ba hankali, kazo inhar kai dan halak ne" wani uban tsalle Mubarak ya daka ya fizge hannunshi yay cikin gidan ganin yana tahowa yasa Aneesa ta shiga waige waige, wukan data hango a makwarara inda aka kai kayan wanke wanke yasa tai wurin da gudunta ta tsugunna tadau wukan ta rike da kyau ta kalli Mubarak din dake zuwa kaman namijin zaki tace "kazo kaga wlh saina maka barakaka" da sauri Mubarak yakarasa gabanta batare daya damu da wukan data daukaba dan yasan duk wargi ne yasa hannu yadaga zai kifamata mari Aneesa ta daddage tayanki fatar hanunshi da wuka, atare daga Khaleelu har Ibrahim sukai ihu dan duk basu zaci zata iya amfani da wukan ba sukayo kansu da gudu.

Wani irin ihu da Mubarak yayi yakoma baya yasa da sauri Baffa dake zaune kan yar kujeran dakinshi yana sauraron labarin BBC hausa na safiya yana kallon Inna na zubamai man shanu kan dumamen shi itama tana sauraron labaran da yakeji ya rage karan da sauri yana gyara zama jin kaman yaji ihu, hayaniya dasuka ji na yaransu yasa atare suka Mike tsaye da sauri, Inna ce tafara yaye labulen ganin yanda hannun Mubarak auta ke fitar da jini sosai yasa tasaki salati tafito da sauri tai wurin Baffa biyeda ita shima yana saurin, karasawa wajen tayi takama hannun Mubarak dake kuka sosai yana kallon jinin dake zuba daga hannunshi tace "innalillahi, menene haka? Meya yankeka Hamma na eh dan Autan inna shi?" cikin fushi Khaleelu na kallon Aneesan dahar lokacin na rikeda wuka tana kallonsu yace "Aneesah ce ta yankeshi shine dan inamata fada wai inna karacemata kala saita parkamin ciki nima" da sauri inna ta zare dankwalin kanta tareda warware wa ta nannade hannun Mubarak tana kallon fuskan Baffa dayay shiru yana kallon Aneesan kaman wani wawa, yanda take hararansu ta damke wukan gam a hannu kaman jira take wani yazo ta fideshi, ahankali Baffa yadaga kafa tareda karasawa inda take hannunta dake rike da wukan takama yarike cikin rashin wasa yace "bani wukan?" kallon fuskanshi tayi ganin yanda yay kini kini da rai yasa ahankali ta sakin mai wukan ya karba, sanan yace "kinyi sallan danace kije kiyi?" girgixa mai kai tayi alamun a'a tana cije pink cute lips dinta, hanyar dakinta yanuna mata da hannu yace "wuce kije kiyi salla kafin na mugun saba miki" sakin lips dinta datake taunewa tayi ta bataraii cikin fushi tai hanyar dakinta ta yaye labule ta shige, ahankali Baffa yajuyo hannun Mubarak din ya karba ganin Inna tariga ta kulle wajen yasa yace "sannu ya isa haka kubar maganan maganan, kuwuce kuje kusha kokon ku, zan sayo maka pain killer kasha Mubarak" wucewa duk sukayi dan suna mugun jin maganan mahaifinsu basuma Baffa gardama koma yayene ko akan miye, yarage wurin daga Inna dake kallonshi saishi, dago kai yayi ya kalleta zaiyi magana tajuya fuuuu tawuce, ajiyan zuciya ya sauke cikin tsananin damuwa sanan ya tsugunna dayan wukan daya gani acikin kwanukan wanke wanken ya dauka yay dakinshi ijiye wukaken yayi a wuri daya ya killace su gudun karta kara dauka sanan ya zauna gaban tuwonshi yana kallon tuwon dake turiri danya dumamu sosai ya fuzar da iska cikeda damuwa, wanan lamarin yafi tunaninshi ta bayanshi shine dama haka yara kedawowa in aka kaisu gidan yari??? Inko har hakane koma wani laifi yaro zaiyi gwara a hukunta shi agida dan zuwanshi gidan yari tabarbara komi yake saima dai yamaida yaro abinda yafi da worse and worse and worse.kika karanta batare dakin biyaba, Allah ya isa, ban yafemikiba.
Chapter 89 · 0% Book details